DORA DAMA AKAN HAGU CIKIN SALLAH SHI NE SUNNAH, SAKIN HANNAYE CIKIN SALLA SABANIN SUNNAH NE

Imamush Shaukaanii ya ce cikin littafinsa Nailul
Autaar 2/205: ((Hadithan dora dama a kan hagu
ishrin ne suka zo daga Annabi mai tsira da amincin
Allah ta hanyar mutum goma sha takwas, tsakanin
Sahabi da Tabi’i)).
Ga wasu daga cikin hadithan da Imamush Shaukaanii
ya yi maganarsu:-
1- Imamu Muslim ya ruwaito hadthi na 401 cewa:
Annabi mai tsira da amincin Allah: ((Ya kasance yana
dora hannun damansa a kan hagunsa)).
2- Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi na 740 da
Imam Malik cikin Muwattaa hadithi na 546 cewa
Manzon Allah mai tsira da amincin Allah yana
umurtan sahabbansa da dora dama a kan hagu:
((Mutane sun kasance ana umurtan su da cewa:
mutum ya dora damansa a kan zira’insa na hagu a
cikin Salla)).
3- Imamut Tabaraanii ya ruwaito cikin Almu’ujamul
Kabiir hadithi na 11,323, da Imamud Daara Qudnii
cikin Babun Fi Akhzish Shimaal Bil Yamiin hadithi na
3, da Imam Ibnu Hibbaan dadithi na 1,770, da Imam
Sulaimaan Ibnu Dawud Attayaalisii cikin Musnad
hadithi na 2,776 cewa Annabi mai tsira da amincin
Allah ya kasance yana cewa: ((Mu taron Annabawa
an umurce mu da gauggauta buda-baki, da jinkirta
sahur, da kuma mu dora hannayenmu na dama a kan
hannayenmu na hagu)). Albaanii ya inganta hadithin
cikin Sahihul Jami’is Sagiir 1/454.
4- Imam Ahmad ya ruwaito hadithi na 15,090, da
Imam Abu Dawud Hadiyhi na 755, da isnadi sahihi
cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ((Ya
wuce wani mutum yana salla amma ya dora
hannunsa na hagu a kan na dama, sai ya balle
hannun ya dora daman a kan hagun)).
5- Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 727, da
Imam Nasa’ii hadithi na 963, da Imam Ibnu
Khuzaimah hadithi na 480 da isnadi sahihi cewa
Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ((Ya kasance
yana dora dama a kan bayan tafinsa na hagu, da
kuma wuyan hannu, da dantse)).
6- Imama Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 759, da
Imam Ibnu Khuzaimah hadithi na 479 cewa Annabi
mai tsira da amincin Allah ((Ya kasance yana sanya
hannun damansa a kan hagunsa, sannan sai ya hada
tsakaninsu a kan kirjinsa alhalin yana cikin salla)).
TAMBAYOYI TARE DA AMSOSHINSU:
(1) Idan wani ya ce: Amma kuma ai Imamut Tabarii
ya ruwaito cikin littafinsa Almuujamul Kabiir hadithi
na 16,563, daga Sahabi Mu’azu Dan Jabal ya ce:-
(( ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﺻﻼﺗﻪ ﺭﻓﻊ
ﻳﺪﻳﻪ ﻗﺒﺎﻟﺔ ﺃﺫﻧﻴﻪ، ﻓﺈﺫﺍ ﻛﺒﺮ ﺍﺭﺳﻠﻬﻤﺎ، ﺛﻢ ﺳﻜﺖ، ﻭﺭﺑﻤﺎ ﻳﻀﻊ
ﻳﻤﻴﻨﻪ ﻋﻠﻰ ﻳﺴﺎﺭﻩ )).
Ma’ana: ((Annabi mai tsira da amincin Allah ya
kasance idan yana cikin sallarsa sai ya daga hannu
daura da kunnensa, idan ya yi kabbara sai ya sake
su, sai kuma ya yi shiru, wani lokaci ma nakan gan
shi yana dora damansa a kan hagunsa)). Wannan
hadithi ai shi ne hujjar sake hannu!!
