Kokarin Gano Rigakafin Cutar Malaria

Masu binciken kimiyya a Amurka sun ce sun kusan samar da riga kafin zazzabin cizon sauro.
A wani yanki a kasar Tanzania inda zazzabin cizon sauro ya yi katutu sun ce sun samu wasu gungun yara da ba sa kamuwa da cutar.
Gwajin da aka yi ya gano cewa wasu kwayoyin da suke kare garkuwar jikin dan Adam su ke fitar da wani sinadari da ke hana yaran kamuwa da cutar.
Binciken an gudanar da shi ne a kan wasu yara kananan su 1,000 a Tanzania din.
Masana kimiya sun wallafa sakamakon binciken na su a mujallar kiwon lafiya mai suna ‘Science’,
‘Gwaji a kan beraye’
Da aka sanyawa beraye irin wannan sinadarin sai aka gano cewa su ma berayen sun samu kariya daga cutar zazzabin cizon sauron.
Farfesa Jeks Kotis na asibitin tsuburin Rode na daga cikin wadanda suka a gudanar da binciken.
Kotis ya ce “Idan aka hada bayanan gwajin da aka yi wuri guda, za a iya ganin cewa abubuwane masu gamsarwa da suka nuna cewa da alama wannan riga-kafi ne da zai iya amfani a jikin dan adama”.
Sai dai masu binciken kimiyyar sun ce ana bukatar karin gwaji akan birai da mutane domin tabbatar da ingancin riga kafin.
Alkaluman da hukumar lafiya ta duniya ta fitar sun nuna cewar a shekara ta 2012, cutar zazzabin cizon sauro ta kashe mutane 600,000 galibinsu daga yankin Afrika kudu da hamadar Sahara.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s