HUKUNCIN KARBAR KYAUTAR IDIN KIRSIMETI DA CIN ABINCIN WANNAN RANA KAMAR YADDA SALAFUS SAA’LIH SUKA YI BAYANI.

1- Da yake Alhamis mai zuwa ne Kiristoci za su
fara abin da suke kira bukin kirsimeti (idin
kirsimeti)
wanda suke yin shi ko dai a ranar 25/12 M ko
kuwa a ranar 7/1 M.
2- Sannan da yake a Nigeria ana zaman cakuda
ne tsakanin su Kiristoci da kuma al’ummar
Musulmi.
3- Sannan da yake shi Musulunci addini ne da ya
bayyanar da hukuncin dukkan wani lamari da ya
shafi rayuwar dan Adam, ko dai ta hanyar nassi,
ko ta hanyar zahiri, ko ta hanyar ishaarah da
iimaai.
4- Sannan da yake akwai masu bidi’ah da dama
da ke halatta abin da Shari’ah ba ta halatta ba,
ko
haramta abin da Shari’ah ba ta haramta ba, lalle
ya dace a yi wa al’ummar Musulmi bayanin
hukuncin abin da ya shafi wannan Idi na Kirsimeti
ta bangarorinsa da ke iya shafar wasu al’ummar
Musulmi.
**************************
To amma kafin mu shiga bayanin wadannan
hukunce-hukunce ya kamata Musulmi su san
abubuwa
kamar haka:-
Na farko: Shi dai bukin kirsimeti wata bidi’ah ce
da bata da kiristoci suka kirkira sannan suka
maida
ita wata ibada da ake samun lada ta hanyar yin
ta -kamar dai yadda wasu Musulmi suka kirkiri
bidi’ar idin mauludi- Kiristoci sun kirkiri wannan
bidi’ar ce kuwa a shekarar miladiyyah ta 360,
watau
a cikin karni na hudu bayan haifuwar Annabi Isa
alaihis salam.
Na biyu: Ya kamata kowa ya san cewa ba ya
halatta Musulmi ya yi tarayya da wadanda ba
musulmi
ba cikin bukukuwansu na idi, watau ta hanyar
halartan wasu tarurruka da za su kira, ko ta
hanyar ba
su wani taimako domin karfafa idodin nasu,
wannan dai shi ne hanyar Salafus Salih –
Sahabbai, da
Taabi’ai, da Taabi’uttaabi’in- dalili kuwa shi ne:-
Imamul Baihaqii ya ruwaito cikin As-Sunanul
Kubraa hadithi na 19,334 cewa Sayyidina Umar
Dan
Khattab Allah Ya kara masa yarda ya ce:-
(( ﺍﺟﺘﻨﺒﻮﺍ ﺃﻋﺪﺍﺀ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﻋﻴﺪﻫﻢ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ku nisanci makiya Allah cikin idinsu)).
Intaha.
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Tamiyyah ya ce –
kamar yadda ya zo cikin Al-Mustadrak Alaa
Fataawaa
Ibnu Tamiyyah 1/108, da Mukhtasarul Fataawaa
Misriyyah1/517 :-
(( ﻭﻟﻴﺲ ﻟﻠﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﺍﻥ ﻳﻌﻴﻨﻮﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﺃﻋﻴﺎﺩﻫﻢ ﻻ ﺑﺒﻴﻊ ﻣﺎ
ﻳﺴﺘﻌﻴﻨﻮﻥ ﺑﻪ ﻋﻠﻰ ﻋﻴﺪﻫﻢ ﻭﻻ ﺑﺎﺟﺎﺭﺓ ﺩﻭﺍﺑﻬﻢ ﻟﻴﺮﻛﺒﻮﻫﺎ
ﻓﻲ ﻋﻴﺪﻫﻢ ﻻﻥ ﺃﻋﻴﺎﺩﻫﻢ ﻣﻤﺎ ﺣﺮﻣﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻟﻤﺎ ﻓﻴﻬﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻔﺮ ﻭﺍﻟﻔﺴﻮﻕ
ﻭﺍﻟﻌﺼﻴﺎﻥ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Musulmi ba su da damar su taimaka
musu cikin idodinsu, ko dai ta hanyar sayar musu
da
abin da za su karfafu da shi, ko ta hanyar ba da
hayar dabbobinsu domin su hau su cikin idinsu,
saboda idodinsu na daga cikin abin da Allah
Madaukakin Sarki da kuma manzonSa mai tsira
da
amincin Allah suka haramta, saboda abin da yake
cikinsu na kafirci da fasikanci da kuma sabo)).
