Tsofaffin Ministocin Jonathan sun sha kaye!

Tsofaffin Ministocin Jonathan sun sha kaye!

Wasu daga cikin ministocin da suka ajiye aikinsu a gwamnatin Goodluck Jonathan sun sha kaye a zaben fitar da gwani da akayi na jam’iyyar PDP.
Tsohon ministan yada labarai, Labaran Maku ya sha kashi a kokarinsa na samun tikitin zama dan takarar gwamna na PDP a jihar Nasarawa.
Can kuma a jihar Ebonyi tsohon ministan lafiya, Farfesa Onyebuchi Chukwu ne ya sha kashi a yayinda tsohon ministan kwadago, Emeka Wogu ya sha kaye a jihar Abia.
A jihar Delta kuwa tsohon ministan Niger Delta,
Godsday Orubebe ne ya sha kaye a yayinda Musiliu Obanikoro ya sha kaye a jihar Lagos a yukunrin samun tikitin zama gwamna a inuwar jam’iyyar PDP.
Kawo yanzu tsohon karamin ministan ilimi, Nyesom Wike ne kadai wanda ya samu nasarar zama dan takarar jam’iyyar PDP a jihar Rivers.
A tsakiyar watan Oktoba ne Mr Jonathan ya
sanarda cewa ministocinsa guda bakwai sun ajiye mukamansu domin shiga takarar gwamna a jihohinsu.

(Allahu Akbar!
Ya Allah! Yanda ka Haramtawa wadannan azzalumai tikitin zama yan takarar Gwamna, Allah ka haramtawa mai gidansu da duk magoya bayansa Tikitin jin dadin Rayuwar Duniya da Lahira).
@Danjagale’s Blog.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s