Sai a ce da shi: Da farko dai ya kamata ka san cewa
wannan hadithi maudhuu’i ne, watau hadithi ne da
cikin isnadinsa akwai makaryaci kazzaabi wannan
kuwa shi ne: Khasiib Bin Jahdar, ya zo cikin littafin
Miizaanu Litidaal 1/653 kamar haka:-
(( ﺍﻟﺨﺼﻴﺐ ﺑﻦ ﺟﺤﺪﺭ: ﻋﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺩﻳﻨﺎﺭ، ﻭﺃﺑﻲ ﺻﺎﻟﺢ
ﺍﻟﺴﻤﺎﻥ، ﻛﺬﺑﻪ ﺷﻌﺒﺔ ﻭﺍﻟﻘﻄﺎﻥ ﻭﺍﺑﻦ ﻣﻌﻴﻦ. ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺣﻤﺪ : ﻻ
ﻳﻜﺘﺐ ﺣﺪﻳﺜﻪ . ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ: ﻛﺬﺍﺏ ﺍﺳﺘﻌﺪﻯ ﻋﻠﻴﻪ ﺷﻌﺒﺔ )).
Ma’ana: ((Khasiib Bin Jahdar: daga Amr Bin Diinaar,
da Abu Salihis Sammaan: Shu’ubah, da Qattaan, da
Ibnu Ma’iin sun karyata shi. Ahmad ya ce: Ba a
rubuta hadithinsa. Bukharii ya ce: Makaryaci ne,
Shu’ubah ya yi bayanin karyarsa))
Na biyu: Da za a kaddara cewa hadithin ingantacce
ne, to da sai a fassara shi da cewa: yana nufin bayan
Annabi ya daga hannayensa daura da kunnuwansa
lokacin kabbarar harama, ya kan sake hannayen nasa
ne zuwa kirjinsa, dole a yi irin wannan fassarar
saboda hadithin ya dace da sauran hadithai
ingantattu cikin babin.
Babban masanin ilmin hadithi Alhaafiz Ibnu Hajar ya
ce cikin littafinsa: Attalkhiisul Habiir 1/554:-
(( ﺗﻨﺒﻴﻪ : ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻐﺰﺍﻟﻲ : ﺳﻤﻌﺖ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻤﺤﺪﺛﻴﻦ ﻳﻘﻮﻝ : ﻫﺬﺍ
ﺍﻟﺨﺒﺮ ﺍﻧﻤﺎ ﻭﺭﺩ ﺑﺎﻧﻪ ﻳﺮﺳﻞ ﻳﺪﻳﻪ ﺍﻟﻰ ﺻﺪﺭﻩ، ﻻ ﺍﻧﻪ ﻳﺮﺳﻠﻬﻤﺎ ﺛﻢ
ﻳﺴﺘﺄﻧﻒ ﺭﻓﻌﻬﻤﺎ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺼﺪﺭ . ﺣﻜﺎﻩ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﺼﻼﺡ ﻓﻲ ﻣﺸﻜﻞ
ﺍﻟﻮﺳﻴﻂ)).
Ma’ana: ((Fadakarwa: Gazaalii ya ce: Na ji sashin
malaman hadithi na cewa: Wannan hadithi ya zo ne a
kan cewa yana sake hannayensa ne zuwa girjinsa, ba
wai yana sake su ba ne, sannan daga baya ya daga
su zuwa girji ba. Ibnus Salaah ya hikaito shi cikin
“Mushkilul Wasiit”)).
(2) Idan wani kuma ya ce: To ai an samu daga cikin
magabata wadanda suka yi salla hannayensu a sake,
don mene ne za a ce da mu yanzu: ba za mu yi salla
hannayenmu a sake ba?
