Ta Cinna Wa Kanta Wuta Dalilin Sabani Da Saurayi

A sakamakon tsananin kishin da ya turnike ta saboda yadda dadironta, wani dan kabilar Ibo mai suna Mista Benge ya juya mata baya zuwa wata yarinya ta daban; bayan tsawon lokacin da suka kwashe suna zaman masha’a, wata budurwa mai zaman kanta ta yayyafa wa jikinta man fetur sannan ta cinna wuta a kauyen Alkali da ke Karamar Hukumar Bursari ta jihar Yobe. Al’amarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata.
Budurwar mai suna Salma Potiskum, ta jefa kanta cikin wani mummunan hali saboda yadda wutar da ta cinna wa kanta ta yi mata illa abin babu kyaun gani. Tun daga wuyanta har gadon bayanta duk sun kone.
Wakilinmu ya garzaya babban asibitin Gashuwa inda wannan budurwar ta ke jinya inda aka same ta cikin wani mawuyacin hali tana ta faman kuka tana fadin “Wayyo Allah, innalillahi wa’inna ilaihir rajun; Lahaula wala kuwwata illa billahil aliyyul azeem”. Sauran majinyatan dake dakin dai sun yi cirko-cirko saboda yadda ihu da karajin budurwar ya hana kowa sakat.
Sai dai kuma, duk da halin da take ciki, ta yi bayanin ainihin abin da ya faru da ita “Mun samu sabani ne da saurayin da muke tare, rana tsaka ya canja min fuska duk da dadewar da muka yi, a sanadiyyar haka sai na rasa abin da ya ke min dadi a duniyar nan, shi ne na yanke shawarar in kona kaina kawai in mutu dan in huta da bakin ciki. Hakika wannan danyen hukunci da na yanke wa kaina, ya tsunduma ni cikin halin ni’yasu, kuma tabbas na yi nadamar daukar wannan matakin”.
Ta yi Kira ga mata masu irin sana’ar tata da cewa su rika yin kaffa-kaffa da maza domin idan ba su yi hankali ba, suna iya jefa rayuwarsu cikin mawuyacin hali irin yadda ta fada ciki.
Wakilin namu yi tattaki zuwa kauyen Alkalin domin bin diddigin yadda wannan al’amarin ya faru a wajen Badalar Walawa, kana da kokarin jin ta bakin Mista Benge. Wani ganau, da ya bukaci a boye sunansa, ya bayyana mana cewa “Muna nan zaune da safiyar yau, sai muka ji ihun neman gudumawa, da muka shiga sai muka tarar da ita Salma Potiskum jikinta yana ci da wuta; ita ta kona kanta da kanta. Nan take muka taimaka aka kashe mata wutar; daga baya aka dauke ta zuwa asibiti a Gashuwa”.
sai dai kuma, duk kokarin jin ta bakin musabbabin wannan ta’asar, Mista Benge, abin ya ci tura, domin an ce yana asibiti tare da majinyaciyar alhalin kuma a can din ma an tafi ba a same shi ba. Amma wata kawa ga Salma Potiskum ta bayyana cewa “ita Salma ta cinna wa kanta wuta ne ta dalilin bakin cikin da saurayinta wanda suka dade tare ya cusa ma ta daga baya, ya kuma nuna mata cewa ba zai ci gaba da zama da ita ba”.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s