Jibwis Nigeria

Jama’atu Izatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (Jibwis Nigeria)

Wannan qungiya ta al’ummar musulmi an kafa ta ne tun a shekarar 1978 a Najeriya, kuma shugabanta na farko shi ne Alhaji Musa Mai Gandu Muhammad, a qarqashin kulawar Malam Abubakar Mahmud Gumi, tare da Sheikh Isma’il Idris bn Zakariyya, a matsayin shugaban majalisar malamai na farko na kungiyar.
Qungiyar ita ce irinta ta farko a tarihin yada Addinin Musulunci a Najeriya, hadi da harkar ilmantarwa, tare da daukaka darajar harkokin addinin Musulunci ba tare da wani tsoro ba. Don haka ne sai kungiyar ta sanya wasu ginshiqan manufofi da take so ta cimma domin kai wa ga gaci.

Daga cikin muhimman manufofin wannan kungiya sun hada da:
– Kawar da duhun jahilci daga cikin al’umma, wanda ya yi wa al’umma katutu.
– Hada kan al’ummar musulmi a bisa koyarwar Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW),
– Wayar da kan al’ummar musulmi game da al’amuran addini, domin a gudu tare a tsira tare.
– Fadakar da al’ummar musulmi domin a yi watsi da wasu miyagun littattafai da suke tura mutane cikin halaka.
– Tabbatarwa da cewa Annabi (SAW) ya kammala isar da sakon Allah (SWT).
– Duk wanda ya yi da’awar annabta, ko kuma yake riya cewa Annabi (SAW) yana ziyartarsa da wani sako, to wannan zunzurutun makaryaci ne.
– Yada Musulunci a Najeriya da wajen Najeriya.
– Yin da’awa a kan fadin Manzon Allah (SAW) cewa: “duk wanda ya ga abin qi, to ya sauya shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to da harshensa, in ba zai iya ba, to da zuciyarsa, amma wannan shi ne mafi raunin imani.”
– Kar a boye hujja in dai har ta tabbata daga littafin Allah Madaukakin Sarki, ko sunnar Manzon Allah (SAW).

Kasancewar wannan kungiya ta shahara sosai a kasashe daban-daban na duniya, wannan ya sa aka samar da kwamitoci daban-daban domin gabatar da ayyuka da yawa. Wasu daga cikin kwamitocin kungiyar sun hada da:
– Kwamitin Da’awah.
– Kwamitin Tarurrukan Wa’azi.
– Kwamitin Kula da Marayu
– Kwamitin Ilimi.
– Kwamitin Mutane Goma.
– Kwamitin Taimakon Gaggawa.
– Kwamitin Zartaswa.

Shugabanta na kasa a wannan lokaci shi ne Sheikh Abdullahi Bala Lau, khalifa na farko a sashin shugabancin wannan kungiya tun bayan kafa kungiyar, wanda tsohon mataimakin shugaban kungiyar ne a zamanin shugabancin marigayi Alh. Musa Maigandu Muhammad, kuma ya gaje shugabancin kungiyar ne bayan rasuwarsa.
– Shaikh Usman Isah Taliyawa Gombe: Mataimakin Shugaban Kungiya Na Kasa.
– Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe: Babban Magatakardan kungiya
– Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo: Shugaban Majalisar Malamai na kasa
– Sheikh Barr. Sabi’u Jibiya Katsina: Mataimakin Majalisar Malamai na Kasa
– Engr Mustapha Imam Sitti: Shugaban Rundunar Yan Agaji na kasa.

Kungiyar ta samu karbuwa a sassa daban-daban na duniya. A Najeriya tana da rassa a dukkanin jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya.
Haka kuma saboda irin yadda kungiyar take kokarin ilmantar da al’umma, wannan ya sa har ta sami kutsawa zuwa ga wasu kasashe, kamar su; Nijar da Mali da Sinigal da Togo da Kamaru da Cadi da Burkina da Gini, Saudi Arabia da sauransu.

Advertisements