ABOKI!

Annabi SAW yana cewa:-
Mutum yana tafiya ne akan dabi’ar Abokin sa. Don haka kowa a cikin ku ya duba yaga da wa ya kamata yayi abota.
Sayyadina Umar Allah ya kara masa yarda yana cewa:-
Babu wata ni’ima bayan ni’imar musulunci da ta wuce abaka aboki nagari. Don haka
duk wanda ya dace da aboki nagari a cikin ku yayi riko dashi Qaaam.
Imamul-shafi’I Allah ya jikan sa da rahama yana cewa:-
In Allah ya azurta ka da aboki nagari to ka rike shi Gam da hannunka. Domin samun
Aboki nagari abune me wahalar gaske, kuma rasa shi abu ne mai saukin gaske.
Imam Hasanul Basari yana cewa:-
Muna son Abokan mu nagari fiye da yanda muke son Iyalanmu da ‘ya’yan mu. Domin
iyalan mu da ‘ya’yan mu suna tuna mana Duniya. Shi kuma Aboki Nagari yana tuna mana Lahira ne. Yace yana daga Siffar Aboki nagari ya fifita bukatarka akan tasa bukatar. Luqmanul Hakim yake cewa da ‘Dansa.
Ya kai ‘Dana farkon Abunda zaka tsururuta arayuwar ka bayan imani da Allah
shi ne Aboki nagari. Domin Aboki na gari tamkar bishiya ce, in ka zauna a kasanta,inuwarta ta lullubeka gabarin Rana. In ka tsigi Dan itacenta ta kosar da kai daga yunwa. In har bata anfanar da kai ba kuma bazata taba cutar da kai ba. Allah ka bani Aboki nagari, kasa in zama nagari da kuma sauran al’ummar musulmai gaba
daya…….duk aboki nagari zai so wannan sako zuwa ga abokinsa don ya samu falalar abin da zai zama alkhairi a gare shi…da musulunci da musulmai.
GODIYA GA ABOKAINA NAGARI!!!

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s