YADDA AKE YIN SALLAR GAWA, SHARUDDANTA Da KABBARORINTA.

Dukkanin Malamai na Mazhabobi sunyi ittifaqi akan cewa SALLAR GAWA (JANAZAH) FARILLAH CE TA KIFAYAH. (wato irin farillar nan wacce wani zai iya dauke wa wani).
Sai dai an ruwaito daga Asbag (daya daga almajiran Imamu Malik) cewar Shi Sunnah ce awajensa.
Za’a iya yin Sallar gawa akowanne Lokaci ko dare ko rana, Inji IMAM SHAFI’IY (RA).
Amma IMAMU AHMAD DA IMAM ABU HANEEFAH (RA) Sunce Makruhi ne ayi sallar Janazah alokutan nan guda Uku.
1. bayan Sallar asubah har zuwa fitowar rana.
2. Bayan sallar la’asar har zuwa faduwar rana..
3. Lokacin da Limamin Jumu’a ya hau kan mimbari yake khudubah.
Shi kuwa IMAMU MALIK (RA) Yace za’a iya yin Sallar Janazah akowanne lokaci in banda lokacin fitowar rana da kuma lokacin faduwarta, yace Makruhi ne.

SHARUDANTA:
Dukkan Maluman Mazhabobin sunyi ittifaqi akan cewa wadannan sune sharudan ingancin Sallar Janazah:
* Tsarki da alwala.
* Suturce Al’aurah.
* Kallon Alqiblah.
Amma Sha’aby da Ibnu Jareer sunce za’a iya yi ko ba tare da alwala ba.
Imam Shafi’iy da Abu Yusuf sunce Limami yana tsayawa ne adaidai kan mutum Namiji, ita kuma mace Liman zai tsaya ne adaidai tsakiyar ta.
Amma IMAMU MALIK DA IMAM ABU HANEEFAH Sunce Liman zai tsaya ne adaidai Qirjin Namiji, ita kuma mace zai tsaya ne adaidai tsakiyarta.

KABBARORINTA :
Kabbarori hudu ake yi asallar janazah abisa ittifakin Mazhabobin nan hudu.
Sai dai an ruwaito Kabbara 3 daga Imam Ibnu Sireen.
Sannan akwai wata ruwayar daga Abdullahi bn Mas’ud (RA) yace: “Manzon Allah (SAW) yayi kabbara 9 abisa Janazah, Sannan yayi 7, Sannan yayi 5, Sannan yayi 4. Kuyi ta kabbarawa mutukar Limaminku ya kabbara. Koda ya Qara abisa hudu to sallar ba ta ‘baci ba”.
Imamush-Shafi’iy yace Zaka cira hannuwanka zuwa kafadunka ayayin dukkan kabbarorin. Amma IMAMU MALIK DA IMAM ABU HANIFAH sunce ba zaka cira hannuwanka ba sai dai akabbarar farko kawai..
Karanta Fatiha bayan kabbarar farko, Farilla ne awajen Imam Shafi’iy da Imamu Ahmad. Amma Imamu Malik da Abu Haneefa Sunce BA ZAKA KARANTA KOMAI BA DAGA CIKIN AYOYIN ALQUR’ANI.
Sannan ana yin Salatun Nabiyyi (SAW) sannan kuma sai Addu’a ga mamacin da sauran al’ummar musulmi abayan Kabbara ta biyu data uku da ta hudu ajere (Respectively).
Sannan mutum zai yi sallama ne guda biyu abisa Mazhabobi uku.
Amma Hanbaliyya sunce Sallama daya zaka yi a damanka.
Aduba Thamrud-dany Babin Sallar Janazah da kuma Rahmatul-Ummah shafi na 81.
WALLAHU A’ALAM.
Allah ya yasa mu cika da imani, Ameeen.

Advertisements

3 Replies to “YADDA AKE YIN SALLAR GAWA, SHARUDDANTA Da KABBARORINTA.”

  1. ALLAHU AKBAR .ALLAH YA KARA MUKU BASIRA YADDA KUKAYI KOKARIN YADA WANNAN ILMI NA WADANNAN MALAMAI.WANDA SUN BAR DUNIYA AMMA KAMAR SUNANAN SABODA ILMI DA SUKA YADA TA HANYAR DA AWA.AMIN.

    Like

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s