Yadda Malamai ke wa’azi a shafukan zumunta.

Yadda Malamai ke wa’azi a shafukan
zumunta.

Daga: Nasidi Adamu Yahya

Tun lokacin da shafukan sada zumunta na
zamani suka bullo jama’a ke amfani da su
domin biyan bukatu daban-daban.
Mutane daban-daban, kama daga ‘yan kasuwa
zuwa shahararrun mawaka da jaruman fina-finai,
da masana kimiyya da ‘yan kwallo, da sauran su,
kan yi amfani da shafukan domin aikewa da
sakonni.
Wani rukunin mutane da ya bai wa wadannan
shafuka muhimmanci kuma shi ne malaman
addini.
Fitattun shugabannin addini irin su Paparoma
Francis sun riki wannan hanya domin aikewa da
sakonni ga mabiyansu, kuma a yanzu haka yana
da mabiya kusan miliyan goma a shafinsa na
Twitter.
Haka batun yake ga malaman addinin Musulinci
ma, inda fitattun malamai irin su Mohamed Al-
Arifi ke kan gaba a cikin malaman addinin Islama
na Saudiyya da ma duniyar Musulmai da ke da
kwarjini a shafukan sada zumunta.
Mohamed Al-Arifi yana da mabiya sama da
miliyan goma sha biyar a shafinsa na Twitter
Wasu daga cikin abubuwan da ya fada a kan
mata su kan jawo ce-ce-ku-ce.
Baya ga al’amuran yau da kullum, Al-Arifi yana
bayyana ra’ayoyi a kan siyasar yankin Gabas ta
Tsakiya.
A Najeriya da sauran kasashen Afirka ma, akwai
malamai da dama da ke rungumar wadannan
shafuka domin isar da sakonni ga mabiyansu.
Malam Isa Ali Pantami, wani fitaccen malamin
addinin Musulunci ne da ke amfani da shafukan
sada zumunta wajen yin wa’azi da gudanar da
muhawara a kan batutuwa da dama.
Ya shaida wa BBC cewa babban abin da ya sa ya
rungumi wadannan shafuka domin yin wa’azi shi
ne, “Kasancewar addinin Musulunci wayayyen
addini, wanda ke tafiya da zamani. Shi ya sa
yake da kyau mai yin wa’azi ya san duniyar da
yake rayuwa a cikinta saboda maganarsa ta dace
da al’umma”.
Malam Pantami ya kara cewa, a baya wasu
Malaman addinin Musulinci sun bayar da fatawar
da ke nuna rashin dacewar amfani da shafukan
sada zumunta na zamani wajen isar da sako,
amma daga bisani suka ga amfani shafukan,
lamarin da ya sa suka sauya ra’ayoyinsu a
kansu.
Shi ma Fasto Sam Adeyemi, wani fitaccen
malamin addinin Kirista, ya mayar da hankali
sosai wajen yin kira ga mabiyansa ta shafinsa na
Twitter.
Malamin cocin ya shahara sosai wajen fadakarwa
da kuma jayo hankalin mabiyansa a kan
muhimmanci riko da gaskiya da kuma bin dokokin
kasa a shafin nasa.
Fasto ne mai bai wa matasa dama su gina
rayuwarsu da kuma hanyoyin da za su bi domin
bunkasa rayuwarsu a wannan zamani mai cike da
rudani.
Wani malami da ya yi fice wajen amfani da
shafukan sada zumunta a Najeriya shi ne Sheikh
Aminu Ibrahim Daurawa.
Malamin, wanda kuma shi ne shugaban hukumar
Hisba ta jihar Kano da ke arewacin kasar, yana
yawaita amfani da shafukan domin aikewa da
nasihohi da fadakarwa ta hanyar wallafa ayoyin
Al-Kur’ani da hadisan Manzon Allah, Annabi
Muhammadu (S.A.W) da kuma fahimtar malamai
a kan matsalolin rayuwa da yadda za a shawo
kan su.
Malamin yana da mabiya kusan dubu dari uku a
shafinsa na Facebook, wadanda kuma ke yi masa
tambayoyi a kan abubuwan da shuka shige musu
duhu.
Menene ra’ayinku kan amfani da shafukan sada
zumunta da Malamai ke yi wajen yin wa’azi?

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s