Darulfikr.com Taku ce Domin Yada Sunnah!!!

(‘ياايها الذين امنوا ان تنصرالله ينصركم ويثبت اقدامكم’)

image

DarulFikr Shafi ne da aka samar dashi domin Yada Sunnah acikin Ikon Allah Yanzu Haka DarulFikr Tana kawo muku karatukan Malamai sama da Guda 60 Kuma ko wane Lokaci Adadin yana Iya Karuwa zuwa sama da haka, Banda wadanda take kawo Hudubobin su da Kuma Lakcoci baya ga Adadin Maziyarta da yake ta Karuwa a Kowane Lokaci babu dare ba Rana Hakama Adadin Masu downloading ako ina a Fadin duniya,

DarulFikr Tayi Yan Gyare-Gyare a Satikan da suka wuce,

-Ta samar da (mp3 Player) Tun a kwanakin Baya,

1, Darulfikr mp3 Player,
Zata Baka damar sauraron Karatuttuka da Lakcoci da Hudubobi na Malamai daban-daban a kowane Lokaci sannan kai zaka Iya Controling dinta da kanka zaka iya zabar malamin da kake so da kuma Littafin da kake son sauraro,

A Ina zan ganta Kuma ta yaya zanyi Controling dinta???

Da zarar ka shiga darulfikr.com zaka ga Alamar Media Player (Alamar wajen sauraron karatu na wayarka ko na Casset ma’ana Alamar Farawa da Tariya da tsayarwa to kana danna Alamar Farawa zata fara nan take zakaji karatu na tashi a hannuka na hagu zakaga wata alama sai ka danna zata Baka zabi na malamai daban-daban sai ka zabi wanda zaka saurara In kuma ka kyale ta ma da kanta zata yi ta zabo maka karatuttuka da wannan ya gama sai kaji wannan قال الله قل الرسول، عليكم بسنتي……. haka zakai ta sauraron maluman sunnah wadanda ka sani da wadanda Baka sani ba haka nan in ka danna Alamar ‘Next’ zata zabo maka wani karatun, sannan wannan mp3 Player tana aiki 24 Hours babu dare babu rana,

2, Recent Update: Shine Yadda zaka dinga ganin Posting na Sababbin Karatuttuka da muka saka Misali in kaje darulfikr.com a can kasa zaka ga Recent Update: zaka ga posting na duk karatukan da mukayi posting a wannan satin in kayi ta shiga see more zakayi ta ganin sauran posting dinmu daya bayan daya ma’ana Idan anyi sabon karatu Ko Lakca Ko Saminar ba sai ka sha wahalar nemanta ba zaka ga posting dinta,

3, Article: Yanzu a Darulfikr.com Ta samar da wajen ajiye rubutuka ma’ana zamu dinga sanya posting masu ma’ana wato bayan downloading din karatu ynx har karatu ma zaka iya yi a darulfikr zakai ta ganin rubutuka masu matukar fa’ida rubutukan da suka shafi Sunnah,

4, Event: Yanzu darulfikr.com ta samar da Bangaren Isar da sanarwar wani taro ko Lakca da sauransu ynx dai Idan za’ai wa’azi ko an daga shi ko wani karatu da za’ai zamu dinga sanyawa Baka da matsalar kiran wani da zarar darulfikr ta samu Tabbaci zata sanyamuku kawai ka Matsa http://www.darulfikr.com zaka samu Ingantaccen bayani, Wannan bangare kaima zaka iya bada sanarwar wa’azinku a saka kuma zaka ga adadin wadanda suka ga Wanann sanarwar,

•••Bayanai Ko kuma Nace Wayar dakai:

1, Masu Matsalar Downloading a Darulfikr.com

-Da farko dai darulfikr site ne da yana da yawan Visitor’s da kuma yawan abubuwan da za’a samu to Yan uwa Irina masu kananan wayoyi da kuma yayyen mu Masu manyan wayoyi kowa yana son ya ziyarta To don saukakawa mun raba link na kowane file dinmu zuwa link guda biyu,

1, Link na farko da muke sanyawa dukkan masu amfani da Computer Ko Manyan wayoyi Kirar Smartphones, Ipad Tablet da sauransu wanda ke amfani da Browser masu kyau (na zamani) sai subi ta kansa,

2, Link na Biyu Yan uwana masu kananan wayoyi ko masu Irin opera dinnan gama gari sai subi ta kan sa suma zasu samu Lafiya-Lafiya,

-Mai Link Na Farko In zai ziyarci darulfikr sai ya saka www.darulfikr.com

-Mai Link na Biyu Idan zai ziyarci darulfikr yana da kyau ya saka www.darulfikr.com/mobile To zaiga abun cikin sauki,

Da fatan yan uwa sun fuskanta,

2, Wasu Yan uwa sukan tambayemu akan Basu ga Malam wane a Darulfikr.com ba, Ko last week wani dan uwa ya tambayeni wai shin darulfikr an kebancetane don wasu malamai kadai??

-To Yan uwa darulfikr ta Dukkan Ahlussunnah ce ba kuma akebance na wani guri ba Taken mu shine Darulfikr.com Takuce Domin yada Sunnah ba kuma ta iya wasu bace dukkan Ahlussunnah Kaima kana da damar mu’amala da darulfikr kuma Malami ko a ina yake In har ya karantar da Sunnah In muka samu to zamu sanya, manufarmu dai Har Kullum itace Yada Sunnah,

-Abin da yasa Baka ganin Malam wane shine:

Muna da yawan Malamai Misali zaka bude darulfikr kaga malamai guda goma wasu ma tayiwu duk Baka san su ba To a karshen maluman zakaga ‘See More’ sai ka danna zai ta kawo maka Maluman daban-daban Haka zakayi ta ganin su, Sbd idan akace dukkan maluman su kawo a page guda to loading din zai yi yawa saidai akwai tsare-tsare mai kyau da darulfikr zatai domin kara kusanta ku da karatukan na Maluman sunnah,

Abu na Biyu da zaisa Baka ga malam wane ba shine:

Tana iya yiwuwa bamu da karatun nasa ko kuma bamu sanshi ba amman kai ka sanshi to zaka iya taimakawa ka bamu karatukansa koda a CD ne ko ka turomana ta inda kake da dama Kaima kana iya taimaka mana da hakan Cibiyar dai Jihar Kano ce,

•Sannan a yanzu haka Darulfikr Tana tsare-tsaren gabatar da wadansu abubuwan masu matukar fa’ida a gareku sababbin tsare-tsare na musamman da zasuyi matukar amfani wajen yada sunnah,

A karshe DarulFikr tana mika godiya ga Malaman mu Sheik Abdulwahab Abdallah (Imamu Ahlussunnah Wal’jama’ah) da Sheik Muhd Rabi’u Umar R/lemo, Sheik Abubakar Abdussalam (Baban Gwale) bisa ga kwarin gwiwa da muke samu daga garesu muna Addu’ar Allah Ya saka musu da mafificin Alkhairi.

DarulFikr Takuce Domin Yada Sunnah!!

Karatukan Sunnah a Tafin Hannunku!!
Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah).
25/03/1437H, 06/01/2016M.

Advertisements

8 Replies to “Darulfikr.com Taku ce Domin Yada Sunnah!!!”

  1. Aslm alkum.ina son karatun sharhus sunna na haifan.Wanda kunka watsa bai wuce hudu ba.ina bukatar sawran.jazakumul LAHU khairan

    Like

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s