Mukurkushe ‘yan Shia da Akai a Zaria, Yaki ne da ta’addanci.

image

Jibwis Nigeria ta leka kasar saudiyya, Inda ta
ruwaito wannan labari, kamar yadda Kuka sani
Wannan shine karo na farko da Sarki salman yayi
jawabi tun bayan murkurkushe ‘yan shi’a a
kwanakinnan. A tattaunawarsa da shugaba
Buhari ta hanyar wayar salula, sarki Salman ya
ambaci cewa kashe daruruwan yan Shia a birnin
zaria shima yaki ne da ta’addanci , kamar yadda
hukumar yada labarai ta kasar Iran ta shaida.
Kafar watsa labarai ta Ahlul Bayt ta ruwaito
cewa shugaban Nigeria Muhammadu Buhari yayi
tattaunawa ta wayar tangaraho ta takwaransa na
Saudi Arabia, Salman bin Abdul Aziz Al Saud.
A yayin tattaunawar, dukkan shugabannin guda
biyu sun mayar da hankali ne kan muhimman
alamura da suka shafi alaka tsakanin kasa-da-
kasa, gami da harkokin da ke faruwa a fadin
kasashen guda biyu.
Wannan de yazamto karona farko bayan afkawa
yan Shi’a da akayi a zaria da saudiyya tayi jawabi
ta hanyar jagoran kasar a kwanaki biyu dasuka
gabata. A wannan tattaunawa ne de sarkin ya
tabbatar da cewa kashe daruruwan yan Shi’a da
akayi a zaria, shima yaki ne da ta’addanci.
Kamar yadda Kafar yada labarai ta FARS ta
tabbatar.
Harwa yau, sarki Salman ya bayyana cikakken
goyon bayan gwamnatin saudiyyah kan yaki da
ta’addanci da kasar Nigeria ke yi a halin yanzu.
Sarkin yakuma kara da cewa Saudi Arabia zata
marawa Nigeria dake Afirka baya, biyo bayan
jerangiyar ta’addancin dake aukuwa a kasar.
Sarki Salman bai gushe ba yana nanata cewa
ayyukan ash-sha kamar ta’ddanci ba koyarwar
addinin islama bane. Haka zalika yakara da cewa
saudiyyah bazata yadda ta shiga sahun masu
katsalandan wa Nigeria ba, domin hakan ka iya
zama barazana ga tsaro da cigaban kasar.
Daga bisani shugaban Nigeria muhammdu Buhari
ya bayyana godiyarsa da jinjinawarsa ga sarki
Salman bisa kuduri da aniyar da gwamnatin
kasarsa ta dauka na hada hanu da Nigeria domin
magance barazanar tsaro da yaki da ta’addanci.
Shugaban na Nigeria Muhammadu Buhari ya
dauki alwashin ziyartar kasar ta saudiyyah a
kwana kwanan nan.

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out / Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out / Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out / Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out / Change )

Connecting to %s