HUKUNCIN KARBAR KYAUTAR IDIN KIRISMETI DA CIN ABINCIN WANNAN RANA KAMAR YADDA SALAFUS SAA’LIH SUKA YI BAYANI.

1- Da yake Alhamis mai zuwa ne Kiristoci za su fara
abin da suke kira bukin kirsimeti (idin kirsimeti)
wanda suke yin shi ko dai a ranar 25/12 M ko kuwa
a ranar 7/1 M.
2- Sannan da yake a Nigeria ana zaman cakuda ne
tsakanin su Kiristoci da kuma al’ummar Musulmi.
3- Sannan da yake shi Musulunci addini ne da ya
bayyanar da hukuncin dukkan wani lamari da ya shafi
rayuwar dan Adam, ko dai ta hanyar nassi, ko ta
hanyar zahiri, ko ta hanyar ishaarah da iimaai.
4- Sannan da yake akwai masu bidi’ah da dama da ke
halatta abin da Shari’ah ba ta halatta ba, ko haramta
abin da Shari’ah ba ta haramta ba, lalle ya dace a yi
wa al’ummar Musulmi bayanin hukuncin abin da ya
shafi wannan Idi na Kirsimeti ta bangarorinsa da ke
iya shafar wasu al’ummar Musulmi.
**************************
To amma kafin mu shiga bayanin wadannan
hukunce-hukunce ya kamata Musulmi su san
abubuwa kamar haka:-
Na farko: Shi dai bukin kirsimeti wata bidi’ah ce da
bata da kiristoci suka kirkira sannan suka maida ita
wata ibada da ake samun lada ta hanyar yin ta –
kamar dai yadda wasu Musulmi suka kirkiri bidi’ar
idin mauludi- Kiristoci sun kirkiri wannan bidi’ar ce
kuwa a shekarar miladiyyah ta 360, watau a cikin
karni na hudu bayan haifuwar Annabi Isa alaihis
salam.
Na biyu: Ya kamata kowa ya san cewa ba ya halatta
Musulmi ya yi tarayya da wadanda ba musulmi ba
cikin bukukuwansu na idi, watau ta hanyar halartan
wasu tarurruka da za su kira, ko ta hanyar ba su wani
taimako domin karfafa idodin nasu, wannan dai shi
ne hanyar Salafus Salih -Sahabbai, da Taabi’ai, da
Taabi’uttaabi’in- dalili kuwa shi ne:-
Imamul Baihaqii ya ruwaito cikin As-Sunanul Kubraa
hadithi na 19,334 cewa Sayyidina Umar Dan Khattab
Allah Ya kara masa yarda ya ce:-
(( ﺍﺟﺘﻨﺒﻮﺍ ﺃﻋﺪﺍﺀ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﻋﻴﺪﻫﻢ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ku nisanci makiya Allah cikin idinsu)).
Intaha.
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Tamiyyah ya ce -kamar
yadda ya zo cikin Al-Mustadrak Alaa Fataawaa Ibnu
Tamiyyah 1/108, da Mukhtasarul Fataawaa
Misriyyah1/517 :-
(( ﻭﻟﻴﺲ ﻟﻠﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﺍﻥ ﻳﻌﻴﻨﻮﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﺃﻋﻴﺎﺩﻫﻢ ﻻ ﺑﺒﻴﻊ ﻣﺎ
ﻳﺴﺘﻌﻴﻨﻮﻥ ﺑﻪ ﻋﻠﻰ ﻋﻴﺪﻫﻢ ﻭﻻ ﺑﺎﺟﺎﺭﺓ ﺩﻭﺍﺑﻬﻢ ﻟﻴﺮﻛﺒﻮﻫﺎ ﻓﻲ
ﻋﻴﺪﻫﻢ ﻻﻥ ﺃﻋﻴﺎﺩﻫﻢ ﻣﻤﺎ ﺣﺮﻣﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻟﻤﺎ ﻓﻴﻬﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻔﺮ ﻭﺍﻟﻔﺴﻮﻕ ﻭﺍﻟﻌﺼﻴﺎﻥ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Musulmi ba su da damar su taimaka musu
cikin idodinsu, ko dai ta hanyar sayar musu da abin
da za su karfafu da shi, ko ta hanyar ba da hayar
dabbobinsu domin su hau su cikin idinsu, saboda
idodinsu na daga cikin abin da Allah Madaukakin
Sarki da kuma manzonSa mai tsira da amincin Allah
suka haramta, saboda abin da yake cikinsu na kafirci
da fasikanci da kuma sabo)). Intaha.