To sai a ce da shi: Na farko dai ya kamata ka san
cewa ya kai dan’uwa! Annabi Muhammad mai tsira da
amincin Allah shi ne kadai wanda Allah Ya aiko shi
zuwa gare ka, bai aiko waninsa zuwa gare ka ba a
matsayin manzo, saboda haka ba daidai ba ne ka bar
umurninsa shi Annabi Muhammad ko kuma ka bar
aikinsa, sannan ka je kana riko da umurni ko da aikin
wani koma wane ne shi a wannan duniya!
Abu na biyu: A lokacin da Sahabi Abdullahi Dan
Abbas ya yi yunkurin tabbatar da sunnar tamattu’i
cikin Hajji, an samu wasu mutane da suka ce da shi:
Ai Abubakar da Umar sun hana Mut’ar Hajji, shi kuwa
sai ya amsa ya ce da su: ((Wani dutse ya yi kusan
sauko muku daga sama! Ina ce muku: Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah ya ce, sannan kuna ce da
ni: Abubakar da Umar sun ce!)).
Wannan magana ta Abdullahi Dan Abbas asalinta na
cikin Musnadu Ahmad hadithi na 3,121, da
Almuujamul Ausat na Tabaraanii hadithi na 21, da
Jami’u bayanil ilmi na Ibnu Abdil Bar hadithi na
2,377, da Alfaqih wal Mutafaqqih na Khatiibul
Bagdaadii hadithi na 380.
Abu na uku shi ne: Barin aiki da maganar Annabi ko
aikinsa zuwa yin aiki da maganar wani ko aikinsa
saba wa Ijma’in Al’ummah ne, shi kuwa yin hakan
haramun ne a bisa ittifakin dukkan malaman Duniya,
idan Annabi ya yi umurni da a yi Kablu a cikin salla
sannan ka ji wani kuma yana cewa a yi sadlu domin
ai sadlu ba ya bata salla to lalle wannan mutum ya yi
haramun ya zama mai sabon Allah a bisa ijma’in
Maluman Musulunci!
Ya zo cikin littafin Iiqazul Himam shafi na 68 cewa
Imamush Shafi’ii ya ce: ((Musulmi sun yi Ijma’i a kan
cewa duk wanda sunnar Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah ta bayyana gare shi, to, ba ya halatta
gare shi ya bar ta saboda yin riko da maganar wani)).
(3) Idan wani ya ce: To ai sake hannaye cikin salla
shi ne mazhabar Imam Malik, tunda mu kuwa
Malikiyyah ne ke nan dukkan abin da Imam Malik ya
yi na Addini shi ne mu ma za mu yi!!
To sai a ce da shi: Na farko dai ya kamata ka san
cewa Allah Madaukakin Sarki bai aiko maka Imam
Malik a matsayin manzo ba, a’a Ya aiko maka Annabi
Muhammad ne a matsayin manzo zuwa gare ka kai
da sauran mutanen Duniya baki daya, shi kuwa
Annabi Muhammad babu inda ya ce da kai ka yi salla
hannayenka a sake, a’a abin da ya ce da kai shi ne:
Ka dora damanka a kan hagunka cikin sallanka. Ta
kaka za ka bar nasa ka riki na wani komin girmansa
kuwa a idanunka?
A bu na biyu: cewa da ka yi: mazhabar Imam Malik
ita ce: yin salla hannaye a sake, magana ce mara
dikka, saboda shi Imam Malik yana da fatawowi
daidai har guda hudu ne cikin wannan mas’alar, ba
wai fatawa daya kawai ba.
Babban Malami cikin mazhabar malikiyyah Imamul
Baajii ya ce cikin littafinsa Almuntaqaa 1/281: Imam
Malik yana da fatawowi hudu da aka ruwaito daga
gare shi cikin wannan mas’alar: Fatawar farko:
Ash’hab ya ruwaito daga gare shi cewa: Babu laifi a
dora dama a kan hagu cikin sallar nafila da farilla.
Fatawa ta biyu: Mutarrif da Ibnul Maajishuun da kuma
almajiransa na Iraq sun ruwaito daga gare shi cewa:
Dora dama a kan hagu cikin salla mustahabbi ne.
Fatawa ta uku: Mutanen Iraq sun ruwaito daga
Malikawa daga shi Imam Malik cewa: Kada a dora
dama a kan hagu cikin salla. Fatawa ta hudu: Ibnul
Qaasim ya ruwaito daga gare shi cewa: makruuhi ne
a dora dama a kan hagu cikin sallar farilla, amma
babu laifi a yi hakan cikin sallar nafila.
A nan ai kun ga ya kamata a ce imma Malikiyyar za a
yi, to sai a yi wacce ta dace da sunnar Annabi mai
tsira da amincin Allah, ba wai wacce ta saba wa
sunnar Muhammadur Rasuulul Lahi ba, Allah ya
taimake kan yin aiki da sahihiyar Sunnar ManzonSa.
(4) Idan wani ya ce: To mene ne fahimtar
Malamanmu na Da’awah da Aqidah kuma cikin
wannan mas’alar?
Sai a ce da shi: Fahimtar mutanen da muka sani daga
cikinsu ita ce: Yin salla hannaye a sake abu ne da
yake sabanin Sunnah. Misali: Sheik Abdulaziz Bin
Baz ya ce cikin littafinsa na fatawa 11/144:-
(( ﺍﻟﺜﺎﺑﺖ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﻧﻪ ﻳﻘﺒﺾ ﻳﺪﻳﻪ
ﺣﺎﻝ ﻗﻴﺎﻣﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﻼﺓ …ﺍﻣﺎ ﺇﺭﺳﺎﻝ ﺍﻟﻴﺪﻳﻦ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﻼﺓ
ﻓﻤﻜﺮﻭﻩ ﻻ ﻳﻨﺒﻐﻲ ﻓﻌﻠﻪ ﻟﻜﻮﻧﻪ ﺧﻼﻑ ﺍﻟﺴﻨﺔ )).
Ma’ana: ((Abin da ya tabbata daga Annabi mai tsira
da amincin Allah shi ne cewa: Yana kame
hannayensa ne lokacin da yake tsaye cikin
salla ..Amma sake hannaye a cikin salla makruhi ne,
yin sa bai kamata ba, saboda kasancewarsa sabanin
Sunnah)).
Sannan ya sake cewa cikin wannan littafin nasa
11/145:-
(( ﻭﺑﻤﺎ ﺫﻛﺮﻧﺎﻩ ﺗﻌﻠﻤﻮﻥ ﺍﻥ ﺇﺭﺳﺎﻝ ﺍﻟﻴﺪﻳﻦ ﻻ ﻳﻘﺪﺡ ﻓﻲ ﺍﺳﻼﻡ
ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ، ﻭﻻ ﻓﻲ ﺍﻛﻞ ﺫﺑﻴﺤﺘﻪ ﻟﻜﻨﻪ ﻣﻜﺮﻭﻩ ﻭﻣﺨﺎﻟﻒ ﻟﻠﺴﻨﺔ ﻻ
ﻳﻨﺒﻐﻲ ﻓﻌﻠﻪ )).
Ma’ana: ((Saboda abin da muka ambata din nan ne za
ku san cewa: Sake hannaye ba ya soke Musuluncin
Musulmi, haka nan cin yankansa, sai dai kuma shi
makruhi ne, kuma abu ne da ya saba wa Sunnah, ba
ya kamata a yi shi)).
Sannan ya sake cewa cikin wannan littafi nasa
29/239:-
(( ﻫﺬﺍ ﻣﻜﺮﻭﻩ، ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﺿﻤﻬﻤﺎ ﻭﺟﻌﻠﻬﻤﺎ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﺪﺭ، ﻭﺟﻌﻞ
ﺍﻟﻴﻤﻨﻰ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻴﺴﺮﻯ ﻭﺍﻟﺮﺳﻎ ﻭﺍﻟﺴﺎﻋﺪ؛ ﻻﻧﻪ ﻗﺪ ﺛﺒﺖ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﺣﺪﻳﺚ ﺳﻬﻞ ﺑﻦ ﺳﻌﺪ، ﻭﻭﺍﺋﻞ ﺑﻦ
ﺣﺠﺮ، ﻭﻫﻠﺐ ﺍﻟﻄﺎﺋﻲ ﻣﺎ ﻳﺪﻝ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ . ﺍﻣﺎ ﺍﻹﺭﺳﺎﻝ ﻓﻼ ﺩﻟﻴﻞ
ﻋﻠﻴﻪ، ﺑﻞ ﻫﻮ ﺧﻼﻑ ﺍﻟﺴﻨﺔ )).
Ma’ana: ((Wannan makruhi ne, abin da yake Sunnah:
Taro su da sanya su a kan kirji, da kuma sanya dama
a kan tafin hagu da wuyan hannu, da dantse, saboda
ya tabbata daga Annabi mai tsira da amincin Allah
daga hadithin Sahl Dan Sa’ad, da Waa’il Dan Hujur, da
Hulb Attaa’ii abin da yake nuna hakan. Amma sake
hannaye babu wani dalil a kansa, kai a gaskiya ma
shi sabanin Sunnah ne)).
(5) Idan wani ya ce: Ko a cikin shugabannin
Mazhabar Imam Malik akwai wadanda ke ganin cewa
da zarar an samu wata fatawa a cikin Mazhabar
malikiyyah wacce ta saba wa sahihiyar sunnar
Manzon Allah, to, a yi watsi da ita, a koma a yi riko
da sahihiyar sunnar Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah kawai?
Amsa a nan ita ce: Lalle akwai su da yawa, a gaskiya
ma ni babu wani shahararre daga cikinsu da na sani
yake cewa: Bayan Bamalike ya fahimci cewa
sahihiyar Sunnah ta saba wa malikancinsa ya yi
watsi da sahihiyar Sunnar ya cigaba da yin aiki da
abin da ya zo cikin mazhabarsa kawai!! Ni ban san
wani mash’huri da ya fidi irin wannan magana mara
kan gado ba. Gaskiyan lamari shi ne: Abin da
shugabannin mazhaba suke cewa shi ne: Duk lokacin
da wani kaulin mazhaba ya yi karo da sahihiyar
Sunnah to sai a jingine mazhabar a yi aiki da
sahihiyar Sunnah. Imam Malik da kansa yana cewa
kamar yadda ya zo cikin littafin Tartiibul Madaarik
1/182:-
(( ﺍﻧﻤﺎ ﺍﻧﺎ ﺑﺸﺮ ﺃﺧﻄﺊ ﻭﺃﺻﻴﺐ، ﻓﺎﻧﻈﺮﻭﺍ ﻓﻲ ﺭﺃﻳﻲ ﻓﻜﻞ ﻣﺎ
ﻭﺍﻓﻖ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺨﺬﻭﻩ، ﻭﻛﻞ ﻣﺎ ﻟﻢ ﻳﻮﺍﻓﻖ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ
ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺎﺗﺮﻛﻮﻩ )).
Ma’ana: ((Ni ba kowa ba ne face mutum, ina yin kure
kuma ina yin daidai, sai ku rika yin nazari cikin
ijtihadina, dukkan abin da ya dace da Alkur’ani da
Sunnah sai ku rike shi, kuma dukkan abin da bai dace
da Alkur’ani da Sunnah ba sai ku bar shi)).
