Dalilin Da Ya Sa Na Karbi Musulunci, Inji Uwargidan Gwamnan Jihar Ogun.

Uwargidan gwamnan jihar Ogun, Olufunsho Amosun
ta labarta yadda ta samu kanta cikin musulunci
bayan auren ta da gwamnan, Sanata Ibikunle
Amosun.
A cikin wata hira da jaridar Vanguard, uwargidan
gwamnan ta ce “farkon wanda na fara bayyanawa
aniya ta ta auren musulmi ita ce mahaifiyata. Farko
sai ta fashe da kuka sannan ta tambaye ni ko na
gayawa mahaifina wanda babban fasto ne na ce a’a.
“Amma a yau, mahaifiya ta da miji na sun zame
mini manyan abokai. Wani lokacin mahaifiyata ta
kan yi raha da maganar idan ta tuna.
“lokacin da na gayawa mahaifi na sai ya ce wannan
abu ne na addu’a. amma ni abunda na fahimta
shine, miji na yana da matukar imani. Kuma na san
miji na bai yi imani da komai ba sai Allah.”
Da aka tambaye ta ko mijin ta ya musuluntar da ita
ne da karfi tsiya, uwargidan gwamnan sai ta kada
baki tace “ muna zaune cikin aminci kuma muna yin
abu tare. Idan lokacin Sallah ya yi zan ce wa ‘ya’ya
na su tashi maza su yi sallah. Su kuma sai suce
momi me ya sa ke bakya sallah tare da mu, ko
baban mu ba addinin kwarai yake bi bane.
Daga nan ne na zauna na yi tunani mai zurfi, cikin
kankanin lokaci na fara sallah ni ma na zama
Musulma. Sauran dogon labari ne amma ni na zabi
musulunci,” inji Amosun.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s