Intaha.
Na uku: Babu wani wanda ya isa ya bugi kirji a
duniyan nan ya ce: ga tabbatacciyar wata da
rana da
aka haifi Annabi Isa alaihis salam a cikinta, sai
dai kowa ya fadi abin da yake zato kawai,
wannan
shi ya sa ma Kiristoci masu yin bukin ranar
Kirsimeti watau ranar haifuwar Annabi Isa alaihis
salam
suka yi sabani dangane da ranar da za a yi
wannan bukin zuwa mazhabobi biyu:-
Mazhabar farko: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran
25 ga watan December, wannan ita ce mazhabar
da
Catholic, da Protestant, da kuma mafi yawan
bangarorin Kiristoci ke bi.
Mazhaba ta biyu: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran
7 ga watan January, wannan ita ce mazhabar da
bangarorin Orthodox ke bi.
Na hudu: Kiristoci kafurai ne kamar yadda
Yahudawa da Majusawa da sauran masu bautar
gumaka
suke kafurai, babu sabani cikin wannan mas’ala
cikin shari’ar Musulunci.
Na biyar: Ya kamata a san cewa akwai wasu
kafuran da Musulunci ya kebanta su da wasu
hukunce-
hukunce saboda tabbatar wa Musulmi wata
maslaha, wadannan kuwa su ne: Yahudawa, da
Kiristoci,
su wannan nau’i na kafurai Musulunci ya halatta
wa Musulmi cin yankansu, da kuma auren
matansu, sabanin mabiya addinin majusu, ko
mabiya addinin Hindu, ko mabiya addinin Budha,
ko
mabiya sauran addinai na bautan gumaka.
*************************
Idan Musulmi sun fahimci wannan sai mu shiga
bayanin mas’alarmu da muke son yi wa jama’a
bayaninta, muna rokon Allah Madaukakin Sarki
Ya taimake mu.
HUKUNCIN KARBAN KYAUTUTTUKAN KAFURAI
A RANAR IDINSU:
Su kyaututtukan da kafurai -Ahlul kitabi ko wasun
Ahlul kitabi- ke ba wa Musulmi a ranakun idinsu
na kafurci da bidi’ah sun kasu kashi biyu ne:-
Na farko: Kyaututtukan da suke ba nama ba ne
da ake bukatar yankawa, watau kamar irinsu:
halawa, da tufafi, da kayan marmari da sauransu.
Na biyu: Kyaututtukan da suke nama ne da ke
bukatar a yi masa yanka irin ta Shari’ah.
To shi na farkon, watau kyaututtukan da suke ba
nama ba ne da ke bukatar yanka irin ta Shari’ah,
babu sabani tsakanin Salafus Salih -a dai iya
saninmu- cikin halaccin karbarsu, saboda dalilai
kamar
haka:-
1- Imamul Baihaqii ya ruwaito athari na 18,644
daga Muhammad Dan Siiriin cewa:-
(( ﺃﺗﻲ ﻋﻠﻲ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻬﺪﻳﺔ ﺍﻟﻨﻴﺮﻭﺯ، ﻓﻘﺎﻝ : ﻣﺎ ﻫﺬﻩ؟
ﻗﺎﻟﻮﺍ : ﻳﺎ ﺍﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻫﺬﺍ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﻴﺮﻭﺯ . ﻗﺎﻝ :
ﻓﺎﺻﻨﻌﻮﺍ ﻛﻞ
ﻳﻮﻡ ﻓﻴﺮﻭﺯ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((An zo wa Sayyidina Aliyyu Dan Abii
Taa’lib Allah Ya kara masa yarda da kyautar
(idin)
Nairuuz, sai ya ce: mene ne wannan? Sai suka
ce: Ya Amirar Muu’miniin! Wannan ranar Nairuuz
ce.