Sannan babban malami Jamaalud Dinil Qaasimii ya
ce cikin littafinsa: Attahdiithu Fi Fununi Mustalahil
Hadith shafi na 245, da babban malami Saalih Bin
Muhammad Alfullaanii cikin littafinsa: Iiqaazu Himami
Ulil Absar shafi na 89: dukkansu biyun sun ce:
Babban malami cikin mazhabar Malikiyyah
Muhammad Almaqqarii ya ce cikin littafinsa na
Qwa’idul Fiqhi:-
(( ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺍﺗﺒﺎﻉ ﻇﺎﻫﺮ ﻧﺺ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﻣﻊ ﻣﺨﺎﻟﻔﺘﻪ ﻷﺻﻮﻝ
ﺍﻟﺸﺮﻳﻌﺔ ﻋﻨﺪ ﺣﺬﺍﻕ ﺍﻟﺸﻴﻮﺥ. ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺒﺎﺟﻲ: ﻻ ﺍﻋﻠﻢ ﻗﻮﻻ ﺍﺷﺪ
ﺧﻼﻓﺎ ﻋﻠﻰ ﻣﺎﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﻫﻞ ﺍﻻﻧﺪﻟﺲ؛ ﻻﻥ ﻣﺎﻟﻜﺎ ﻻ ﻳﺠﻴﺰ ﺗﻘﻠﻴﺪ
ﺍﻟﺮﻭﺍﺓ ﻋﻨﻪ ﻋﻨﺪ ﻣﺨﺎﻟﻔﺘﻬﻢ ﺍﻷﺻﻮﻝ ﻭﻫﻢ ﻻ ﻳﻌﺘﻤﺪﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ .
ﺍﻧﺘﻬﻰ. ﻭﻗﺎﻝ ﺃﻳﻀﺎً : ﻗﺎﻋﺪﺓ: ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺭﺩ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻤﺬﻫﺐ
ﻋﻠﻰ ﻭﺟﻪ ﻳﻨﻘﺺ ﻣﻦ ﺑﻬﺠﺘﻬﺎ ﻭﻳﺬﻫﺐ ﺑﺎﻟﺜﻘﺔ ﺑﻈﺎﻫﺮﻫﺎ؛ ﻓﺎﻥ
ﺫﻟﻚ ﻓﺴﺎﺩ ﻟﻬﺎ ﻭﺣﻂ ﻣﻦ ﻣﻨﺰﻟﺘﻨﺎ، ﻻ ﺍﺻﻠﺢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻤﺬﻫﺐ
ﻟﻔﺴﺎﺩﻫﺎ، ﻭﻻ ﺭﻓﻌﻬﺎ ﺑﺨﻔﺾ ﺩﺭﺟﺎﺗﻬﺎ، ﻓﻜﻞ ﻛﻼﻡ ﻳﺆﺧﺬ ﻣﻨﻪ
ﻭﻳﺮﺩ ﺍﻻ ﻣﺎ ﺻﺢ ﻟﻨﺎ ﻋﻦ ﻣﺤﻤﺪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ، ﺑﻞ ﻻ
ﻳﺠﻮﺯ ﺍﻟﺮﺩ ﻣﻄﻠﻘﺎ؛ ﻻﻥ ﺍﻟﻮﺍﺟﺐ ﺍﻥ ﺗﺮﺩ ﺍﻟﻤﺬﺍﻫﺐ ﺍﻟﻴﻬﺎ )).
Ma’ana: ((Bai halatta bin zahirin nassin Imami tare da
sabawarsa ga jigogin Shari’ah (Qur’ani da Hadithi) a
wurin korarrun Shaihunai. (Imam) Baajii ya ce: Ban
san wani kauli da ya fi tsananin saba wa Malik ba
kamar (kaulin) mutanen Andulus ba, saboda Malik ba
ya halattar da bin masu ruwaya daga gare shi ba a
lokacin da suka saba wa Jigogi, su ba sa dogara a
kan haka. Intaha. Sannan (Imam Baajii) ya sake
cewa: Qaa’idah: Bai halatta a yi raddin Hadithai zuwa
ga mazhaba ta fiskar da zai rage wani abu na
armashinsu, kuma ya tafiyar da amincewa da
zahirinsu, domin hakan bata su ne da kuma
wulakanta matsayinsu. Kada Allah Ya kyautata
mazhabobi ta hanyar bacinsu (watau su hadithan)
kada (Allah Ya daukaka mazhabobin) ta hanyar karya
darajarsu (su hadithan). Dukkan wata magana Ana
iya aiki da ita, ana kuma iya yin watsi da ita, amma
banda abin da ya inganta a wurinmu daga
Muhammad mai tsira da amincin Allah, ko kadan bai
halatta a yi raddin (maganarsa), domin abin da ke
wajibi shi ne: Yin raddin mazhabobi zuwa gare ta))
(watau maganar Annabi mai tsira da amincin Allah).