Na uku: Babu wani wanda ya isa ya bugi kirji a
duniyan nan ya ce: ga tabbatacciyar wata da rana da
aka haifi Annabi Isa alaihis salam a cikinta, sai dai
kowa ya fadi abin da yake zato kawai, wannan shi ya
sa ma Kiristoci masu yin bukin ranar Kirsimeti watau
ranar haifuwar Annabi Isa alaihis salam suka yi
sabani dangane da ranar da za a yi wannan bukin
zuwa mazhabobi biyu:-
Mazhabar farko: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 25
ga watan December, wannan ita ce mazhabar da
Catholic, da Protestant, da kuma mafi yawan
bangarorin Kiristoci ke bi.
Mazhaba ta biyu: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 7
ga watan January, wannan ita ce mazhabar da
bangarorin Orthodox ke bi.
Na hudu: Kiristoci kafurai ne kamar yadda Yahudawa
da Majusawa da sauran masu bautar gumaka suke
kafurai, babu sabani cikin wannan mas’ala cikin
shari’ar Musulunci.
Na biyar: Ya kamata a san cewa akwai wasu kafuran
da Musulunci ya kebanta su da wasu hukunce-
hukunce saboda tabbatar wa Musulmi wata maslaha,
wadannan kuwa su ne: Yahudawa, da Kiristoci, su
wannan nau’i na kafurai Musulunci ya halatta wa
Musulmi cin yankansu, da kuma auren matansu,
sabanin mabiya addinin majusu, ko mabiya addinin
Hindu, ko mabiya addinin Budha, ko mabiya sauran
addinai na bautan gumaka.
*************************
Idan Musulmi sun fahimci wannan sai mu shiga
bayanin mas’alarmu da muke son yi wa jama’a
bayaninta, muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya
taimake mu.
HUKUNCIN KARBAN KYAUTUTTUKAN KAFURAI A RANAR IDINSU:
Su kyaututtukan da kafurai -Ahlul kitabi ko wasun
Ahlul kitabi- ke ba wa Musulmi a ranakun idinsu na
kafurci da bidi’ah sun kasu kashi biyu ne:-
Na farko: Kyaututtukan da suke ba nama ba ne da
ake bukatar yankawa, watau kamar irinsu: halawa, da
tufafi, da kayan marmari da sauransu.
Na biyu: Kyaututtukan da suke nama ne da ke
bukatar a yi masa yanka irin ta Shari’ah.
To shi na farkon, watau kyaututtukan da suke ba
nama ba ne da ke bukatar yanka irin ta Shari’ah, babu
sabani tsakanin Salafus Salih -a dai iya saninmu-
cikin halaccin karbarsu, saboda dalilai kamar haka:-
1- Imamul Baihaqii ya ruwaito athari na 18,644 daga
Muhammad Dan Siiriin cewa:-
(( ﺃﺗﻲ ﻋﻠﻲ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻬﺪﻳﺔ ﺍﻟﻨﻴﺮﻭﺯ، ﻓﻘﺎﻝ: ﻣﺎ ﻫﺬﻩ؟ ﻗﺎﻟﻮﺍ : ﻳﺎ
ﺍﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻫﺬﺍ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﻴﺮﻭﺯ . ﻗﺎﻝ : ﻓﺎﺻﻨﻌﻮﺍ ﻛﻞ ﻳﻮﻡ
ﻓﻴﺮﻭﺯ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((An zo wa Sayyidina Aliyyu Dan Abii Taa’lib
Allah Ya kara masa yarda da kyautar (idin) Nairuuz,
sai ya ce: mene ne wannan? Sai suka ce: Ya Amirar
Muu’miniin! Wannan ranar Nairuuz ce. Sai ya ce: (in
haka abin yake) ku rika yin Fairuuz a ko wace rana)).
Intaha.
2- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito cikin
Musannaf athari na 24,371, da Imam Ishaq Ibnu
Raa’huyyah cikin Musnad athari na 1,606 daga
Qaa’bus Dan Zibyaan daga shi mahaifin nasa cewa
wata mace ta tambayi Nana A’isha Allah Ya kara mata
yarda ta ce:-
(( ﺍﻥ ﻟﻨﺎ ﺍﻛﺎﺭﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺠﻮﺱ ﻭﺍﻧﻪ ﻳﻜﻮﻥ ﻟﻬﻢ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻓﻴﻬﺪﻭﻥ ﻟﻨﺎ،
ﻓﻘﺎﻟﺖ: ﺍﻣﺎ ﻣﺎ ﺫﺑﺢ ﻟﺬﻟﻚ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﻓﻼ ﺗﺄﻛﻠﻮﺍ ﻭﻟﻜﻦ ﻛﻠﻮﺍ ﻣﻦ
ﺃﺷﺠﺎﺭﻫﻢ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ
Ma’ana: ((Muna da ‘yan kodago daga cikin Majusawa,
sannan kuma suna da ranar idin da suke aika mana
da kyaututtuka. Sai ta ce: Amma abin da aka yanka
saboda wannan ranar to kada ku ci, to amma ku ci
daga ‘ya’yan itatuwansu)). Intaha.
3- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito a cikin
Musannaf athari na 24,372 daga Abuu Barzah cewa:-
(( ﻛﺎﻥ ﻟﻪ ﺳﻜﺎﻥ ﻣﺠﻮﺱ ﻓﻜﺎﻧﻮﺍ ﻳﻬﺪﻭﻥ ﻟﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﻴﺮﻭﺯ
ﻭﺍﻟﻤﻬﺮﺟﺎﻥ ﻓﻜﺎﻥ ﻳﻘﻮﻝ ﻷﻫﻠﻪ : ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﻓﺎﻛﻬﺔ ﻓﻜﻠﻮﺍ ﻭﻣﺎ
ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﻓﺮﺩﻭﻩ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Yana da wasu mazauna Majusawa, kuma
sun kasance suna aika masa da kyautuka a lokacin
Nairuuz da Mihrajan, sannan ya kasance yana gaya
wa iyalansa cewa: Kyautar da ta kasance ta kayan
marmari ne to ku ci, wacce kuma ta kasance ba
hakan ba, to ku mayar da ita)). Intaha.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi taliki a kan
wadannan hujjojin a cikin littafinsa mai suna
Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqiim 2/554-555 ya ce:-
(( ﻓﻬﺬﺍ ﻳﺪﻝ ﻋﻠﻰ ﺍﻧﻪ ﻻ ﺗﺄﺛﻴﺮ ﻟﻠﻌﻴﺪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﻨﻊ ﻣﻦ ﻗﺒﻮﻝ
ﻫﺪﻳﺘﻬﻢ، ﺑﻞ ﺣﻜﻤﻬﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻭﻏﻴﺮﻩ ﺳﻮﺍﺀ؛ ﻻﻧﻪ ﻟﻴﺲ ﻓﻲ
ﺫﻟﻚ ﺇﻋﺎﻧﺔ ﻟﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﺷﻌﺎﺋﺮ ﻛﻔﺮﻫﻢ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Wannan duka yana nuni ne a kan cewa: Idi
ba yi da wani tasiri a kan hana karban kyautarsu, a’a
hukuncin karban kyautarsu ba yi da wani bambanci
tsakanin lokacin Idi da kuma lokacin da ba na Idi ba,
saboda babu wani abu na taimakon addininsu a cikin
karban kyautarsu)). Intaha.

TA’ALIKI:
Da wannan ne za mu fahimci cewa: Maluman
Musulunci sun hana cin yankan da Majusawa suka yi
domin bukukuwan idinsu, to amma fa ba wai sun
hana cin yankan ba ne saboda kasancewarsa yankan
da aka yi domin bukin idin kafurai ba, a’a an hana cin
yankan ne saboda kasancewarsa yankan Majusawan
da ba sa cikin mutanen nan ne da ake kira Yahudawa
ko ake kira Kiristoci, dukkan kuma kafurin da ba ya
cikin abin da ake kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci
to ba a cin yankansa.
