ALBISHIRINKU DALIBAN ILMI.

Daga: Abdullahi Almadeeniy Kagarko

Hamshakiyar jami’ar nan ta duniya dake birnin Madina; wato Al – jami’atul Islamiyyah ko Islamic University of Madina; duk shekara tana bude kofar amsar dalibai dakeson karatun addinin ko na boko a kusan tsawon watannin kowace shekara. A karkashin haka muke yiwa yan’uwanmu dalibai albishir cewa duk mai son yayi applying a wannan jami’ah mai dimbin tarihi ga muhimman abubuwan da akeso ya mallaka domin turawa a website na ita jami’ar:
1- Statement of result (Kashfud-darajãt).
2- Testimonial (Shahãdah Thãnawiyyah).
3- International Passport (Jawãzus – Safar).
4- Birth Certificate (Shahãdtul Mīlãd).
5- Coloured Passport photograph (As-suratul – shakhsiyyah)
6- Medical Report (Taqreer Ďibbiy).
7- Recommendation Letter guda 2 ( 2 Tazkiyyah).
8- Senior Secondary Certificate( idan makarantar da aka gama tana badawa). Amma shi ba dole bane, domin testmonial yakan zama makwafinsa.
Idan kuma dalibi yanason yayi applying ne a bangaren courses na boko (amma izuwa yanzu social sciences ne aka fara bada admission a jami’ar) sai ya kara da abubuwa kamar haka:
1- Jarabawar dake nuna dalibi ya iya turanci mai suna TOEFEL ko wata wadda take daidai da ita.
2- Jarabawar dake nuna dalibi computer litterate ne mai suna ICDL.
Kaitsaye idan mutum ya mallaki wadannan takardun sai yaje CAFE mafi kusa dashi ya shiga wannnan link din: admission.iu.edu.sa sai yazabi harshen da yafi fahimta sai yashiga zaiga wurin da ake aka rubuta NEW APPLICATION (TAQDIMU ĎALABIN JADEED) sai yashiga ya cike abubuwan da ake bukata. Bayan ya gama cikewa zaigani an nuna masa jerangiyar list na takardun yakamata ya tura, sai yazabi takardun da aka ambata a sama abisa abunda mutum yazaba zai karanta (imma karatun addini ko na boko). Sannan sai yayi scanning din originals takardunsa yayi uploading din kowanne a inda aka bukaci yasa su. Idan kayi uploading takarda ta karshe zasu baka RAQAMUL – ĎALAB (APPLICATION NUMBER) sai kayi printing dinshi ka rikeshi dakyau, domin idan kasamu admission shine zaibaka daman ka iya printing din admission letter daga website na jami’ar.
MUHIMMAN TSOKACI:
1- Ka tabbatar shekarun ka basu wuce 25 ba. Idan kuma sun wuce sai ka samo wani birth certificate ko declaration of age a kotu, haka ma shekaru dake cikin Indegene.
2- Ka tabbatar shekarar takardarka ta gama sakandire bai wuce shekaru 5 ba. Idan kuma ya wuce sai ka sake rubuta ko samun wata jarabawar.
3- Ana samun takiyyah ne a wurin daya daga cikin wadannan: Kungiyar addini(kamar izala), ko wanda keda matsayi na phd ko farfesa a fannin da mutum keso ya karanta(amma anfiso asamu daga wanda yagama ita jami’ar Madina din), ko makarantar da dalibi yagama, ko wani majlisi na karantarwa da ya’da ilmi, ko wata cibiya ta ilmi, ko kuma wani sanannen mutum a cikin al’ummah. Amma gabadayan wadannan yakamata su rubuta tazkiyyar a letter headed paper ne.
4- Ana samun medical report ne a asibitin gwamnati wanda a ciki za’a bayyana cewa mutum lafiyarshi kalau baya dauke da wata cuta daga cikin muggan cututtuka irinsu HIV, Diabities, Hypertension, Dialysis, Heart Diseases da makamantansu, tareda nuna blood group na mutum da genotype da height.
5- Ka tabbatar sunayenka iri daya ne a dukkan takardunka, hakama shekaru.
6- Ga wadanda ke son rubuta jarabawa na TOEFEL ko ICDL anayin gabadayansu a Abuja, amma akwai wasu jihohi da suma akeyi, kamar Kaduna da makamantansu. Idan za’a rubuta sai a bincika.
7- Yakamata mutumin dayayi applying ya rinka bibiyan application din lokaci bayan lokaci, sannan yasamu wani daga cikin dalibai na jami’ar yabashi application number dinsa domin ya rinka fadin masa halin da application dinsa ke ciki.
8- Wajibi mutum ya kula da application number dinsa, idan zai yiwu ma ya rubutashi a wurare dadama domin gudun salwantarsa.
9- Idan anyi applying sai shekara ta zagayo akeyin admission.
10- Idan mutum yanada hali bayan yayi applying zai iya zuwa a matsayin mai umrah ko mai aikin hajji(idan lokacin hajji ne) sai yayi abunda ake cewa MUQABALAH (wato INTERVIEW) a jami’ar, domin yin hakan yana daga cikin abubuwan dake kara armashin samun admission, amma ba lallai bane, domin ana samun dalibai dadama da ake daukansu ba tareda sunzo sunyi interview din ba.
11- Sannan mutum ya rinka yawaita addu’a, domin Allaah ne kadai ke iya sa a dauki mutum ba wani ba.
A KARSHE IDAN ALLAAH YASA MUTUM YA SAMU ADMISSION TO KOMAI KYAUTA NE, TUN DAGA TASOWARSA DAGA KASAR SU HAR ZUWA KARATUNSA DA KAYAN KARATU DA ABINCI DA ABIN SHA DA TUFAFI DA KOMAI DUKA KYAUTA NE. KASAR TAUHIDI SAUDIYYAH ITACE ZATA DAUKEWA DALIBI KOMAI.
MUNA ROKON ALLAAH YASAKA MATA DA ALKHAIRI, MU KUMA YABAMU DAMAR CIN MORIYAR WADANNAN ALKHAIRAN.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s