(6) Idan wani ya ce: Dalilan nan duka da ka kawo na
cewa: dora dama a kan hagu cikin salla shi ne
Sunnah, sake hannaye kuwa sabanin Sunnah ne,
wasu mutane za su ce ba su gamsu da su ba, hasali
ma za su ce dukkan hadithan masu rauni ne, saboda
haka yin salla hannaye a sake shi ne daidai domin
shi ne abin da suka sani a mazhabar Malikiyya!!!
To, sai a ce da shi: Na farko dai da ma ba dukkan
gaskiyar da masu wa’azi ke fada ba ne mutane ke
karba, Annabawa da Manzanni sun gaya wa
jama’arsu gaskiya, amma an samu mutane da yawa
wadanda suka karyata su, suka yi watsi da gaskiyar
da suka fada musu. Wannan shi ya sa za ka ga ‘yan
bidi’ah da yawa suna karyata ingantattun hadithan
Buhari da Muslim suka ruwaito cikin sahihansu,
matukar dai hadithan sun saba wa abin da Dagutansu
suka dora su a kan shi iyazan billah!
A bu na biyu shi ne: Ciwon son zuciya na da wahalar
waraka, wannan shi ya sa duk yadda masu wa’azi
suka yi kokarin fahimtar da Kiristoci cewa aqidarsu ta
cewa Allah yana da Da watau Isa, kuma shi Allah
Dayan uku ne! watau: shi ne Allah Uba, sannan kuma
akwai Allah Da! Sannan kuma akwai Allah Ruhu Mai
tsarki! Duk lokacin da masu wa’azi suka yi kokarin
fahimtar da su cewa wannan kure ne bayyananne sai
ka ga cewa suna ta kawo tawilce-tawilce da wasu
shubuhohi domin tabbatar da ra’ayinsu marar
makama da hujja!!
Haka nan in ka dubi yan bidi’ah nau’i daban-daban
da ake da su cikin Al’ummar Musulmi za ka rika
ganin yadda suke zaburowa da karfi suna kare son
zuciyarsu. Misali yanzu in ka yi kokarin fahimtar da
batijjane cewa: aqidarsa ta cewa Salatul Fatihi
saudaya tana daidai da Alkur’ani sau dari shida
wanda wannan yana nufin ke nan Salatul Fatihi ta fi
Alkur’ani sau dari biyar da casa’in da tara!! In ka
shaida musu cewa wannan akidah tasu wani nau’i ne
na ilhadi da raina Littafin Allah Madaukakin Sarki, to
nan da nan za ka ga cewa sun yi ca a kanka da
zage-zage, da bace-bace, kuma za ka ga cewa sun
nace suna ta yin tawilce-tawilce domin su tabbatar
da son zuciyarsa!!
To amma irin wannan hayaniya ta yan bidi’ah, da ‘yan
bin son zuciya sam bai kamata ba a ce za ta hana
masu wa’azi ci gaba da shiryar da Al’ummah zuwa ga
sahihiyar sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah
ba.
Muna rokon Allah muna kaskantar da kai a gabanSa
da ya tausaya Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce Ya
ba mu ikon bin ta, Ya kuma nuna mana karya karya
ce Ya ba mu ikon guje mata.
Ameeeeen.
@Danjagale’s Blog.
http://t.co/2wFeKmjyQW

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s