Fitowa ta 01 Bayani Dan Gane da Bikin Mauludi Daga Littafin Zararren Takobi akan Bidi’o’in Watannin Shekara.

  • Sheik Abdulwahab Abdallah (Imamu Ahlussunnah Wal’jama’ah)

 

Yadawa: Cibiyar Bn Baaz Islamic Foundation

 

Tambaya Ta 9: Yaushe aka fara yin bikin Mauludin Annabi (SAW) ?

 

Amsa:

Alal haqiqa zuwan Manzon Allah ( wannan duniyar babbar ni’ima ce da Allah Ya yi wa bayinsa wacce babu irinta. Kuma Rahama ce ga halitta gaba daya wacce babu kamarta.  Allah Ya samar da shi don ya zama mai gargadi da bishara ga bayinsa. Kuma ya zo ya gudanar da rayuwarsa mai cike da albarka. ya isar da saqon Allah, ya tarbbiyyantar da  al’Ummar, ya nuna musu yadda za su bi Allah, Ya yi jihadi da gwagwarmaya domin tabbatar da Addinin  Allah. bayan ya gama isar da sakon Ubangijinsa ya koma ga Allah ba tare da ya ware wata rana guda domin yin bikin zagayowar ranar haihauwarsa  ba. Haka suma Sahabbansa da manyan Halifofinsa a bayansa suka gudanar da rayuwarsu, suka koma ga Allah ba su taba ware wata rana guda ko dai a watan da aka haife shi, ko a waninsa da sunan bikin tunawa da ranar da aka haife shi ba. Haka nan ba’a sami wanda Ya yi irin wannan bikin a Tabi’ai da tabi’ut-tabi’ina wadanda su ne mafiya alkhairin qarnoni da suka sami shaida daga Manzon Allah (. Duk kuwa da tsananin qaunar da suke yiwa Manzon Allah ( da tsananin biyayyarsu gare shi. Sai bayan shudewar wadannan qarnoni masu falala da albarka  ne aka qirqiro wannan bidi’ar ta taruwa da sunan tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah ( wanda waxansu mutane da suke kiran kansu Fadimiyyun suka fara qirqirowa.  Kuma suke riya cewa su ‘ya’yan Sayyadina Aliyu ( ne, bisa da’awa ta qarya. Tunda a haqiqanin gaskiya ba su da alaqa da Sayyadina Aliyu ( ko ‘ya‘yansa. Domin su jikokin Ibn Daisan ne wanda aka fi sani da Alqaddah. Shi kuma bararren bawan Ja’afar Assadiq ne kuma daya daga cikin wadanda suka kafa mazahabar Fadimiyya Badiniyya a Iraq. (Mazahabar da suke allantar da Sayyadina Aliyu (() sanna ya tafi qasashen magrib yace wai shi jinin Aqil dan Abi Dalib ne.

Da ya ga masu wuce gona da iri daga cikin ‘yan Shi’a Rafidawa masu Limamai goma sha biyu (12) sun karbi da’awarsa sossai, sai yace shi Dan Muhammad bn Isma’il bn Ja’afar Assadiq ne. Sai suka qara ruqunqumeshi tare da cewa shi Muhammad bn Ismia’il, Malaman tarihi sun nuna bai taba haihuwa ba.

Haka dai suka yi ta yaduwa a qasashen Magrib da Misra suna yada da’awa ta qarya kuma suna jingina kansu da ahlul baitin Manzon Allah ( wanda tsakanin su da su kamar tsakanin mahudar rana da mafadarta ne. Don haka ne ma manyan Malamai daga cikin magabata kamar Alqali Ibn Khallikan da Ibnul Jauzi da Mallam Abu Shama da wasunsu suka ambaci vatancin nasabar da suke jingina kansu gareta.

 

Zamu dora a fitowa ta gaba,

 

Bn Baaz Islamic Foundation,

30/02/1437, 12/12/2015,

Bnbaazfoundation@gmail.com

@https://twitter.com/baazfoundation

Advertisements

2 Replies to “Fitowa ta 01 Bayani Dan Gane da Bikin Mauludi Daga Littafin Zararren Takobi akan Bidi’o’in Watannin Shekara.”

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s