An samu dantayi mai kai biyu a cikin wata saniya a Legas

A karshen makon da ya gabata ne mahautan kasuwar shanu ta Oko-Oba da ke unguwar Agege a Legas suka ga wani abin mamaki yayin da aka gano wani dantayin saniya a lokacin da ake fede ta.
Lamarin ya ba mutane mamaki domin saniyar ba ta nuna wata alama ta rashin lafiya ba sakamokon dantayin da take dauke da shi.
Wani wanda ya ga yadda lamarin ya auku mai suna Alhaji Rabi’u Maihoto ya bayyana wa Aminiya ta wayar salula cewa wani Bayarabe ne ya sayi saniyar.
Ya ci gaba da cewa, bayan ya sayi saniyar sai ya bayar a yanka a gyara masa naman. Ana cikin fida sai kawai aka ga dantayi mai kai biyu a cikinta da ransa. Har lokacin da aka ciro shi yana da rai, sai daga bisani ya mutu.
Alhaji Rabi’u Maihoto ya kara da cewa, “Lamarin ya ba mu mamaki domin dantayin an kammala halitattarsa kuma da an bar saniyar, ba a yanka ta ba da babu shakka za ta haife shi”.
Ya bayyana cewa shi ne karo na farko da aka taba samun dantayi mai kai biyu a kasuwar, kuma da ransa.
Jim kadan da bazuwar labarin, sai mutane suka taru a wurin da ake fidar saniyar suna kallo, wasu na daukar hoto da wayar salulularsu wasu kuma na sanyawa masu daukar hotuna da na’urar daukar hoto suna daukar musu hoton.
Masu sana’ar daukar hoto a kasuwar sun sami ciniki sosai saboda yadda mutane suka rika sayen hoton dantayin.
Daga bisani an ware dantayin gefe guda don kada namansa ya hadu da na mahaifiyarsa inda daga bisani aka dauke shi aka jefar a inda hukumar kasuwar ta tanada.
In ba a manta ba, a kwanakin baya aka gano wani dantayi a cikin wata tunkiya mai siffofi dabbobi biyar a kasuwar Alaba Rago da ya yi kama da dabbobi daban-daban kamar mage da kare da zomo da kyanwa da alade.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s