Sun datse masa hannu don yana bin bashin Naira 200.

A cikin makon da ya gabata ne iyayen wadansu yara da makwabtansu da ke zaune a unguwar Awala da ke filin jirgi a unguwar Tudun Wada ta karamar Hukumar Gusau a Jihar Zamfara suka fada cikin tashin hankali da jimami da kuma firgici, a yayin da wadansu matasa biyu da aka gayyato su suka sare wa wani matashi mai suna Rabi’u wuyan hannu har ya fadi kasa.
Yadda abin ya faru kuwa shi ne, mahaifiyar Rabi’u ce ta bai wa danta waya domin ya sayar mata, da aka je wajen saidawa sai wani mai suna Mannir ya saye ta a kan Naira 1,700, sai ya ba da Naira 1,500, amma daga baya cikon sauran Naira dari biyu ya gagara.
Da yake yi wa Aminiya bayani lokacin da wakilinmu ya same shi a kan gadon asibiti inda ake duba shi, Rabi’u ya bayyana cewa, ganin ana ta yi masa yawo da hankali kan Naira dari biyu, sai ya yanke shawarar sanar da magabata don su karba masa hakkinsa. Wannan ya sa ya tafi wajen mahaifiyar Mannir. “Ina tsaye da mahaifiyarsa, ina fada mata yadda abin ya faru tsakaninmu, sai Mannir ya zo ya same mu, da ya ganmu sai ya koma, bayan kamar minti biyar sai ya dawo, dawowarsa da kamar minti biyu sai ga wadannan matasa sun zo suna kashe mini idanu da fitila, daga hannun da na yi don in kare hasken da hannun dama sai kawai na ji sara, nan na yi tsalle na ruga da gudu. Sai na tafi wajen ’yan sanda don su taimaka mini, ko da dan sandan ya haska sai ya ga babu hannu, sai ya ce, “Me ke faruwa ne, ina hannun?” Sai na ce ’yan ta’adda ne suka sare ni”. Inji Rabi’u.
Da wakilinmu ya tambaye shi ko ya san wadanda suka aikata masa wannan mugun aiki, sai Rabi’u ya ce, “Na san su kwarai da gaske da ma haka suke, sun addabi kowa, don sukan zo suna saran jama’a a wadansu lokuta a baya. Akwai wani mai suna Dawa Shafi’u da kuma wani wai shi dan Akilu , kuma ni babu abin da ya taba hada ni da su, ba mu taba samun wata matsala a tsakaninmu ba. Shi Mannir ne ya gayyato su don su zo su sare ni, kuma sun sare ni, amma yanzu tun da an kama su, ina rokon kotu ta bi mini hakkina.”
Malam Muhammad Idris, dan uwa ne ga wanda aka sara, ya bayyana wa Aminiya cewa, saboda Rabi’u ya je bin bashin Naira dari biyu suka sare shi, amma tun da an kama su lallai za mu bi masa hakkinsa, yanzu za mu saurari ’yan sanda su gama bincike ne sannan sai su kai mu kotu domin ta bi masa hakkinsa na cire masa hannu da aka yi.
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin mahaifiyar Mannir, wadda danta ne ake bi bashin, kuma a gabanta ne abin ya faru, sai dai abin ya ci tura.
DSP Lawal Abdullahi shi ne jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, a zantawarsa da wakilinmu kan lamarin, ya bayyana cewa, wadanda ake zargi suna hannu, idan suka kammala bincikensu za su kai su kotu.

Advertisements

One Reply to “Sun datse masa hannu don yana bin bashin Naira 200.”

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s