“Yanayin mutum kan bazu a Facebook”

Wani bincike na jami’ar California, Yale a Amurka ya nuna cewa, yanayin da mutane ke ciki na iya yaduwa a dandalin sa da zumunta, kamar Facebook.
Binciken ya yi amfani da tsokacin miliyoyin masu amfani da shafin Facebook, inda ya duba tasirin ruwan sama.
Masu binciken sun gano cewa ta hanyar mutum guda da ruwan sama ya shafa, hakan na tasiri a kan wasu karin mutane biyu.
“Magana a kan yanayin da mutane ke ciki a wani guri, kan bazu a duniya a rana guda,”
Sun duba tsokacin mutane abokan wandanda ruwan sama ya shafa, da kuma wadanda ke zaune a biranen da yanayinsu ke da dan dama-dama.
Sakamakon ya nuna cewa duk tsokaci na bakin ciki guda daya, kan janyo wasu irinsa 1.29 fiye da yadda aka saba gani, a tsakanin abokai.
Haka kuma abin mamakin shi ne, tsokaci na farin ciki ya fi tasiri sosai, inda yake janyo irinsa 1.79.
A cewar masu binciken “Hakan na nufin cewa yanayi ko halin da mutane ke ciki, kan yadu ta dandalin sa da zumunta, ta yadda ya kan kai ga samun tarin mutanen dake samun kansu cikin farin ciki ko kuma bakin ciki.”
“A sakamakon haka za mu iya ganin karuwa game da yanayin da mutane ke ciki a duniya, da zai iya janyo karin rashin tabbas game da komai, kama daga siyasa zuwa tattalin arziki. “

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s