Sai ya ce: (in haka abin yake) ku rika yin Fairuuz
a ko wace rana)). Intaha.
2- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito cikin
Musannaf athari na 24,371, da Imam Ishaq Ibnu
Raa’huyyah cikin Musnad athari na 1,606 daga
Qaa’bus Dan Zibyaan daga shi mahaifin nasa
cewa
wata mace ta tambayi Nana A’isha Allah Ya kara
mata yarda ta ce:-
(( ﺍﻥ ﻟﻨﺎ ﺍﻛﺎﺭﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺠﻮﺱ ﻭﺍﻧﻪ ﻳﻜﻮﻥ ﻟﻬﻢ ﺍﻟﻌﻴﺪ
ﻓﻴﻬﺪﻭﻥ ﻟﻨﺎ، ﻓﻘﺎﻟﺖ : ﺍﻣﺎ ﻣﺎ ﺫﺑﺢ ﻟﺬﻟﻚ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﻓﻼ ﺗﺄﻛﻠﻮﺍ
ﻭﻟﻜﻦ ﻛﻠﻮﺍ
ﻣﻦ ﺃﺷﺠﺎﺭﻫﻢ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ
Ma’ana: ((Muna da ‘yan kodago daga cikin
Majusawa, sannan kuma suna da ranar idin da
suke aika
mana da kyaututtuka. Sai ta ce: Amma abin da
aka yanka saboda wannan ranar to kada ku ci, to
amma ku ci daga ‘ya’yan itatuwansu)). Intaha.
3- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito a cikin
Musannaf athari na 24,372 daga Abuu Barzah
cewa:-
(( ﻛﺎﻥ ﻟﻪ ﺳﻜﺎﻥ ﻣﺠﻮﺱ ﻓﻜﺎﻧﻮﺍ ﻳﻬﺪﻭﻥ ﻟﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﻴﺮﻭﺯ
ﻭﺍﻟﻤﻬﺮﺟﺎﻥ ﻓﻜﺎﻥ ﻳﻘﻮﻝ ﻷﻫﻠﻪ : ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﻓﺎﻛﻬﺔ ﻓﻜﻠﻮﺍ
ﻭﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﻓﺮﺩﻭﻩ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Yana da wasu mazauna Majusawa,
kuma sun kasance suna aika masa da kyautuka a
lokacin Nairuuz da Mihrajan, sannan ya kasance
yana gaya wa iyalansa cewa: Kyautar da ta
kasance
ta kayan marmari ne to ku ci, wacce kuma ta
kasance ba hakan ba, to ku mayar da ita)).
Intaha.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi taliki a kan
wadannan hujjojin a cikin littafinsa mai suna
Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqiim 2/554-555 ya ce:-
(( ﻓﻬﺬﺍ ﻳﺪﻝ ﻋﻠﻰ ﺍﻧﻪ ﻻ ﺗﺄﺛﻴﺮ ﻟﻠﻌﻴﺪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﻨﻊ ﻣﻦ ﻗﺒﻮﻝ
ﻫﺪﻳﺘﻬﻢ، ﺑﻞ ﺣﻜﻤﻬﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻭﻏﻴﺮﻩ ﺳﻮﺍﺀ؛ ﻻﻧﻪ ﻟﻴﺲ
ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﺇﻋﺎﻧﺔ ﻟﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﺷﻌﺎﺋﺮ ﻛﻔﺮﻫﻢ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Wannan duka yana nuni ne a kan cewa:
Idi ba yi da wani tasiri a kan hana karban
kyautarsu, a’a hukuncin karban kyautarsu ba yi
da wani bambanci tsakanin lokacin Idi da kuma
lokacin da ba na Idi ba, saboda babu wani abu na
taimakon addininsu a cikin karban kyautarsu)).
