Mai son sana’ata kadai zan aura -Budurwa mai tuka keken NAPEP

Wakiliyar mu ta samu damar tattaunawa da wata budurwa mai suna Kenny T. Agboola, da ke sana’ar tuka babur mai kafa uku (Kake Napep ko Adaidaita Sahu ko kuma Marwa kamar yadda ake kiransa a jihar Legas). Kenny T Agboola ta bayyana irin kalubalen da take fuskanta a matsayinta na mace da ke sana’ar da maza ne kawai suka yi fice da ita, ta bayyana dalilin da ya sa ta shiga sana’ar da kuma burin da take so ta cimma. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Za mu so ki gabatar da kanki?
Kenny: Sunana Kenny T. Agboola, an haife ni jihar Ogun. Na kai kimanin shekaru 24 da haihuwa. Daga jihar Ogun iyayena suka dawo jihar Legas tare da ni. A jihar Legas na tashi a nan na girma. A jihar Legas na yi makarantar firamare da sakandire. Saboda haka zan iya cewa a jihar Legas na yi rayuwa ta. Idan na ce na fi sanin Legas a kan jihar Ogun ban yi karya ba.
Aminiya: Me ya ba ki sha’awa kika shiga sana’ar tukin babur din Marwa?
Kenny: Gaskiya abin da ya ba ni sha’awa shi ne, da farko dai ni ba ci-ma-zaune ba ce, kuma na ga maza ne kawai suke yi, saboda haka sai na fara tunanin cewa me zai sa maza ne kawai suke sana’ar nan, ai ya kamata a samu mata a cikinta. