Dakta Ahmad BUK Ya Kammala Karatun Hadisan Manzon Allah (Kutubus Sitta) Bayan Tsawon Shekaru 24 Yana Karantarwa.

Daga: Salihu Mu’azu Koki

A jiya Asabar 1 ga watan Zulhijja 1437 ne Babban Malamin Hadisin nan Dr. Ahmad BUK ya kammala karantar da “KUTUBUS-SITTA” manyan littattafan hadisin nan guda shidda (6) wato :
-Bukhari.
-Muslim.
-Tirmizi.
-Abu Dawud.
-Nasa’i.
-Ibn Majah.
Bayan shafe shekaru 24 yana yiwa Sunnar Annabi SAW hidima, an fara wannan karatu ne aranar 02 ga watan Nuwamba, 1992, a cikin jami’ar Bayero BUK, wanda aka kammala a jiya Asabar.
Wannan ba karamar baiwa bace domin a cikin malaman musulunci ‘yan kadan ne Allah yake musu wannan baiwar.
Idan Allah ya kai mu bayan Sallah Malam zai saka littafin “MUWADDA” na imamu Malik.
Muna rokon Allah da sunayan sa tsarkaka, da sifofinsa madaukaka kamar yadda ya albarkace shi da lafiya (domin kuwa duk da yawan shekarun sa, idonsa yana gani tar, kuma yana tafiya da kafafun sa, batare da yadogara sanda ba, wannan baiwa ce ta ubangiji) Allah yakareshi da lafiya, yasakawa Dr. Ahmad da Jannatul Firdausi, ya karbi wannan aiki daya gabatar, ya albarkaci bayan sa.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s