Ta Kashe Kawarta Dalilin Facebook

Buduwar mai kimanin shekaru 16 ta hallaka kawarata har lahira ta hanyar caka mata wuka fite da sau 60, sakamakon wani sabani da ya shiga tsakaninsu ta dandalin sada zumuncin nan na Facebook. Jaridar Notus, ta kasar Medico, ita ta rawaito wannan labarin, inda rahotannin suka nuna cewa Erandy Elizabeth Gutierrez da Anel Baez, kawayen da bacci ne kawai ke raba su, inda a mafi yawancin lokuta suna daukar hoto tare don bazawa a shin dandalin zumuntar.
Lamarin ya faru ne bayan da Anel ta dauki wani hoton da suka dauka tare da Erandy tsirara, ta kuma sanya a shafin yanar gizon zamani, wanda yin hakan ya fusata Gutierrez ta sha alwashin binne kawarta tata kafin karshen shekarar nan.
“Kina ganin kamar ina da saukin kai, amma a yadda nake gani yanzu, na kashe sau” Erandy ta rubuta a shafinta na Twitter a kwanan baya, wanda yanzu an goge rubutun.
Duk irin wannan kurari da Erandy ta rika ti, bai sanya Baez jin komai a ranta ba. “Ina ganin zan iya tsira daga sharrinta” ina ji Baez.
Rahotannin sun bayyana cewa Erandy ta gayyaci Gutierrez gidan da ke Guamuchili, da nufin su shirya kuma su manta duk abin da ya faru a baya.
Bayan shigarsu gidan, bakuwar ce za ta shiga bandaki, amma sai ta shi ga kicin inda ta yi amfani da wannan damar ta dauko ta dawo falo ta rika caka mata har sai da Beaz ta ce ga garinku nan. An dai samu marigayiyar da tabo sukar wuka har 65 a sassan jikinta.
Kamar ‘yan sanda suka tabbatar, bayan kisan killa da ta aikata, Gutierrez ta yi amfani da wani wanda za ta kaucewa zargin aikata laifin, daga ciki har da halarta bikin binne gawar, kafin daga karshe jami’an tsaro su yi awon gaba da ita.
Idan har zargin da ake yi mata ya tabbata cewa ta aikata laifin. Kotun kasar za ta yanke hukunci shekaru bakwai ne kawai a gida yari.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s