HAKA TA KUSA CIMMA RUWA!

Daga: Danladi Haruna
.
Daga alamun da na gani yau a kasuwa, nan gaba kadan farashin kayan abinci zai zubo kasa warwas. A lokacin ne za #MuganiAkasa na hakika. Kusan duk inda ka duba ‘yan kasuwa ne manya da kanana sun kasa hajar kayan abincinsu suna jiran masu saye. Babban abin da ya fi yawa a wurin shi ne shinkafa, sai doya, sai makaroni da taliya da garin kwaki da kubewa da sauran kayan cimaka.
.
Kowanne dan kasuwa ya zuba wa sarautar Allah ido yana jiran mai saye ya zo ya siya. Watakila saboda karancin kudin da ke hannun jama’a ne ya sa cinikin ke tafiyar hawainiya duk da cewa jama’a na cikin tsananin bukatar abincin. Ni dai na tambayi farashin garin kwaki kuma na ji ya sauko a kan yadda na saya satin da ya wuce. Sauran kuwa ban taya ko daya ba, tun da ba ni da abin saye!
.
A bisa ka’idar saye da sayarwa, duk lokacin da farashin abu ya yi tashin gwauron zabi sakamakon karanci ko yawan bukata da jama’a ke yi, to masu sayarwa kuma za su yi ta zagayawa suna lalubo abin bisa kwadayin su sayar su samu riba. Daga nan idan abin ya yawaita, sai kuma cinikinsa ya ragu, sai kuma farashin ya zubo kasa har zuwa daidai yadda mai saye zai ji cewa abin bai yi tsada ba. Wannan ka’ida masa tattalin arziki ke kira ‘equilibrium’. Yanzu kuwa, manoman shinkafa sun yawaita, masu sayar da ita na karuwa yayin da masu bukatarta na raguwa.
.
Sai dai matsalar ‘yan kasuwar kasashenmu, kullum lissafinsu shi ne samu riba ta kowacce fuska. Da zarar farashin abu ya samu kari, su ma sai su kara wa nasu kudi duk da cewa tsohon saye ne. Idan kuma farashin ya sauko sai su ki saukar da nasu bisa hujjar wai asara za su yi. Wannan ya saba wa dokar ciniki a musulunci, kuma ya saba wa dokar ciniki a yahudanci da zamananci.
.
Yadda suke aukawa irin wannan haramcin kuwa, da zarar sun samu labarin cewa farashin abu kaza ya samu kari, nan da nan sai su lissafa wanda ya rage a hannunsu. Su lissafa ribar da za su samu. Idan sun lissafa ribar sai su kwashe adadin kudin su yi bushashar su ba tare da la’akari da abin da ka je ya zo ba. Wannan ta sa idan an samu saukar farashin abu ba sa iya sauko da kayansu, a karshe su shiga sawun wadanda Allah ke fushi da su sakamakon gallazawa bayinsa.
.
Marigayi Danmaraya Jos yana cewa a wata wakarsa.
.
Haba ‘yan kasuwar kasar nan,
Ku daina boye kayan abinci,
Tare da kayan sana’a.
.
Ribar taro da sisi,
Ku ce sai an ba ku goma
Kayan kun aje a shago,
Wani kan teburi ya sanya,
Wani ko ya aje a daki,
Wani kyankyaso ya bata,
Wani sannan gara ta taushe,
Wani ko ruwan sama ya bata,
Jari ya zo ya karye,
Ribar da uwar duk su kare,
To kun ga kun asara,
Haba ‘yan kasuwar kasar nan
.
Ya kamata nan gaba gwamnati ta sa doka, duk wanda aka samu da laifin boye abinci da zummar sai ya yi tsada zai fito da shi, to a kwace kayan a rarraba wa talakawa sadaka.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s