RAYUWAR IBRAHIM ZAKZAKY, TASOWARSHI, DA’AWARSHI DA ABUNDA YA KAMATA MUTANE SU SANI GAME DA SHI’ANCI (2)

…Cigaba daga rubutun baya.

A rubutun dana gabatar a baya na bayyana yadda Ibrahim Zakzaky da Malaminsa Islamul Haqq suka aiwatar da da’awarsu da ayyukansu na yada shi’anci. Sai dai wannan maganar na kawo ta ne daga cikin mahanga da fahimtar Farfesa Abdullahi Mahdi tsohon mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello na Zariya.
Sai dai akwai wadanda akayi gwagwarmayar dasu tun a farko kamar Malam Ali Ibrahim Attukriy, wanda yayi mun wasu tambihai da nuna cewa a magana ta gaskiya shi Islamul Haqq yana da tsananin kyama ga Iran. Wannan ya sanya zan takaita bayanan da nake tattare dasu ta wannan bangaren har sai na samu zama da Malam Aliyu Ibrahim Attukriy. Cikakken bayanai akan haka zasu zo a wasu wuraren daban.
Sai dai ina son masu karatu su fahimci cewa ba zamu tattaro dukka tarihin gwagwarmayar bane, sai dai zan cirato wadanda suke da alaka ne da asalin sakon da nake son isarwa na wasu abubuwa da ya kamata mutane su sani game da shi’anci, musamman yan boko da wadanda basu fahimci addini ba ko sun fahimta to a baibai suka fahimceshi.
Ibrahim Zakzaky ya samu nasarar yada manufofinsa ne da kuma burinshi ta hanyar tarurrukar IVC (Islamic vacation Course) da ake gabatarwa, babu shakka ya sanu ta wannan waje kuma manufarshi ta isa ta wannan wajen. A lokacin Ibrahim Zakzaky da Matarsa (Budurwarsa a wancan lokacin) ta taimaka mashi sosai wajen yada manufofinsa. A wancan lokacin babbar gubar da suka cusa a zukatan mutane shine karatun boko haramun ne, kuma a lokacin sunci nasara sosai wajen yaudarar matasa akan wannan da’awar, musamman matasa marasa dabara da tunani, kuma mafi yawanci ‘ya’yan talakawa.
An dauki tsawon lokaci ana gwagwarmaya da sunan musulunci.
A shekarar 1979 bayan Khumaini yayi abunda ya kira juyin juya hali, inda ya tunkude shugaban Iran Shah daga mulki. Wannan aiki da yayi ya burge dayawa daga cikin ‘yan boko kuma kungiyoyin da suke da hamasa na addini sun ji dadin wannan aiki na Khumaini. Daga cikin wadanda suka rudu da wannan aiki na Khumaini akwai kungiyar dalibai musulmi na Nigeria ta wancan lokacin. Sheikh Muhammad Auwal Albani Zariya yana bamu labari cewa a wannan lokacin kungiyar dalibai musulmi na MSS sun shirya wasu wakilai da zasu je kasar domin taya su murna akan wannan abu da akayi da suna ”Juyin juya hali” wanda ya bayyana a yau shi’anci ne da kuma yakan musulmi. Bayan sun isa wannan kasa da suna taya su murna, su kuma kasar Iran dama manufarsu da burinsu baya wuce a yada shi’anci a kasashen duniya. Wannan ya sanya suka karbi dalibai Musulmi da hannu bibbiyu domin zasu yi musu aiki. A daidai wannan gabar ne wasu suke cewa ta nan ne Ibrahim Zakzaky ya karbo kwangilar yada shi’anci. Kasar Iran ta kulla alaka da wasu mutane masu yawa yan kasar nan, daga cikinsu akwai Sheikh Abubakar Jibril Farfaru, wanda a lokacin kasar Iran ta mu’amalance su da shi su Sheikh Abubakar Tureta. Sheikh Abubakar Jibril Farfaru yana bamu labari da cewa: "Ni da Sheikh Abubakar Tureta mun yi alaka da Iran fiye da shekara goma, a lokacin juyin juya hali, an dinga gayyatarmu zuwa kasar Iran din, zuwan da muke yi a kai a kai ya sanya suka saki jiki da mu. Haka yasa muka zama yan gida a Iran, amma bayan mutuwar Khumaini a shekarar 1988 mun je Iran, inda mukayi kwana fiye da arba’in, wato har karshen zaman makokin. Daga karshe a lokacin dawowarmu gida Nijeriya, ministan cikin gida a wancan lokacin na kasar Iran ya tambayemu irin abinda muke so su yi muna tsaraba dashi. Inda Sheikh Tureta nan take yace masa littafai muka fi so. Haka nan aka siyo littafai masu tulin yawa. Domin a lokacin a kasar nan babu littafansu. Wadannan littafan da aka ba su, sun taimaka kwarai wajen gane sirrin addinin shi’a da sharrin da yake cikinta. Wannan abubuwa da suka karanta ya sanya suka yanke alakar dake tsakaninsu da kasar Iran.
Ta gaba guda kuma a nan kasa Nijeriya an samu wadanda suke ta wa’azi da fadakarwa da nuna cewa Ibrahim Zakzaky shi’anci yake son ya kaisu zuwa gareshi. Farfesa Abdullahi Mahadi yana bamu labari da cewa: ” A shekarar 1980s, sanda matasan da ya yaudara suka fahimci cewa Ibrahim Zakzaky ba yi da abin fade don gane da ilimi addinin musulunci sai kame-kame da kauce-kauce da kuma batar da hankalin mutane, mafi yawanci sun rabu da shi daga baya. Daga ciki akwai su Sheikh Aminu Aliyu Gusau (Allah ya kara mashi lafiya) da su Malam Aliyu Ibrahim da Malam Mujahid da sauransu, inda suka kafa tafiyarsu ta Attajdid.
A lokacin mutanenshi sun gane shi ne bisa kalmomin tunzurawa da yayi amfani da su kamar su: "Amfani da kalmonin a yaki amurka, kafurai ne dagutai, da kamfen da masallacin Qudus da kiran mutane a fito zanga-zanga duk shekara.

Za mu tsaya anan, sai a rubutu na gaba zamu cigaba Insha Allahu.

Najeeb Elkabir Kwarbai
30/11/2016

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s