LABARAI A TAKAICE

*Wani harin da ‘yan Boko Haram su ka kai yankin Mallam Fatori ya yi sanadiyyar rasa ran Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali wanda don kwazon sa a yaki da Boko Haram a ke yi wa lakabi da “SARKIN YAKI”

*Abu Ali dai ya ma taba samun lambar yabo daga babban hafsan rundunar sojan kasan Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai don kwazon sa wajen kwato garuruwa daga ‘yan ta’addan Boko Haram.

*Rundunar sojan Najeriya ta ba da labarin ceto karin daya daga cikin matan Chibok mai suna Maryam Ali Maiyanga wacce ta ke dauke da yaro mai suna Ali dan wata 10 da haihuwa.

*An gano Maryam a yankin karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno.

*Wannan yan nuna yanzu saura mata 196 a ke nema daga hannun ‘yan Boko Haram.

*Rahotanni sun nuna akwai wadanda su ka rasa ran su a cikin matan fiye da 270 da a ka sace a makarantar su ta sakandaren Chibok shekaru 2 da su ka wuce.

*Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta ba da labarin sake kakakin tsohon shugaban Najeriya Jonathan, wato Reuben Abati wanda ya zauna don binciken sa da a ke yi kan amsar Naira miliyan 50 daga Kanar Sambo Dasuki.

*Hakanan labari ya nuna tsohon ministan Abuja Sanata Bala Muhammad ya samu jinyar da ta sanya kai shi ganin likita.

*Sauran wadanda ke hannun EFCC sun hada da tsohon minister Femi Kayode da Muslihu Obanikoro.

*An kammala taron murnar cika shekara 10 da nada Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar a fadar sa da ke Sokoto arewa maso yammacin Najeriya.

*Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida taron wanda ya jaddada tarihin daular Usmaniyya da tutoci 12 da Shehu Usman Dan Fodio ya bawa almajiran sa da su ka kafa masarautu masu tasiri har zamanin yau.

*An ga tsohon shugaban NAJERIYA Obasanjo kan doki, hakanan Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha da Bishop Father Mathew kuka da suma duk sun hau dawakai.

Ibrahim Baba Suleiman
Jibwis Social Media
06/Safar/1438
06/November/2016

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s