Fitowa ta 02 Bayani Dangane da Bikin Mauludi Daga Littafin Zararren Takobi akan Bidi’o’in Watannin Shekara.

  • Sheik Abdulwahab Abdallah (Imamu Ahlussunnah Wal’jama’ah)

 

Cigaba daga Inda muka tsaya a kashi na Daya,

 

Ibn khallikan yace “Masana da masu tabbatar da ilimin nasaba suna inkarin da’awarsa akan wannan nasabar”.

Imamul Baghdadi Abdulqadir bn Dahir yace:  ‘ya ‘yansa (Alqaddah) su ne suka qwace manyan madafun ikon qasar Masar (don haka suka samu damar yada wannan da’awar)

Alqali Muhammad bn Addayib Albaqillani yace:

“Su (Fadimiyyun) mutane ne da suke bayyanar da Shi’anci kuma suke boye tsantsar majusanci a cikin zukatansu”.

An tambayi Ibn Taimiyya game da su, sai yace:

“Su ne suka fi kowa fasiqanci da kafirci, kuma duk wanda ya shaide su da imani ko tsoron Allah ko ingancin nasaba, to haqiqa ya shaidesu, da abin da ba shi da ilmi akansa”.

Don haka ne Malam Almuqrizi na Alqahira, mai kare aqidun ‘yan Shi’a Fadimiyya Badiniyya yace:

“Halifofin Fadimiyya suna da bukukuwa da suke yi a tsawon shekara, kamar bikin farkon shekara, da na Ashura, da na Mauludi…da sauransu”

 

[Duba Alkhudadul muqriziyya 1/490],

 

Don haka wannan Malamin ya qara tabbatar da cewa yan Fadimiyya su suka fara qirqiro wannan bidi’ar, sune kuma suka kafa daularsu ta Fadimiyya a qasar Misra a tsakiyar qarni na hudu na hijra. Sannan daularsu ta cigaba da tafiya har izuwa tsakiyar qarni na shida bayan hijra kamar yadda littattafan tarihi suka bayyana, sannan ta cigaba da yaduwa a qasashen Musulmi, kamar qasar Mausil dake iyakar Iraq da Khurasan da kuma garin Irbil dake gabas da Mausil a kudancin Iraq.

 

Zamu cigaba InshaAllah a fitowa ta Uku

 

Bn Baaz Islamic Foundation,

05/03/1437, 16:12/2015,

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s