Intaha.
TALIKI:
Da wannan ne za mu fahimci cewa: Maluman
Musulunci sun hana cin yankan da Majusawa
suka yi
domin bukukuwan idinsu, to amma fa ba wai sun
hana cin yankan ba ne saboda kasancewarsa
yankan da aka yi domin bukin idin kafurai ba, a’a
an hana cin yankan ne saboda kasancewarsa
yankan Majusawan da ba sa cikin mutanen nan
ne da ake kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci,
dukkan kuma kafurin da ba ya cikin abin da ake
kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci to ba a cin
yankansa.
HUKUNCIN CIN NAMAN DABBAR DA YAHUDAWA
KO KIRISTOCI SUKA YANKA DA HANNAYENSU
SABODA YIN BUKUKUWAN IDINSU:
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi bayani game
da cin abin da Yahudawa ko Kiristoci suka yanka
saboda bukukuwan idinsu, a cikin littafinsa mai
suna Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqim 2/555,558 ya
ce:-
(( ﻭﺍﻧﻤﺎ ﻳﺠﻮﺯ ﺍﻥ ﻳﺆﻛﻞ ﻣﻦ ﻃﻌﺎﻡ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻓﻲ
ﻋﻴﺪﻫﻢ ﺑﺎﺑﺘﻴﺎﻉ ﺍﻭ ﻫﺪﻳﺔ ﺍﻭ ﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﻣﻤﺎ ﻟﻢ ﻳﺬﺑﺤﻮﻩ
ﻟﻠﻌﻴﺪ . ﻓﺄﻣﺎ
ﺫﺑﺢ ﺍﻟﻤﺠﻮﺱ ﻓﺎﻟﺤﻜﻢ ﻓﻴﻬﺎ ﻣﻌﻠﻮﻡ ﻓﺈﻧﻬﺎ ﺣﺮﺍﻡ ﻋﻨﺪ
ﺍﻟﻌﺎﻣﺔ . ﻭﺃﻣﺎ ﻣﺎ ﺫﺑﺤﻪ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻻﻋﻴﺎﺩﻫﻢ ﻭﻣﺎ
ﻳﺘﻘﺮﺑﻮﻥ
ﺑﺬﺑﺤﻪ ﺍﻟﻰ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻧﻈﻴﺮ ﻣﺎ ﻳﺬﺑﺢ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻣﻦ
ﻫﺪﺍﻳﺎﻫﻢ ﻭﺿﺤﺎﻳﺎﻫﻢ ﻣﺘﻘﺮﺑﻴﻦ ﺑﻬﺎ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ، ﻭﺫﻟﻚ
ﻣﺜﻞ ﻣﺎ
ﻳﺬﺑﺤﻮﻥ ﻟﻠﻤﺴﻴﺢ ﻭﺍﻟﺰﻫﺮﺓ، ﻓﻌﻦ ﺍﺣﻤﺪ ﺭﻭﺍﻳﺘﺎﻥ :
ﺍﺷﻬﺮﻫﻤﺎ ﻓﻲ ﻧﺼﻮﺻﻪ : ﺍﻧﻪ ﻻ ﻳﺒﺎﺡ ﺍﻛﻠﻪ ﻭﺍﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﻢ
ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ
ﺗﻌﺎﻟﻰ . ﻭﻧﻘﻞ ﺍﻟﻨﻬﻲ ﻋﻦ ﺫﻟﻚ ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻭﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ
ﻋﻤﺮ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: (Cin abincin Ahlul Kitabi a lokacin idinsu
ga abin da dama ba su yanka shi saboda Idi ba,
yana halatta ne ta hanyar saye da kudi, ko kuwa
kyauta, ko wanin haka. Amma abin da Majusawa
suka yanka hukuncinsa sananne ne, watau
haramun ne a wurin dukkan malamai, to amma
abin da
Ahlul Kitabi suka yanka saboda idinsu, da kuma
abin da suke yin ibada ta hanyar yanka shi ga
wanin
Allah’ kamar abin da suke yankawa saboda
Almasihu, da Zahrah, irin dai abin da Musulmi
suke
yankawa na Hadaya, da Layya, domin neman
kusantar Allah da shi, to, Imam Ahmad yana da
fatawowi biyu game da hakan, fatawar farko
wacce ita ce ta fi shahara: Wannan ba ya halatta
a ci
shi koda kuwa ba a ambaci sunan wanin Allah a
kansa ba. An nakalto hana cin wannan yankan
ma
daga Nana A’isha, da Abdullahi Dan Umar..
