TAMBAYA 001: Malam ya ingancin cewa Likitoci sun ce idan mutum ya kai Azumi ya sami wani a bu mai ɗumi ya ci ko ya sha saboda Antar sa tana bushewa, ga shi kuma na ji Hadisi manzon Allah ba da shi yake buɗa baki ba, yana yi ne da DABINO.

TAMBAYA: 001

Malam ya ingancin cewa likitoci sun ce idan mutum ya kai Azumi ya sami wani abu mai ɗumi ya ci ko ya sha saboda Antar sa tana bushewa, ga shi kuma na ji Hadisi manzon Allah ba da shi yake buɗa baki ba, yana yi ne da DABINO.

AMSA:

Toh, ni dai ba Likita bane, bansan gaskiyar hakan ba a wajen likitocin.

Amma dai abinda na sani Hadisi ya inganta daga Manzon Allah صلى الله عليه وآله وسلم cewa: "Manzon Allah yana yin buɗa baki da ƊANYEN DABINO, idan bai samu ba, sai yayi da BUSASHSHEN DABINO, idan bai samu ba, sai ya KURƁI RUWA YA SHA"

Malamai suka ce: Babu abinda yake saurin bin jijiyoyin mutum bayan ya ɗauki lokaci bai ci komai ba kamar ZAƘIN DABINO wanda babu wani Zaƙi da yake kamar sa wajen amfani, shi yasa manzon Allah yake yin hakan. KUMA MANZON ALLAH SHINE LIKITAN LIKITOCI!

Na tambayi MATA TA game da haka kasancewar ta masaniya a kiwon lafiyar ɗan Adam, sai ta ce mani:

"Allah Ya halicci dan adam ko yana azumi yana samun supply of nutrients irinsu glucose ta hanyar aika ma brain saqo cewa glucose level a cikin jiki yayi qasa saboda azumin, daga nan ita kuma zata yi signalling ayi secreting wasu hormones like Glucocorticoids da zasuyi stimulating break down of glycogen stores domin a samu release of glucose saboda jiki ya amfana, so idan aka ce hanta na bushewa kenan ba zata iya yin wannan aikin ba".

A ɓangaren lafiyar ma kenan ba haka bayanin yake ba.

Saboda haka, MAFI ALKHYAIRIN SHIRIYA ITACE SHIRIYAR MANZON ALLAH صلى الله عليه وآله وسلم.

Allah shine masani.

Abubakar Saidu Musa Funtua.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s