HUKUNCIN CIN NAMAN DABBAR DA YAHUDAWA KO
KIRISTOCI SUKA YANKA DA HANNAYENSU SABODA
YIN BUKUKUWAN IDINSU:
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi bayani game da
cin abin da Yahudawa ko Kiristoci suka yanka saboda
bukukuwan idinsu, a cikin littafinsa mai suna
Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqim 2/555,558 ya ce:-
(( ﻭﺍﻧﻤﺎ ﻳﺠﻮﺯ ﺍﻥ ﻳﺆﻛﻞ ﻣﻦ ﻃﻌﺎﻡ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻓﻲ ﻋﻴﺪﻫﻢ
ﺑﺎﺑﺘﻴﺎﻉ ﺍﻭ ﻫﺪﻳﺔ ﺍﻭ ﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﻣﻤﺎ ﻟﻢ ﻳﺬﺑﺤﻮﻩ ﻟﻠﻌﻴﺪ . ﻓﺄﻣﺎ ﺫﺑﺢ
ﺍﻟﻤﺠﻮﺱ ﻓﺎﻟﺤﻜﻢ ﻓﻴﻬﺎ ﻣﻌﻠﻮﻡ ﻓﺈﻧﻬﺎ ﺣﺮﺍﻡ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻌﺎﻣﺔ . ﻭﺃﻣﺎ ﻣﺎ
ﺫﺑﺤﻪ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻻﻋﻴﺎﺩﻫﻢ ﻭﻣﺎ ﻳﺘﻘﺮﺑﻮﻥ ﺑﺬﺑﺤﻪ ﺍﻟﻰ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ
ﻧﻈﻴﺮ ﻣﺎ ﻳﺬﺑﺢ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻣﻦ ﻫﺪﺍﻳﺎﻫﻢ ﻭﺿﺤﺎﻳﺎﻫﻢ ﻣﺘﻘﺮﺑﻴﻦ
ﺑﻬﺎ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ، ﻭﺫﻟﻚ ﻣﺜﻞ ﻣﺎ ﻳﺬﺑﺤﻮﻥ ﻟﻠﻤﺴﻴﺢ ﻭﺍﻟﺰﻫﺮﺓ،
ﻓﻌﻦ ﺍﺣﻤﺪ ﺭﻭﺍﻳﺘﺎﻥ : ﺍﺷﻬﺮﻫﻤﺎ ﻓﻲ ﻧﺼﻮﺻﻪ : ﺍﻧﻪ ﻻ ﻳﺒﺎﺡ ﺍﻛﻠﻪ
ﻭﺍﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﻢ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ . ﻭﻧﻘﻞ ﺍﻟﻨﻬﻲ ﻋﻦ ﺫﻟﻚ ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ
ﻭﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: (Cin abincin Ahlul Kitabi a lokacin idinsu ga
abin da dama ba su yanka shi saboda Idi ba, yana
halatta ne ta hanyar saye da kudi, ko kuwa kyauta, ko
wanin haka. Amma abin da Majusawa suka yanka
hukuncinsa sananne ne, watau haramun ne a wurin
dukkan malamai, to amma abin da Ahlul Kitabi suka
yanka saboda idinsu, da kuma abin da suke yin ibada
ta hanyar yanka shi ga wanin Allah’ kamar abin da
suke yankawa saboda Almasihu, da Zahrah, irin dai
abin da Musulmi suke yankawa na Hadaya, da Layya,
domin neman kusantar Allah da shi, to, Imam Ahmad
yana da fatawowi biyu game da hakan, fatawar farko
wacce ita ce ta fi shahara: Wannan ba ya halatta a ci
shi koda kuwa ba a ambaci sunan wanin Allah a
kansa ba. An nakalto hana cin wannan yankan ma
daga Nana A’isha, da Abdullahi Dan Umar.. Fatawa ta
biyu ita ce: Cin wannan yankan makruuhi ne ba
haramun ba. Wannan ita ce mazhabar Malikiyyah,
Imam Malik ya kyamaci cin abin da Ahlul Kitabi suka
yanka saboda Coci-Cocinsu, ko saboda idinsu amma
ba tare da ya haramta hakan ba)). Intaha.