Fatawa ta biyu ita ce: Cin wannan yankan
makruuhi ne
ba haramun ba. Wannan ita ce mazhabar
Malikiyyah, Imam Malik ya kyamaci cin abin da
Ahlul
Kitabi suka yanka saboda Coci-Cocinsu, ko
saboda idinsu amma ba tare da ya haramta
hakan ba)).
Intaha.
Sannan har yanzu Sahikhul Islam Ibnu Taimiyyah
ya ce a cikin Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqim
2/559 :-
(( ﻭﻧﻘﻠﺖ ﺍﻟﺮﺧﺼﺔ ﻓﻲ ﺫﺑﺎﺋﺢ ﺍﻷﻋﻴﺎﺩ ﻭﻧﺤﻮﻫﺎ ﻋﻦ ﻃﺎﺋﻔﺔ
ﻣﻦ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻢ، ﻭﻫﺬﺍ ﻓﻴﻤﺎ ﺍﺫﺍ ﻟﻢ ﻳﺴﻤﻮﺍ
ﻏﻴﺮ
ﺍﻟﻠﻪ، ﻓﺎﻥ ﺳﻤﻮﺍ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﻋﻴﺪﻫﻢ ﺍﻭ ﻏﻴﺮ ﻋﻴﺪﻫﻢ ﺣﺮﻡ
ﻓﻲ ﺍﺷﻬﺮ ﺍﻟﺮﻭﺍﻳﺘﻴﻦ، ﻭﻫﻮ ﻣﺬﻫﺐ ﺍﻟﺠﻤﻬﻮﺭ، ﻭﻫﻮ ﻣﺬﻫﺐ
ﺍﻟﻔﻘﻬﺎﺀ ﺍﻟﺜﻼﺛﺔ ﻓﻴﻤﺎ ﻧﻘﻠﻪ ﻏﻴﺮ ﻭﺍﺣﺪ، ﻭﻫﻮ ﻗﻮﻝ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ
ﺍﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ ﻭﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ، ﻭﻫﻮ ﻗﻮﻝ ﺍﻛﺜﺮ ﻓﻘﻬﺎﺀ
ﺍﻟﺸﺎﻡ ﻭﻏﻴﺮﻫﻢ . ﻭﺍﻟﺜﺎﻧﻴﺔ : ﻻ ﻳﺤﺮﻡ ﻭﺍﻥ ﺳﻤﻮﺍ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ،
ﻭﻫﺬﺍ ﻗﻮﻝ ﻋﻄﺎﺀ ﻭﻣﺠﺎﻫﺪ ﻭﻣﻜﺤﻮﻝ ﻭﺍﻻﻭﺯﺍﻋﻲ ﻭﺍﻟﻠﻴﺚ
.((
ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((An ciro yin sauki a kan cin yanke-
yanken idodin (Yahudawa da Kiristoci) da
makamantansu
(su yanke-yanken) daga wani sashi na Sahabbai
Allah Ya kara musu yarda amma fa wannan sai
idan
ba su ambaci wanin Allah a lokacin yankan ba, in
kuma har sun ambaci wanin Allah a lokacin
yankan to cin sa ya haramta a cikin fatawa mafi
shahara daga cikin fatawowi biyu da Imam
Ahmada
yake da su a cikin mas’alar, wannan kuwa shi ne
mazhabar jumhur, kuma shi ne mazhabar
Fuqaha’un nan guda uku, kamar yadda mutane da
yawa suka ruwaito, kuma shi ne maganar Aliyyu
Dan zabii Taa’lib da waninsa a cikin Sahabbai,
daga cikinsu ma akwai Abud Dardaa, da Abu
Umamah, da Irbadh Dan Saa’riyah, da Ubaa’dah
Dan Saa’mit, kuma shi ne maganar maluman
Sham
da wasunsu. Fatawar Imam Ahmad ta biyu ita
ce: Cin wannan yankan ba haramun ba ne koda
kuwa
sun ambaci sunan wanin Allah a lokacin yankan,
wannan kuwa shi ne maganar Ataa’u, da
Mujaa’hid,
da Makhuul, da Auzaa’ii, da kuma Laith)). Intaha.
