JAKADAN SAUDIYYA A NIJERIYA YA ZUBDA HAWAYE DON TAUSAYIN WATA MATA


Daga Yasir Ramadan Gwale

Mai Girma Jakadan Sa’udiyya a Najeriya, Sheikh Fahad Abdallah Sufyan, ya kadu matukar kaduwa sakamakon wani rahoto da ya karanta wanda Jaridar Daily Trust ta wallafa a ranar 13 ga watan Agusta 2016. Rahoton an yi masa taken, “Meet Kaduna Lady Who’s Raising 5 Abandoned Babies” wato labarin wata mata da ta kula da rayuwar yara biyar tsintattu. Jakadan ya kadu ainun bayan karanta wannan Rahoto, inda ba da bata lokaci ya bukaci Ustaz Abubakr Siddeeq wanda shi ne Limamin Masallacin Abuja da yake Fassara huduba da Turanci, inda ya tambaye shi ko yaga rahoton da Jaridar ta buga. Inda Ustaz Siddeeq yace bai karanta ba. Nan da nan Jakadan ya turawa Ustaz Siddeeq hoton shafin jaridar da ya dauka a wayarsa ta Whatsapp dan ya duba ya gani. Jakadan ya kuma, bukaci Ustaz ya binciko wannan mata tare da shirya masa yadda zai gana da ita ido da ido.

Labarin dai na wata mata ce mai suna Hajiya Uwani Yusuf Waziri, wadda aka fi sani da Uwar Marayu. Wannan mata mazauniyar unguwar Kaji ce a jihar Kaduna. Tana da ‘ya ‘ya goma sha daya, duk da irin halin da take ciki, ta dauki gabarar kula da tarbiyyar yaran da aka tsinta ta rike su a matsayin ‘ya ‘yan ta. A duk lokacin da aka tsinci jariri a unguwannin Rigachukum ko Barakallahu ko Hayin Na Iya a kasan gada ko cikin Lambatu akan kai su gidan Hakimi, nan take shi kuma Hakimi zai tura da jairin da aka tsinta zuwa gidan Uwar Marayu.

Ina cikin garin Kaduna a lokacin Jakada Sheikh Fahad Abdallah Sufyan ya bani wannan umarni. Dan haka abin sai ya zo min da sauki wajen tuntubar yadda zan hadu da wannan mata. Dan haka ne na samu abokina Dr. Mahadi Shehu wanda shi ne Shugaban Kamfanin Dialogue Global Links tare da gudunmawar Maryam Ahamadu – Suka wadda ta hada wannan rahoto da tallafawar Rufa’at Maccido muka kai ga wanna mata.

Bayan da muka yi katarin gamuwa da Hajiya Uwar Marayu, muka sanya ranar Laraba 17 ga watan Agusta 2016, domin ganawar wannan mata da Jakada Sheikh Fahad Abdallah Sufyan da Misalin karfe 11 na safe a Birnin Tarayya Abuja. A lokacin Maryam da Hajiya Uwar Marayu sun zo tare da daya daga cikin marayun da wannan mata take raino mai suna Zainab, wadda take cikin zanin goyo. Mai Girma Jakadan Sa’udiyya Sheikh Fahad, ya yi mana tarba ta musamman a ofishinsa, ya marabcemu da Shayin Larabawa na Gahwa da Dabino. A lokacin nayi kokarin zubawa kowa da kaina, amma Jakadan yace kar na damu zai zubawa kowa da kansa dan girmama Uwar Marayu. Bayan ya gama zubawa kowa Gahwa, ya kalli Zainab a cikin zanin goyo yace, yanzu wannan jariri bai yiwa kowa laifi ba na zuwan sa duniya amma an yasar da shi.

