Yan-Sanda a Najeriya sun haramta zanga-zangar neman ceton ‘yammatan Chibok.

A Najeriya, rundunar ‘yan sandan birnin tarayyar kasar, Abuja, ta haramta dukkan tarukan da suka shafi fafitika ta ceto ‘yan matan sakanadaren Chibok, wadda kungiyar nan ta “Bring Back Our Girls”, wato a maido mana ‘yammatanmu, ke sahun gaba-gaba.
Rundunar dai ta ce tarurrukan da ake yi babbar barazana ce ga tsaron kasa.
Sai dai kungiyar Bring Back Our Girls a nata bangaren, ta ce bayyana matakin da cewa ya saba da tsarin mulki irin na demokuradiyya.
Ta kuma ce za ta ci gaba da da wannan fafitika, don haka za a jira a ga abin da zai auku gobe idan wadannan masu zanga-zangar sun sake fita.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s