Taliki na farko:-
Za mu fahimta daga maganganun malaman da
suka gabata cewa: Abin da Yahudawa da
Kiristoci
suke yankawa saboda bukukuwan idinsu yana
kasuwa ne zuwa kashi biyu:-
Na farko: Abin da suka ambaci sunan Allah yayin
yanka shi.
Na biyu: Abin da suka ambaci sunan wanin Allah
yayin yanka shi.
To ita tabbar da aka ambaci sunan Allah lokacin
yanka ta, Malamai sun kasu kashi biyu game da
hukuncin cinta.
Mazhabar farko: Sahabbai da yawa sun ba da
damar cin wannan nama. Maluman Malikiyyah,
da
Imam Ahmad cikin ruwayah sun halattar da cinsa
amma tare da nuna kyama.
Mazhaba ta biyu: Nana A’isha, da Abdullahi Dan
Umar, da kuma Maluman Hanaa’bilah sun ce cin
wannan nama haramun ne.
Sannan ita kuma dabbar da aka ambaci sunan
wanin Allah lokacin yanka ta, watau kamar
wacce aka
ambaci sunan Yesu Almasihu lokacin yanka ta,
wannan ma Malamai sun kasu kashi biyu game
da
hukuncin cin wannan dabbar:-
Mazhabar farko: Cin wannan dabba bai halatta
ba, wannan shi ne abin da Aliyyu Dan Abii
Taa’lib,
da Abud Dardaa’u, da Abuu Umamah, da Irbadh
Da Saa’riyah, da Ubaa’dah Dan Saa’mit, da
Hanafiyyah, da Malikiyyah, da Shafi’iyyah, da
Hanaa’bilah, da mafi yawan maluman kasar
Sham, suk
fada.
mazhaba ta biyu: Cin wannan dabba halal ne,
wannan shi ne abin da Ataa’u, da Mhjaa’hid, da
Makhul, da Auzaa’ii, da Laithu Dan Sa’ad, da
kuma Imam Ahmad cikin ruwaya suka fada.
Taliki na biyu:-
Za mu iya fahimta daga maganganun da suka
gabata cewa: Naman kasuwa da Musulmi ke
yankawa
da hannayensu idan Kiristoci suka saya suka
dafa a matsayin abincin Kirsimeti, to wannan
abincin
halal yake ga dukkan wanda suka ba da shi gare
shi. Wallahu A’alam.
****************************
HUKUNCIN CIN YANKAN KIRISTOCI DA
YAHUDAWA A MAZHABAR MALIKIYYAH:
A karshen wannan makala tamu za mu yi
bayanin mene ne mash’hurin mazhabar
Malikiyyah game
cin yankan Kiristoci da Yahudawa, saboda
Musulmin wannan kasa tamu Nigeria su kara
fahimtar irin
banbancin da yake tsakanin abin da ke rubuce
cikin littattafan Mazhabar Malkiyyah, da kuma
abin
da wasu jahilan ‘yan bidi’ah da suke ikirarin cewa
su masu bin Mazhabar Malikiyyah ne, alhali kuwa
hayaniyarsu kawai suke yi, son zuciyarsu ne
kawai suke bi, duk abin da jahilan shaihunansu
suka ce
to shi ne addini a wurinsu. Allah ya tsare mu da
sharrin Shaidan.
