RAYUWAR IBRAHIM ZAKZAKY, TASOWARSHI, DA’AWARSHI DA ABUNDA YA KAMATA MUTANE SU SANI GAME DA SHI’ANCI (1)

Bayan zurfin bincike da tuntuba da nayi domin sanin hakikanin abunda shi’a take nufi da inda ta dosa. Wannan ya sanya na samu zama da wasu da yawa daga cikin magabata da sukayi rayuwa da Ibrahim Zakzaky da kuma wadanda suka auka cikin da’awar cikin rashin sani, wasu kuma saboda hamasa ta addini.
Sai dai nayi godiya ga Allah daya sanya cewa ni haifaffen Unguwar Kwarbai ne, inda jagoran kira zuwa ga Shi’anci yake, kuma na kara godiya ga Allah cewa duk wadanda aka fara wancan hayaniya dasu wasu iyaye nane, wasu kuma Malamai ne ga Iyayena nima na samu tagomashin zuwa wajensu domin daukan karatu, wasu kuma abokai ne ga Mahaifa na. Wannan ya sanya naji dadi a raina cewa babu shakka zan samu cikakken lokaci domin zama tare dasu domin su bani tarihi akan hakikanin yadda manufofin Zakzaky suka fara bayyana. Ta bangare guda kuma tun lokacin dana taso har na fara wayau na riski cewa gidanmu yayi makotaka da mazaunin Yan Shi’a a wancan lokacin,kuma har na riski lokacin da gwamnatin General Sani Abacha ta rinka kama Yan Shi’a a Zariya.

Daga cikin Yan Shi’an da nayi makotaka dasu kuma da wayau na, sun hada da:
1-Hamza Lawal Badikko.
2-Malam Hassan (Ya mutu)
3-Malam Abdullahi (Bansan halin da yake a yanzu ba)
4-Malam Ahmad (Baban Bara’a) wanda shine yake daukan ‘ya’yan Zakzaky zuwa makaranta a baya, bansan halin da yake ciki ba a yanzu.
5-Malam Buhari (Mutum garin Zamfara, haifaffen Maradun).
6-Malam Gulamu.
7-Ciroma (Wanda shi tun kamun da akayi mashi a lokacin Gwamnatin Abacha,bayan anyi belin dinshi ya bar Zariya. Amma abunda ya shafi shi’a, bansani ba ko yana nan yanayi ko ya bari)
8-Malam Turi (Wakilin Zakzaky na garin Kano, wanda a yanzu labari ya yadu a duniya cewa an kasheshi.)

Na ambacesu ne da sunan ”Malam” kasantuwar mu a lokacin muna musu kallon cewa Malamai ne, masana addini kuma masu kishin addini. Sannan wadannan dana ambato su, sune wadanda zan iya tuna su, kodai saboda anyi zama dasu zai wuya a manta dasu, ko kuma saboda yadda a lokacin suka zama masu kyaman mutane da kuma nuna alakarsu da addini yasa ba za’a manta dasu ba.
Wata gaba da bazan manta da ita ba, shine farkon makarantar Fudiyya ta farko da aka gina a tafiyar Harka, an gina ta ne a Unguwar Kwarbai, kuma a gidan Yayan mahaifina a nan Unguwar Kwarbai din. Babu shakka da yawan mutane sun rudu da wannan makaranta, kuma sun sanya ‘ya’yansu a makaranta. Nima har an sanya yan uwana guda biyu a ciki. A wannan lokacin idan suka dawo basu da abunda suke bita a matsayin sakamakon karatun makaranta sai wakar ”Sojojin Hizbullah”. Wanda a lokacin wadanda suka gane manufar tafiyar sun yi ta fadakarwa da jawo hankali akan shi’a din. Daga cikin wadanda nasan sunyi kaurin suna bisa tuntuba da nayi, sune:
1-Malam Idris Salihu Kwarbai
2-Sheikh Sani Kakeyi.
Duk da kowannensu akwai inda yafi bada gudunmuwa, amma na kirga su a matsayin wadanda suka dage wajen fallasa munanan manufofi da akidun shi’a a Zariya da kuma al’umma gabaki daya.
Na fara shimfida ne da wadannan bayanan domin mai karatu ya gane cewa, akalla an kiyaye rayuwar Ibrahim Zakzaky kuma yan uwanshi na gida sune suka fara kundace tarihinsa da fito da ko wanene shi, kamar yadda bayani zai zo akan haka In Allah ya so.

FARUWAR SHI’ANCI A NIJERIYA DA SHIGOWARTA.
Shi’a ta fara shigowa Nijeriya ne ta hannun wani dan Kasar Pakistan mai suna Islamul-Haqq, wanda a wannan lokacin yake koyarwa a jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, a tsakanin shekarun 1970s.
Ginin shi’anci a Nijeriya ya fara ne daga tsakiyar 1970s zuwa tsakiyar 1980s. Kuma a jami’ar Ahmadu Bello hakan ya fara.

Farfesa Abdullahi Mahadi ya bada labari cewa shi Islamul Haqq a wannan lokacin abokin aikinshi ne a tsangayar fasaha da zaman takewar dan adam (Faculty of arts and social science). Yace a wancan lokacin shi Farfesa yana koyarwa a sashen tarihi (Department of History). A wannan lokacin ofisoshinsu yana kallon juna ne.

Islamul Haqq yayi kokari wajen ganin ya kira Farfesa Abdullahi Mahadi zuwa ga bin tafarkin shi’a, sai dai bai amince mashi akan hakan ba.

Farfesa yacigaba da cewa: "Daga nan, sai ya ci nasarar jawo Ibrahim Zakzaky cikin shi’anci. A wannan lokacin Ibrahim Zakzaky dalibinsa ne a sashin koyar da ilimin tattalin arziki (Department of Economics). Gidan Islamul Haqq ya zama cibiyar karantar da shi’anci. Ta hanyar yaudara da batar da mutane daga gane gaskiya. Islamul Haqq da Ibrahim Zakzaky sun yi nasarar shigar da dalibai shi’anci, musamman a tsangayar kimiyya (Faculty of Science) da masu share fagen shiga jami’a (School of Basic studies). Suna nunawa yara karatun haramun ne. Zan iya cewa Islamul-Haqq da Ibrahim Zakzaky sune suka fara gina tushen Boko Haramun a Nijeriya.

Baya ga yaudaran wadannan yara da Ibrahim Zakzaky da Malaminsa sukayi, Ibrahim Zakzaky da budurwarsa (Matarsa a yanzu) mai suna Zeenat, suka fara yawon yada shi’anci a makarantun sakandare na Arewacin Nijeriya. A wani lokaci Zeenat ta yi wani huduba a wata makarantar ‘yan mata (FGGC Sokoto) daga fitanta makarantar, yaran masu karancin wayewa da rayuwa su ka fita kan tituna suna cewa sai sun yi jihadin musulunci. Sai da jami’an tsaro suka kama su. A lokacin da iyayen yaran suka je kabo ‘ya’yansu, sai suka ki yarda da iyayensu su karbi belin dinsu,a cewarsu iyayen kafurai ne.

Zamu cigaba a rubutu na gaba.

Najeeb Elkabir Kwarbai
29/11/2016

Advertisements

2 Replies to “RAYUWAR IBRAHIM ZAKZAKY, TASOWARSHI, DA’AWARSHI DA ABUNDA YA KAMATA MUTANE SU SANI GAME DA SHI’ANCI (1)”

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s