ZEENATU MATAR ZAKZAKY

Yasir Ramadan Gwale

Tunda kake baka taba jin wani Ahlussunnah ya buda baki ya ce ZEENATU matar ZAKZAKY Iblishiya ba ce, ko ya ce mata Kilaki ko ya zagi ubanta ya ce masa Munafuki ko algungumi. Haka kuma, na tabbata da Zakzaky ya san uban matarsa fitsararre ne mutumin banza na tabbata ba zai auri ‘yarsa ba. Tarbiyyar Ahlussunnah ce kare mutunci da darajta Mata, ballantana kuma matan aure.
Duk d’a na gari ba zai so a zagi uwarsa ba, dan haka yake girmama uwar wani, dan sanin kima da darajar tasa gyatumar. Ko kusa ba tarbiyyar Sunnah bace zagin mata bare kuma katangaggun mata.

To yanzu sabida Allah, mutanan da ba zasu iya buda baki su yi mummunan kalamai akan Zeenatu Matar Zakzaky ba, sune zasu bude bakin su me wari su zagi Nana Aisha da Hafsah Matan Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Hasbunallahu Wani’imal Wakeel!

Mutanan da basa zargin Jagoran su El Zakzaky da auren matar da bata dace ba, su ne kuma zasu ce wai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya auri matan da basu dace ba! Har suna zaginsu tare da tsine musu. Ya Allah Kada ka kama mu da laifukan wawayen cikinmu.
Kuma a haka wasu rikirkitattu suke tunanin mu gamsu mu yadda cewar ‘yan Shiah Musulmi ne muyi tarayya da su? Yanzu idan ace Mu Ahlussunnah muna zagin uban Zeenatu tare da tsine masa Albarka, shin wace riba zamu samu?
A haka, kuma wasu ke tunanin muyi shiru sabida an zagi Matan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam da iyayan su, wadan da sune AminanSa Sallallahu Alaihi Wa Sallam.
Ya Allah ka kare mu daga fadawa Halaka da Tab’ewa ka kare mu da zurriyar da Shianci. Allah ka shirye su, su fahimci gaskiya su koma mata. Wallahi Summa Tallahi Shianci bata ne, duk wanda yabi Shiah ya Halaka. Allah ka kiyashe mu.

Yasir Ramadan Gwale
14-09-2016

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s