Bam ya Hallaka Mutane 25 a Kaduna…… Wannan ne karo na biyu da Bam ya tashi a Kaduna cikin wata guda.

Rahotanni daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria na cewar wata mota makare da bam ta fashe inda ta hallaka mutane akalla 25 tare da raunata wasu da dama.
Rundunar ‘yan sandan jihar sun tabbatar da afkuwar lamarin tare da rasuwar mutane 25.
Wani shaida ya bayyanawa BBC cewar lamarin ya faru ne a kan titin Isa Kaita gab da titin Ahman Pategi da ke Unguwar Sarki a Kaduna.
A cewarsa, bam din ya fashe ne jim kadan bayan da wani babban malamin addinnin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya wuce da ayarin motoci bayan kamalla tafsirin Alkur’ani a dandanlin Murtala da ke tsakiyar Kaduna.
Sai dai babu abinda ya samu Sheikh Dahiru Usman Bauchi da ‘ya’yansa.
Mutumin da ya shaida lamarin ya kara da cewar baya da gawarwakin da ya kirga akwai mutane da dama da suka samu raunuka sannan kuma mutane na cikin firgici.
Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin, amma kuma kungiyar Boko Haram ce ke kaddamar da hare-hare a Nigeria inda ta hallaka dubban mutane tun daga shekara ta 2011.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s