Manufar Rayuwa: Mummunan Zato

Kowa ma ya san zato zunubi ne, ko da kuwa ya zamo gaskiya. Duk da haka, mutanen wannan duniya sun toshe kofofin zukatansu wurin hana ma zato yin zaman dirshan. Da yawa ma zukatan na su a bude su ke su na marhaba da wani al’amari wanda za su yi zato a cikinshi. Wuce nan ma, wasu farautar laifuka ko bibiyan mutane don su zargi ayyukansu su ke yi.
Mutane dabi’unsu daban daban ne, sai dai babu wata dabi’a wacce ba a iya rusa ta ko a gina ta. Shi ne ma ya fi dacewa ga iyaye su zama maluman farko wurin shigar da dabi’u ga dansu. Misali, akwai wani sarki mai suna Akbar a yankin indiya wanda ya rayu a tsakankanin shekarar 1542 zuwa 1602 wanda ya ke son samun tabbaci akan jijitar wai idan a ka haifi yaro ya zama ba a koyar da shi kowanne harshe ba, zai girma ne ya na mai magana da harshen Yahudanci.
Sai sarkin ya sa a ka kebe mi shi wasu jarirai guda goma. Da jariran su ka girma sai ya zama ba su iya kowanne harshe (sabanin cewa za su tashi da yaren Yahudanci), haka nan kuma dabi’unsu irin na dabbobi. Hatta tafiya ba su iya yi sai dai rarrafe kamar yadda tumaki ke yi.
Wannan nazari kadai ya isa ya gamsar da mu cewa duk mutumin da mahaifanshi su ka wawaitar da yarintarshi ya na iya girman sakarci da dabi’u rikitattu. Ko kuma ya hadu da wasu su jibga mishi irin tasu dabi’ar. A nan za mu iya karkasa dabi’un mutane mu ware masu kyau da marasa kyau.
A hannu daya sai mu ce dabi’u masu kyau natijarsu na komawa zuwa ga iyaye ne, marasa kyau ma na komawa gare su ne.
Kyautata zato da munana zato dukkaninsu dabi’u ne wadanda ke kishiyantar juna. Haka nan kuma ya na da kyau mu fahimci cewa dabi’u guda biyu wadanda ke karo da juna (kishiyoyi) ba su taba haduwa a lokaci guda wurin tasirantuwa ga mutum.
Ko dai ka kasance mai mummunar dabi’a ko kuma mai kyakkyawa. Kamar dabi’ar fushi ne, ai ba zai yiwu a samu wani mutum mai masifaffen fushi ba, sannan kuma a lokaci guda mai tsananin hakuri.
Idan ka ga mutum ya na kyautatawa mutane zato a mu’amalolinshi da su, babu mamaki ko kadan akan cewa iyayenshi mutane ne masu kyautata zato. Mafi yawan lokuta idan kuma ka ga wani na munana zato a kodayaushe, to iyayenshi ma ta na iya yiwuwa halinsu kenan.
Tun ice na danye a ke lankwasa shi. Dalilan da su ka sa a tashin farko na fara da zargin iyaye shi ne; su ne mutanen farko da linzamin rayuwar dansu ke a hannunsu. Idan sun kasance masu hikima da hangen nesa, dansu zai kwaikwayo hikima da hangen nesar nan ta su.
Daga cikin matakan da ya kamata iyaye su dauka don kauracewa dansu dabi’ar munana zato sun kunshi daina zargi. Kar iyayen su rika yawan zargi, ta yadda har dansu zai iya koyo. Zargi a nan na nufin kar mata ta rika zargin mijinta ba gaira ba dalili, shi ma mijin haka.
Sannan kuma idan har wani abu ya faru wanda iyayen ba su da tabbaci ko hakikani sai su ci gaba da bincike don samun sahihanci ko kuma su fita batun maganar kawai kwata kwata. Idan ba haka ba dan su zai girma da yawo da jita jita da saurin lakaba ma mutane zantukan da ba gaskiya ba.
Duk wannan misalin ina kokarin nuna rawar da iyaye za su iya takawa ne wurin shigar da dabi’ar kyautata zato ga ‘ya ‘yansu, cikin ruwan sanyi ba tare da wani wahala ba.
A wannan zamanin da mu ke ciki munana zato na daya daga ‘yan sahun gaban al’amuran da ke tsinke igiyar aure. Munana zaton na farawa ne daga zargi; idan zargin ya yi yawa sai zuciya ta fara shigo da zato, a haka zaton zai ta girma har ya zama mummuna, sai a nemi aure a rasa.
Munana zato har walayau shi ne ke gina katangar karfe tsakanin ubangida da yaronshi. A wasu lokutan matsala ce kankanuwa wacce ba ta bukatar sa’o’i (hours) an magance ta, amma sakamakon munana zato sai ta kai ga an yi rabuwar tsiya.
Babban matsalar mutumin da ke munana zato shi ne halinshi ba halin kwarai ba ne. bincike ma ya nuna cewa da yawa wadanda ke saurin munana zato ba tare da bincike ba, su na yin haka ne saboda abun da su ke zato a kai aikinsu ne.
Wani abu da masu wannan mugun hali ba su fahimta ba shi ne, idan mutum ya yi nisa a harkar munana zato abun na rika a zuciyarshi ne. ta yadda ko akan idonshi a ka assasa wani aikin alheri, zai ce sharri ne.
Idan ka na so ka taimaki kanka ka daina munana ma mutane zato, shi ya fi komi sauki ga duk mai son dainawa, amma kuma akwai wahala ga wanda ya rika a harkar. Kawai sai ka daina bibiyan ayyukan mutane, musamman ma abubuwan da babu ruwanka a cikinsu. Sannan ka sa alheri a zuciyarka sama da sharri, idan ka yi haka, za ka tsira daga mummunan zato.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s