02 Sau nawa maza suke tunanin jima’i a rana?

Sakamakon da aka samu ba za a iya kwatanta shi kai tsaye da na (mai bincike) Fisher ba, domin mafi yawan da aka samu shi ne wanda ya yi tunanin sau bakwai a rana.
Mutanen sun samu sakamakon da ya nuna cewa kusan sau daya mutum ke yi a rana idan aka kwatanta da sakamakon Dakta Fisher wanda ya nuna sau 19 mutum ke tunanin jima’i a rana.
Gab daya dai abin da ya bayyana shi ne mutane suna tunanin jima’i amma ba kamar yadda wancan bayani na baya ya ce ba, na cewa mutum na yi sau daya a duk dakika bakwai. Abin bai kai haka ko kusa.
To sai dai kuma abin mamakin da binciken Hoffman shi ne yadda wadanda aka gudanar da binciken a kansu tunaninsu ba ya kawo musu maganar jima’i.
Abubuwan da tunaninsu ya kunsa su ne, abinci da barci da tsaftar jikinsu da ganawa da jama’a da hutu da shan gahawa( a kusan karfe 5:00 na yamma) da kallon talabijin da duba wasikar email da kuma sauran abubuwan da suka shafi harkar sadarwa ko labarai a duk tsawon rana.
A zahirin gaskiya ma tunanin jima’i ya zo musu ne kusan a karshen rana(kusan 12:00 dare) kuma ko a lokacin ma ya zo ne bayan tunanin barci.
Haka shi ma wannan bincike na Hoffman za a iya cewa ya gurbata da matsalar da na Fisher ya gamu da ita, domin mutanen da aka gudanar da binciken a kansu sun san cewa a wani lokaci a rana za a bukace su, su rubuta abin da suke tunani a cikin wayar, wannan zai sa su ga cewa sun yawaita wasu ko wani tunanin.
Idan ya kasance tunanin jima’i din suke yi, hakan zai sa su ji kunyar nuna cewa tunanin jima’i sukle yawan yi a rana, saboda haka sai su ki rubutawa da yawa.
Duk da cewa za mu iya yin watsi da labarin da ke cewa yawancin namiji babba yana tunanin jima’i sau daya a duk dakika bakawai a rana, to amma kuma fa ba za mu iya tabbatar da cewa ga ainahin yawan da yake na hakika ba.
Wannan abu ne da zai iya kasancewa ya bambanta daga mutum zuwa mutum, kuma ko da a kan mutum daya ma ya danganta da yanayin da yake ciki da lokaci. Kuma abin da zai kara rikita lissafin ma shi ne duk wani kokari na kirga tunanin mutum a kan wani abu, hakan zai iya sa ya sauya tunanin nasa.
Bayan wannan kuma akwai matsala ko muhawar cewa babu wata hanya ta kidaya tunanin mutum dalla-dalla.
Tunani ba abu ba ne mai tazara ko nisa da za a iya cewa an auna shi kamar yadda ake auna nisan gari ko tsawon wani abu na fili ko zahiri.
To in haka ne menene ya hadu ya zama tunani? Kamar girman me zai kai kafin a iya kirga shi? Ba tunanin da ka yi ko daya ko ma da yawa yayin da kake karanta wannan? Akwai tarin abubuwa da dama da za a yi tunani a kai!

Advertisements

One Reply to “02 Sau nawa maza suke tunanin jima’i a rana?”

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s