KU JI TSORON ALLAH KU DAINA RIYA!

Daga: Abdurrahaman Abubakar Sada

Aikin Hajji Ibadah ce, kuma dukkanin Ibada don Allah kaďai ake yi ba don talla (nunawa mutane) ba.
******************************
Amma yau mun wayi gari musamman wajen Aikin Hajji ko Umrah, idan Allah ya yi wa mutum arzikin tafiya, ya na isa Airport, sai ya dauki hoto ya ce; ga shi nan akan hanyarsa ta tafiya kasa Mai tsarki, in aka shiga cikin Jirgi, sai ya dauki hoto ya ce; ga ni a cikin Jirgi, in aka sauka kasa Mai tsarki, sai ya samu wuri Mai kyau ya yi hoto ya ce; ga ni a Saudi Airport, ko ga ni ina jifar Shaidan, sai ka ga mutane su na ta daukar hotunan su su na sanyawa a “Social Media” wai da sunan a taya su addu’a. Ko ka ga mutum ya dauki Al Qur’ani an dauke hoto ya na nuna wa Duniya wai ga shi a cikin Masallacin Annabi Muhammad (S.A.W), ko ga shi a Arfa, Wannan shi ne hakikanin ma’anar ‘YURA’UUNAN NAASA”, (su na yi don a gani, kuma an gani sai me).
******************************
Allah Ya sa mu gyara ko ayyukan mu sa samu shiga. Amin.
.
Abdurrahaman Abubakar Sada.
30/Dhul-Qa’adah/1437.
02/September/2016.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s