A lokacin da Jakada Sheikh Fahad, yake bayani idanunsa sun cika da kwalla, zuciyarsa ta raurawa. Yayi ta kokarin yin magana amma ina kukan da yake a zuciya yaci karfinsa, inda ya kasa hadiye hawayen da suke kwaranya a kumatunsa. Ganin haka, sai na Mikawa Jakada audugar share Gumi dake kusa da ni, dan ya goge hawayen da suke guda a kuncinsa. Dukkanmu da muke zaune a wannan waje, muka kasa jurewa, zukatanmu suka raurawa hawayen tausayi ya dinga bayyana a fuskokin mu, adaidai lokacin, Zainab dake cikin zanin goyo da bata san meke faruwa ba, ta fa she da kuka, abinda ya kara tsinka mana zukata, nan dai Uwar Marayu ta shayar da ita Madarar da ke tare da ita, wadda ke zube a cikin Bulumboti.

Haka nan, Sheikh Fahad Abdallah, yayi karfin hali ya fara magana cikin murya mai cike da nuna tausayi da damuwa. Yace, masu Imani sune suke jibantar lamarin ‘yan uwansu musamman wadan da suke cikin tsananin bukata. Kamar marayu da mata da aka mutu aka barsu da yara. Wadannan sune suka cancanci a taimaka musu. Ya k’ara da cewar, Manzon Allah Tsira Da Amincin Allah su k’ara Tabbata a gareshi ya ce, Ni da wanda yake jibantar al’amarin Marayu kamar yatsu ne guda biyu, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam yana mai nuni da yatsunsa biyu. Ya cigaba da bayani yana cewa; Watarana wani mutum yazo wajen Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, yake ce masa, Ya Rasulullahi zuciya ta na fama da kunci da damuwa haka kurum, Manzo yace da shi, ka jibinci al’amarin Marayu ka ciyar da su daga abinda kake ci, Allah zai saukaka maka lamarinka, zuciyarka zata samu nutsuwa.

Jakada Sheikh Fahad, ya cigaba da cewa, Hajiya Uwar Marayu kin cancanci jinjina da Yabo, kuma kin cancanci ayi koyi da ke, kin zama zak’ak’ura a cikin matan Najeriya. Ya cigaba da bayanin cewar, duk wanda ya yayewa wani damuwa, Allah zai yaye masa damuwa ranar tashin Alkiyama. Ke uwar marayu ce, ina tunasar dake Hadisin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam da yake cewa zamu shiga Aljannah tare da shi, yayi mata nuni da yatsunsa biyu; duk wanda ya jibanci al’amarin Marayu.

Bayan da ya gama gajeriyar tunasarwa. Ya mikawa Hajiya Uwani Uwar Marayu wata gagarumar kyautar da ya bukaci kada a bayyanawa duniya kyautar da yayi mata. Sannan ya yiwa Marayun da take raino Goma ta Arziki. A hakikanin gaskiya zan iya cewa wannan kyauta da yayi musu Takai ta kawo duk da ya roki Alfarmar kada na bayyana abinda ya bayar, amma ya yiwa Uwar Marayu kyauta mai girma. “Wanda duk ya taimaki wani, shima Allah zai taimake shi ya jibanci lamarinsa.”

Wannan abinda Jakadan Sa’udiyya ya yiwa wannan mata Hajiya Uwani Uwar Marayu ya kamata ya zabarurar da al’ummar mu wajen tausayawa Marayu musamman jariran da ake haifa kuma a yasar da su akan titi ko cikin Lambatu. Mu yawaita kyauta da sadaka domin bamu san Me Allah ya yi mana tanadi na alheri ba. Allah Ta’ala ya fada a cikin Sura Ta Biyu Aya Ta 268, Shaid’an yana tsoratar da ku da talauci da fatara, yana kuma yi muku bushara da rayuwa mai tsawo. Allah kuma yayi muku alkawarin Rahama da sakamako mai gwabi. Allah shi ne Masani mai hikima”.

Hanzari: Wannan bayani Ustaz Abubakr Siddeeq ne ya yi a shafinsa na Facebook da Blogspot. Ni kuma na fassara shi zuwa Hausa. Allah ya sa mu dace.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s