01 Sau nawa maza suke tunanin jima’i a rana?

Ko maza suna tunanin jima’i a duk dakika bakwai? Ba lalle ba. To amma maimakon ya yi mamakin ko hakan gaskiya ne, Tom Stafford ya yi tambaya ne kan yadda za a ce za a iya tabbatar da hakan ko a’a.
An gaya mana cewa maza suna yawan tunanin jima’i kusan a duk dakika bakwai kamar yadda wasu bayanai suka nuna.
Yawancinmu mun yarda da wannan magana tsawon lokacin da ya kai har ma muna shakkun gaskiyarsa.
To maimakon ka tsaya kana tunanin ko hakan gaskiya ne, kawai ka tsaya ka yi tunanin yadda za ka tabbatar da hakan ko ka karya ta.
Idan mun yarda da wannan kididdiga ta cewa maza kan yi tunanin jima’i a duk bayan dakika bakwai a rana hakan na nufin ke nan sau 514 suke yi a duk sa’a daya. Ko kuma ma a ce sau 7,200 a duk ranar da yake a farke(ba ya barci).
Hakan ya yi yawa ne ko in ce lambar ta yi girma ne? Ina ganin abin ya yi yawa ina ganin hakan ya wuce yawan duk tunanin da nake yi a rana. To amma ga wata tamabaya mai kyau: ta yaya zan iya kirga yawan tunani na ko na wani(na jima’i ko na wani abu) a rana ?
Hanyar masana kimiyya ta kirga tunani dai ta hada ne da dakatar da mutane kwatsam a daidai lokacin da suke wani abu, a kuma bukace su, su fadi tunanin da suke yi a wannan lokacin kuma a wannan wurin.
Terri Fisher da ayarinta na masu bincike daga Jami’ar Jihar Ohio ta Amurka sun gudanar da wannan binciken.
Sun bai wa wasu daliban kwaleji 283 abin da za su rika dannawa na kirge, inda suka raba daliban gida uku suka ce musu a duk lokacin da suka ji tunanin jima’i ko abinci ko barci ya zo musu to su danna wannan abu domin kirgawa.
Ta hanyar wannan bincike sun gano cewa akalla cikakken namiji yana tunanin jima’i sau 19 a rana.
Wannan ya wuce na matan da aka gudanar da binciken a kansu, inda su kuma binciken ya nuna mace tana tunanin jima’in kusan sau goma a rana.
Sai dai kuma binciken ya nuna cewa maza bayan tunanin na jima’i suna kuma tunani a kan abinci da barci, wanda hakan ke nuna cewa maza sun fi zama wadanda wasu abubuwan na rayuwa ke shigar musu rai.
Ko kuma in ba haka ba wadanda aka yi binciken a kansu sun rika kirga duk wani abu da ya zo musu rai ko da ba wani tunani ba ne na sosai, sai su dauke a matsayin tunani.
Babban dai abin sha’awa a kan binciken shi ne yawan bambance bambancen da aka samu na tunani iri-iri.
Kamar yadda wasu suka ce suna tunanin jima’i sau daya ne a rana, yayin da wasu kuma suka nuna cewa suna tunaninsa sau 388, wanda hakan ya nuna cewa kusan duk minti biyu suna tunanin jima’in.
Sai dai wata babbar matsala da wannan bincike ita ce, dabi’ar nan ta dan-adam, wadda a duk lokacin da ka fara tunanin wani abu, idan ka so ka daina tunanin daga nan zai rika ci gaba da dawo maka.
Wannan shi ne yanayin da daliban da aka gudanar da binciken Fisher suka samu kansu a ciki.
Ka duba ka gani, masu binciken sun basu abin da za su rika dannawa a duk lokacin da suka ji tunanin jima’i ko abinci ko barci ya zo musu. To ka yi tunanin sun bar wurin da suke wato sashen nazarin halayyar dan-adam na kwalejin, suna rike da wannan abin dannawa a hannu suna kokarin ka da su yi tunani a kan jima’i a ko da yaushe kuma a dai dai lokacin suna kokarin tunawa su danna wannan abu.
Anan abin da nake gani shi wancan mutumin da ya ce yana tunanin jima’i ko ya yi tunanin jima’i sau 388 yanayin da ya samu kansa a ciki ke nan.
Ko da yaushe a raina:
Wata hanyar binciken kuma ita ce wadda Wilhelm Hoffman da abokan aikinsa suka yi, inda suka bai wa wasu Jamusa manya wayoyin salula na komai-da-ruwanka, wadanda aka saita ta yadda za su rika tunatar da su sau bakwai a rana a lokuta daban daban har tsawon sati daya.
Masu binciken sun bukace su da su rubuta a cikin wayar abin da ya zo musu a tunaninsu a duk lokacin da kararrawar wayar ta kada. Dalilin sa su, su rubuta abin a wayar domin adanawa, shi ne saboda tunaninsu ya kasance ba abin da yake ciki da ya shafi adana abin da ake so su rubuta, ma’ana idan suka rubuta abin a wayar za su iya ci gaba da harkokin da suka saba ba tare da wani abu ya shiga ransu ba.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s