Kungiyar IZALA‪ ‬ta Kasa ta Nemi Shehu Dahiru Bauchi da ya gaggauta janye kalaman da yayi akan Shehu Usman Dan Fodiyo da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad III.

Kiran ya fito ne daga bakin Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar na kasa Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, Shehin Malamin yace Irin maganganun M. Dahiru Bauchi ya yi game Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, da kuma Mujaddidi Shehu Uthmanu Dan Fodiyo lalle abin takaici ne matuka.
Hakikatan yin irin wadannan maganganu a irin wannan lokaci da muke ciki wani sashe ne na dabarun yakar al’ummar Arewacin Nigeria, da kuma al’ummar Musulmin Nigeria gaba daya da makiya wannan Al’ummah suke tsarawa to amma fa ya kamata a san cewa hakan ba ya nufin cewa shi mai wadannan maganganun yana da cikakkiyar masaniya kan wannan muguwar dabara ta makiya namu, ko kuma shi din wani yaniki ne kaitsaye daga cikin su wadannan makiya namu-.
Cikin maganganun batunci da M. Dahiru Bauchi yayi ya ambaci cewa mu a nan Nigeria muna da jikan Annabi mai tsira da amincin Allah! Ina jin yana ishara ne zuwa ga Sheik Ibrahim Sharif Saleh, to amma ni a dan karamin sani da na yi wa shi Sheik Ibrahim Saleh ba na jin zai goyi bayan irin wadannan bayanai mara makama da M. Dahiru Bauci ya yi.
Yana da kyau M. Dahiru Bauci ya gaggauta janye wadannan bayanai nasa, ya kuma nemi gafarar masu rai daga cikin wadanda ya zalunta da wadannan bayanai nasa.
Babban abin da muke bukata mu al’ummar Arewacin Nigeria, da dukkan Musulmin Nigeria da ma dukkan wani dan kasa na gari mai so wa Nigeria alheri a wannan lokaci shi ne mu nitsu mu maida hankulanmu a kan tsara hanyoyin da za mu bi domin sama wa wannan Kasa tamu kyakkyawan jagoranci.

Muna Rokon Allah Ya taimake mu, ya hada mana kan al’ummar Musulmi akan fadin Allah da Manzonsa (SAW).

Advertisements

One Reply to “Kungiyar IZALA‪ ‬ta Kasa ta Nemi Shehu Dahiru Bauchi da ya gaggauta janye kalaman da yayi akan Shehu Usman Dan Fodiyo da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad III.”

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s