Babban malamin Malikyyah Imamul Qurtubii ya
ce cikin littafinsa Aljaami’u Li Ahkaamil Qur’an
6/53:-
(( ﻭﻗﺎﻝ ﺟﻤﻬﻮﺭ ﺍﻻﻣﺔ ﺍﻥ ﺫﺑﻴﺤﺔ ﻛﻞ ﻧﺼﺮﺍﻧﻲ ﺣﻼﻝ
ﺳﻮﺍﺀ ﻣﻦ ﺑﻨﻲ ﺗﻐﻠﺐ ﺍﻭ ﻏﻴﺮﻫﻢ، ﻭﻛﺬﻟﻚ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ )).
Ma’ana: ((Jumhuurin Al’ummah sun ce: Lalle
yankan ko wane kirista halal ne, babu banbanci
daga
kabilar Taglib ne ko daga wasunsu, haka nan su
ma Yahudawa)). Intaha.
Khalil Dan Ishaq ya ce cikin Mukhtasar Khalil
shafi na 90
(( ﻭﺍﻥ ﺳﺎﻣﺮﻳﺎ ﺍﻭ ﻣﺠﻮﺳﻴﺎ ﺗﻨﺼﺮ ﻭﺫﺑﺢ ﻟﻨﻔﺴﻪ ﻣﺴﺘﺤﻠﻪ،
ﻭﺍﻥ ﺍﻛﻞ ﺍﻟﻤﻴﺘﺔ ﺍﻥ ﻟﻢ ﻳﻐﺐ ))
Ma’an: ((koda ya kasance wani basaamire ne, ko
bamajuse ne da yazama kirista ya yanka abin da
yake halal a gare shi saboda kuma kan shi, koda
kuwa yana halatta cin mushe ne, matukar dai
musulmi na sane da cewa shi din ne ya yi
yankan)).
Sannan ya zo cikin littafin Adhalulu Madaarik
2/92:-
(( ﻳﺠﻮﺯ ﻟﻠﻤﺴﻠﻢ ﻧﻜﺎﺡ ﺣﺮﺍﺋﺮ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ .. ﻭﻛﺎﻥ
ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺑﺘﺰﻭﺟﻮﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ ﻭﺍﻟﻨﺼﺎﺭﻯ ﻛﺜﻴﺮﺍ ﺯﻣﻦ
ﺍﻟﻔﺘﺢ .. ﻭﻧﻜﺢ
ﻋﺜﻤﺎﻥ ﻧﺼﺮﺍﻧﻴﺔ، ﻭﻧﻜﺢ ﻃﻠﺤﺔ ﻳﻬﻮﺩﻳﺔ )).
Ma’ana: ((yana halatta ga musulmi auren
‘yantattun matan Ahlul Kitaabi.. Sahabbai sun
kasance da
yawa suna auren matan Yahudawa da Kiristoci a
lokacin da ake cin kasashe da yaki.. Sayyidina
Uthman ya auri wata kirista, Sayyidina Talhah ya
auri wata bayahudiya)).
***********************
Muna rokon Allah Ya nuna mana gaskiya gaskiya
ce ya ba mu ikon bin ta Ya kuma nuna mana
karya
karya ce ya ba mu ikon guje mata. Ameen.
Dr. Ibrahim Jalo Jalingo.

Advertisements

One Reply to “HUKUNCIN KARBAR KYAUTAR IDIN KIRSIMETI DA CIN ABINCIN WANNAN RANA KAMAR YADDA SALAFUS SAA’LIH SUKA YI BAYANI.”

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s