NDLEA ta cafke mutane uku dauke da hodar ibilis a sansanin ‘yan gudun hijira dake Maiduguri.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA ta cafke wasu mutane uku da hodar ibilis da ake kira koken a daya daga cikin sansanin ‘yan gudun hijira dake cikin birnin Maiduguri

Shugaban hukumar NDLEA na jihar Borno Barrister Joseph Ona shivya shaidawa manema labarai a wani taron fadakarwa akan illar shan miyagun kwayoyi da suka gudanar a birnin Maiduguri.
Yace yawaitar ta’ammali da miyagun kwayoyi
abu ne mai tada hankalin gaske ganin yadda
ake yawan kama tabar wiwi da hodar iblis da
ake kira koken.
Da yake magana akan wadanda suka kama a
sansanin ‘yan gudun hijira da hodar iblis yace
nan ba da jimawa ba zasu gurfanar dasu a
gaban shari’a. Baicin mutanen uku da suka
kama da koken a sansanin ‘yan gudun hijiran
sun kuma kama wasu 16 dake yin anfani da
tabar wiwi duk a sansanin.
A cikin garin Maiduguri sun kama wani mutum
wanda ya boye tabar wiwi mai nauyin kilo dari
da goma sha biyu a cikin gidansa lamarin da ya
nunawa hukumar cewa ana hada-hadar tabar
wiwi a tsakanin al’umma.
Barrister Joseph Ona yace ba zasu yi kasa a
gwuiwa ba wajen ganin sun rage irin
wadannan miyagun mutane dake bata tarbiyan
al’umma.
Abun takaici, hukumar ta kama wasu ‘yan
Civilian JTF guda uku da suka fito daga garin
Kareto na karamar hukumar Mobar da motar
Civilian JTF ta karamar hukumar suna dauke
da wasu layu da makamai tare da tabar wiwi a
cikin motar.
Shugaban kananan dillalan masu sayarda
magunguna a jihar Borno ya yi bayani akan
mahimmancin taron. Sun shirya taron ne
domin wayar da kawunan jama’a akan illar da
shan kwaya ke yiwa matasa. Maganin da
yakamata a sha domin warkaswa matasan
suna sha domin su bugu.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s