KABBARORIN IDIN AZUMI DA IDIN LAYYA

Ibrahim Jalo Jalingo

Yin kabbarori a bayyane a zamunan Idin azumi, da Idin layya abu ne da yake sunnar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah.
*************

KABBARORIN IDIN AZUMI:

Lokacin da ake yin kabbarorin a Idin azumi yana farawa ne tun daga lokacin da aka ga watan Shawwal a farkon daren Idi, za a kuma ci gaba da yin kabbarorin har zuwa lokacin da liman zai fara sallar Idi.
Su kabbarorin Idin azumi ana yin su ne ba tare da wani kaidi ba; watau Musulmi zai rika yin su a bayyane cikin masallatai, da gidaje, da kasuwanni, da hanyoyi.
************

KABBARORIN IDIN LAYYA:

Amma su kabbarorin Idin layya akwai wadanda za a yi su a bisa kaidi, akwai kuma wadanda za a yi su ba tare da kaidi ba.
Wadanda ake yin su a bisa kaidi su ne wadanda ake yin su bayan ko wace sallar farilla tun daga sallar Asubahin ranar Arafah har zuwa sallar La’asar a ranar karshe na kwanukan tashriiq; kwanukan tashriiqi su ne 11, da 12, da 13 ga watan Zul Hijjah.
Kabbarorin da ake yin su ba tare da kaidi ba kuma su ne: wadanda ake yin su cikin masallatai, da gidaje, da kasuwanni, da hanyoyi, da gurare masu kama da wadannan. Su wadannan kabbarori mara kaidi ana fara yin su ne tun daga lokacin da watan Zul Hijjah ya kama har zuwa karshen kwanukan tashriqi.
**************

SIGAR WADANNAN KABBARORIN:

Babu wani nassi sahihi daga Annabi mai tsira da amincin Allah da ya zo da wata ayyanannar siga ta wadannan kabbarorin, to amma Malamai sun ba da wasu sigogi kamar haka:-
1. Allahu Akbar, Allahu Akbar, Laa’ilaaha illallahu, Allahu Akbar, Allahu Akbar. Wa Lillahil hamd.
ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ .
2. Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Laa’ilaaha illallah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar. Wa Lillahil hamd.
ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ .
3. Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Laa’ilaaha illallah. Allahu Akbar, Allahu Akbar. Wa lillahil hamd.
ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﻻ ﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻛﺒﺮ، ﻭﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ .
Muna fata Allah Ya taimake mu. Ameen.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s