LABARAI A TAKAICE

*Kamfain Matatar man Dangote zai fara aiki a 2018

*Kamfanin wanda haryanzu ana gina shi zai zama daya daga cikin manyan matatar mai a nahiyar Afrika.

*Bayan haka kuma yana gina katafaren kamfanin sarrafa iskar gas da kuma Kamfanin takin zamani.

*Wani dan sanda a jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin Najeriya ya harbe abokin aikin sa bisa gardamar raba na goron Naira 20,000.

*Labarin dai ya nuna dan sandan da ya rasa ran sa ya so a tsakurawa shugaban ofishin su sashe daga kudin amma daya abokin ya ki yarda inda cikin fushi ya ja kunamar bindiga ya harbe abokin aikin na sa.

*An kai gawar wanda ya rasa ran na sa dakin ajiye gawa inda a ke ci gaba da ta’aziyya ga iyalan marigayin mai mata 2.

*Wassu miyagu da a ke ganin ‘yan tsageran Neja Delta ne sun kai hari kan wani bututun mai na kamfanin man fetur na Najeriya NNPC a tashar FORCADOS.
Harin dai dai ya faru ne dab da garin Warri mai matatar man fetur.
Rundunar sojan Najeriya dai na ci gaba da yaki da ‘yan tsageran inda ita kuma gwamnati ke bin maslahar siyasa don magance matsalar.

*Bayan ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi da shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki; alamu na nuna fadar shugaban Najeriya ASO ROCK za ta sake gabatar da bukatar hurumin karbo lamunin Dala biliyan 29 daga ketare.
In za a tuna fadar shugaban Najeriya ta tura batun neman amincewar karbo lamunin amma bai samu karbuwa a majalisar ba don nuna damuwar rashin cikakken bayanin yadda za a yi amfani da kudin.

*Gwamnatin Najeriya dai na nuna ba ta da zabi face ta ciwo bashi don aiwatar ayyukan raya kasa a da ke kasafin kudi.

*ZABEN AMURKA: A na ci gaba da kada kuri’a a zaben Amurka inda masu zabe ke kada kuri’un su wa imma ga Hillary Clinton ta Democrats ko ga Donald Trump na Republican. Hillary dai da rakiyar mijin ta tsohon shugaban Amurka Bill Clinton ta kada kuri’ar ta a Newyork.

*Dan takarar Republican Donald Trump na kan gaba da yawan kuri’un wakilai fiye da ‘Yar takarar Democrat Hillary Clinton a zaben Amurka.

*Sakamakon farko ya nuna Trump ya samu kuri’u 245 na wakilai daga cikin 270 da ya kamata ya samu ya lashe zaben a matsayin sabon shugaban kasa yayin da Clinton ke da kuri’u 215 a yanzu haka.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
09/Safar/1438
09/November/2016

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s