TAMBAYA Akan Romance

Assaalamu alaikum Allah ya karawa malam hazaka da fahimta. Malam tambayata anan sune
1-malam na kasance ina dan yin soyayya tare da romance dan haka miye hukuncin mai yin romance?
2-malam ban taba saduwa da mace ba amma nasan ko ina. To idan na tuba yaya tubana?
3-malam ya maganar da ake cewa in kayi zina da wata sai anyi da taka dan ance ita Zina bashi ce. miye gaskiyar maganar??
kuma inna tuba za a dau fansar?
Nagode.
AMSA
******
Hukuncin Romance shine: Haramun ne. Domin shima wani nau’I ne na Zina.
Manzon Allah (saww) yace an rubuta ma kowacce ga’bar Dan Adam nata kason na zina:
Zinar hannu ita ce ta’bawa (ta’ba matar da bata halatta gareka ba)
Zinar Qafa shine tafiya (wajen da bai halatta gareka ba).
Idan idanu shine Kallo (kallon abinda bai halatta gareka ba).
Kuma hadisi ne Sahihi.
Don haka wannan abinda kakeyi shima zina ne. Kuma BABBU SHAKKA duk irin yadda kayi da ‘ya’yan mutane sai an aikata irin haka akan Qanwarka ko yayarka, ko UWARKA MAHAIFIYA, ko Qanwar Mahaifinka, ko Qanwar mahaifiyarka, ko kuma ‘YARKA TA CIKINKA.
Akwai wani Sarki daga cikin Sarakunan Daular ABBASIYYAH, yayi kokonton anya kuwa wannan maganar haka take?
Don haka ya sumbanci matar da ba tasa ba, kuma shima yana nan wata rana ya haifi ‘Ya mace, kuma ta girma ta zama budurwa, tana cikin tafiya a kasuwa, ga Dakaru masu kareta.
Amma duk da haka sai da wani ‘Dan-Dako yazo ya rungumeta ya sumbanceta.
Ya kai Saurayi!! Ina kiranka kaji tsoron Allah ka tuba, tuba irin wacce Allah yake so. Ba wai tuba irinta mayaudara ba.
Domin hakika babu alamar Nadama acikin maganganunka. Kuma Allah yana jinka.
Idan kana tunanin cewa zaka je kayi Iskanci da ‘ya’yan mutane, sannan zakaje kace ka tuba, don kar ayi da ‘Yarka, to kayi kuskure.
Allah ya fika wayo, kuma yana nan yana jiranka a madakata.
Idan ka tuba, tubar gaskia, in Allah yaga dama ya karba shikenan. In kuwa tuban muzuru kayi, to kaima kasan sakamakon mayaudara shine Tozarta anan duniya da kuma lahira.
Allah ya kiyaye mu daga aikata zina da dangoginta.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s