Matsalar Manhajar Android wajen Kariya

An gano matsalar manhajar Android da ke iya bayar da damar da za a iya kutse cikin bayanan katin dibar kudi na Banki na mai amfani da wasu manhajojin.
Kamfanin harkokin tsaro na intanet na BlueBox, ya ce manhajar Android ba ta cikakken bincike akan na’urorin kare kutse (IDs) kafin ta bai wa sauran manhajoji (Apps) dama ta musamman akan wayoyin komai-da-ruwanka da kananan kwamfutocin hannu.
Masu BlueBox suka ce matsalar ita ce masu wayoyin salula da kananan kwamfutoci na hannu na komai da ruwanka (Tablets) ba lalle sai sun bayar da izini ba, wata manhajar (Apps) take aiki a na’urorinsu.
Kamfanin ya ce ya sanar da Google tun da farko domin ya dauki matakan gyara manhajarsa (Operating System).
Google ya tabbatar cewa ya kirkiro abin da zai magance wannan matsala.
Mai magana da yawun kanfanin manhajar Android ta ce, suna godiya ga BlueBox da ya gano musu wannan matsala.
Ta ce, irin wannan bincike da wasu ke yi shi ne yake sanya wa Android ta na kara inganci.
Kuma ba tare da wani jinkiri ba suka aika da bayanan yadda za a kare matsalar ga abokanan huldar Android.
Har yanzu wasu wayoyin masu Android na fuskantar matsalar
Sai dai kuma har yanzu wadanda ke amfani da manhajar Android ta daga 2.1 zuwa ta 4.3 ba su samu hanyar magance matsalar ba.
Kuma wayoyin komai-da-ruwanka (Smart Phones) da kananan kwamfutocin hannu da ba su samu hanyar magance matsalar ba, na cikin hadari idan suka dauko wata manhaja ba daga rumbun Google Play Store ba.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s