Sannan har yanzu Sahikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya
ce a cikin Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqim 2/559 :-
(( ﻭﻧﻘﻠﺖ ﺍﻟﺮﺧﺼﺔ ﻓﻲ ﺫﺑﺎﺋﺢ ﺍﻷﻋﻴﺎﺩ ﻭﻧﺤﻮﻫﺎ ﻋﻦ ﻃﺎﺋﻔﺔ ﻣﻦ
ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻢ، ﻭﻫﺬﺍ ﻓﻴﻤﺎ ﺍﺫﺍ ﻟﻢ ﻳﺴﻤﻮﺍ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ،
ﻓﺎﻥ ﺳﻤﻮﺍ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﻋﻴﺪﻫﻢ ﺍﻭ ﻏﻴﺮ ﻋﻴﺪﻫﻢ ﺣﺮﻡ ﻓﻲ ﺍﺷﻬﺮ
ﺍﻟﺮﻭﺍﻳﺘﻴﻦ، ﻭﻫﻮ ﻣﺬﻫﺐ ﺍﻟﺠﻤﻬﻮﺭ، ﻭﻫﻮ ﻣﺬﻫﺐ ﺍﻟﻔﻘﻬﺎﺀ ﺍﻟﺜﻼﺛﺔ
ﻓﻴﻤﺎ ﻧﻘﻠﻪ ﻏﻴﺮ ﻭﺍﺣﺪ، ﻭﻫﻮ ﻗﻮﻝ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ ﻭﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ
ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ، ﻭﻫﻮ ﻗﻮﻝ ﺍﻛﺜﺮ ﻓﻘﻬﺎﺀ ﺍﻟﺸﺎﻡ ﻭﻏﻴﺮﻫﻢ . ﻭﺍﻟﺜﺎﻧﻴﺔ : ﻻ
ﻳﺤﺮﻡ ﻭﺍﻥ ﺳﻤﻮﺍ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻫﺬﺍ ﻗﻮﻝ ﻋﻄﺎﺀ ﻭﻣﺠﺎﻫﺪ
ﻭﻣﻜﺤﻮﻝ ﻭﺍﻻﻭﺯﺍﻋﻲ ﻭﺍﻟﻠﻴﺚ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((An ciro yin sauki a kan cin yanke-yanken
idodin (Yahudawa da Kiristoci) da makamantansu (su
yanke-yanken) daga wani sashi na Sahabbai Allah Ya
kara musu yarda amma fa wannan sai idan ba su
ambaci wanin Allah a lokacin yankan ba, in kuma har
sun ambaci wanin Allah a lokacin yankan to cin sa
ya haramta a cikin fatawa mafi shahara daga cikin
fatawowi biyu da Imam Ahmada yake da su a cikin
mas’alar, wannan kuwa shi ne mazhabar jumhur,
kuma shi ne mazhabar Fuqaha’un nan guda uku,
kamar yadda mutane da yawa suka ruwaito, kuma shi
ne maganar Aliyyu Dan zabii Taa’lib da waninsa a
cikin Sahabbai, daga cikinsu ma akwai Abud Dardaa,
da Abu Umamah, da Irbadh Dan Saa’riyah, da
Ubaa’dah Dan Saa’mit, kuma shi ne maganar
maluman Sham da wasunsu. Fatawar Imam Ahmad ta
biyu ita ce: Cin wannan yankan ba haramun ba ne
koda kuwa sun ambaci sunan wanin Allah a lokacin
yankan, wannan kuwa shi ne maganar Ataa’u, da
Mujaa’hid, da Makhuul, da Auzaa’ii, da kuma Laith)).
Intaha.
Taliki na farko:-
Za mu fahimta daga maganganun malaman da suka
gabata cewa: Abin da Yahudawa da Kiristoci suke
yankawa saboda bukukuwan idinsu yana kasuwa ne
zuwa kashi biyu:-
Na farko: Abin da suka ambaci sunan Allah yayin
yanka shi.
Na biyu: Abin da suka ambaci sunan wanin Allah
yayin yanka shi.
To ita tabbar da aka ambaci sunan Allah lokacin
yanka ta, Malamai sun kasu kashi biyu game da
hukuncin cinta.
Mazhabar farko: Sahabbai da yawa sun ba da damar
cin wannan nama. Maluman Malikiyyah, da Imam
Ahmad cikin ruwayah sun halattar da cinsa amma
tare da nuna kyama.
Mazhaba ta biyu: Nana A’isha, da Abdullahi Dan
Umar, da kuma Maluman Hanaa’bilah sun ce cin
wannan nama haramun ne.
Sannan ita kuma dabbar da aka ambaci sunan wanin
Allah lokacin yanka ta, watau kamar wacce aka
ambaci sunan Yesu Almasihu lokacin yanka ta,
wannan ma Malamai sun kasu kashi biyu game da
hukuncin cin wannan dabbar:-
Mazhabar farko: Cin wannan dabba bai halatta ba,
wannan shi ne abin da Aliyyu Dan Abii Taa’lib, da
Abud Dardaa’u, da Abuu Umamah, da Irbadh Da
Saa’riyah, da Ubaa’dah Dan Saa’mit, da Hanafiyyah,
da Malikiyyah, da Shafi’iyyah, da Hanaa’bilah, da mafi
yawan maluman kasar Sham, suk fada.
mazhaba ta biyu: Cin wannan dabba halal ne, wannan
shi ne abin da Ataa’u, da Mhjaa’hid, da Makhul, da
Auzaa’ii, da Laithu Dan Sa’ad, da kuma Imam Ahmad
cikin ruwaya suka fada.
