Rabin masu mu’amala da intanet suna kan Facebook.

Mutane biliyan 1.49 ne suke amfani da Facebook a karshen watan Yuli.
Rabin mutanen da suke ta’ammali da intanet a duniya suna shiga manhajar sada zumunta ta Facebook, akalla sau daya a duk wata.
Kamfanin ya ce yawan mutanen da suke shiga shafin na sada zumunta akalla a kowane wata ya tasamma zuwa kaso 13 cikin dari.
Yawan masu amfani da Facebook din a tsawon watanni uku, daga watan Mayu zuwa karshen watan Yuli sun kai biliyan 1.49 a fadin duniya.
Saboda haka yawan mutanen ya kai rabin kiyasin mutane biliyan uku da ke mu’amala da intanet a duniya.
Kamfanin ya ce mutane a kasar Amurka suna kashe minti daya daga cikin kowane mintuna biyar da suke da shi, a kan kafar sada zumunta ta Facebook din.
Hakan yasa kamfanin yana samun kudin shiga masu matukar kauri da yawansu ya kai dala biliyan 4.4 kwatankwacin fan biliyan 2.6.
Tallace-tallace ta kafar su ne suka fi kawo kudaden shigar.
Mark Zuckerberg, mai shekaru 31 kuma dan asalin Amurka tare da abokansa guda hudu ne suka kirkiri kafar sada zumuntar ta Facebook, a shekarar 2004.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s