Taliki na biyu:-
Za mu iya fahimta daga maganganun da suka gabata
cewa: Naman kasuwa da Musulmi ke yankawa da
hannayensu idan Kiristoci suka saya suka dafa a
matsayin abincin Kirsimeti, to wannan abincin halal
yake ga dukkan wanda suka ba da shi gare shi.
Wallahu A’alam.
****************************
HUKUNCIN CIN YANKAN KIRISTOCI DA YAHUDAWA A MAZHABAR MALIKIYYAH:
A karshen wannan makala tamu za mu yi bayanin
mene ne mash’hurin mazhabar Malikiyyah game cin
yankan Kiristoci da Yahudawa, saboda Musulmin
wannan kasa tamu Nigeria su kara fahimtar irin
banbancin da yake tsakanin abin da ke rubuce cikin
littattafan Mazhabar Malkiyyah, da kuma abin da
wasu jahilan ‘yan bidi’ah da suke ikirarin cewa su
masu bin Mazhabar Malikiyyah ne, alhali kuwa
hayaniyarsu kawai suke yi, son zuciyarsu ne kawai
suke bi, duk abin da jahilan shaihunansu suka ce to
shi ne addini a wurinsu. Allah ya tsare mu da sharrin
Shaidan.
Babban malamin Malikyyah Imamul Qurtubii ya ce
cikin littafinsa Aljaami’u Li Ahkaamil Qur’an 6/53:-
(( ﻭﻗﺎﻝ ﺟﻤﻬﻮﺭ ﺍﻻﻣﺔ ﺍﻥ ﺫﺑﻴﺤﺔ ﻛﻞ ﻧﺼﺮﺍﻧﻲ ﺣﻼﻝ ﺳﻮﺍﺀ ﻣﻦ
ﺑﻨﻲ ﺗﻐﻠﺐ ﺍﻭ ﻏﻴﺮﻫﻢ، ﻭﻛﺬﻟﻚ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ )).
Ma’ana: ((Jumhuurin Al’ummah sun ce: Lalle yankan
ko wane kirista halal ne, babu banbanci daga kabilar
Taglib ne ko daga wasunsu, haka nan su ma
Yahudawa)). Intaha.
Khalil Dan Ishaq ya ce cikin Mukhtasar Khalil shafi
na 90
(( ﻭﺍﻥ ﺳﺎﻣﺮﻳﺎ ﺍﻭ ﻣﺠﻮﺳﻴﺎ ﺗﻨﺼﺮ ﻭﺫﺑﺢ ﻟﻨﻔﺴﻪ ﻣﺴﺘﺤﻠﻪ، ﻭﺍﻥ
ﺍﻛﻞ ﺍﻟﻤﻴﺘﺔ ﺍﻥ ﻟﻢ ﻳﻐﺐ ))
Ma’an: ((koda ya kasance wani basaamire ne, ko
bamajuse ne da yazama kirista ya yanka abin da yake
halal a gare shi saboda kuma kan shi, koda kuwa
yana halatta cin mushe ne, matukar dai musulmi na
sane da cewa shi din ne ya yi yankan)).
Sannan ya zo cikin littafin Adhalulu Madaarik 2/92:-
(( ﻳﺠﻮﺯ ﻟﻠﻤﺴﻠﻢ ﻧﻜﺎﺡ ﺣﺮﺍﺋﺮ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ .. ﻭﻛﺎﻥ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ
ﺑﺘﺰﻭﺟﻮﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ ﻭﺍﻟﻨﺼﺎﺭﻯ ﻛﺜﻴﺮﺍ ﺯﻣﻦ ﺍﻟﻔﺘﺢ .. ﻭﻧﻜﺢ
ﻋﺜﻤﺎﻥ ﻧﺼﺮﺍﻧﻴﺔ، ﻭﻧﻜﺢ ﻃﻠﺤﺔ ﻳﻬﻮﺩﻳﺔ )).
Ma’ana: ((yana halatta ga musulmi auren ‘yantattun
matan Ahlul Kitaabi.. Sahabbai sun kasance da yawa
suna auren matan Yahudawa da Kiristoci a lokacin da
ake cin kasashe da yaki.. Sayyidina Uthman ya auri
wata kirista, Sayyidina Talhah ya auri wata
bayahudiya)).
***********************
Muna rokon Allah Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce
ya ba mu ikon bin ta Ya kuma nuna mana karya
karya ce ya ba mu ikon guje mata.
Ameeeeen.
Via: http://t.co/2wFeKmjyQW

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s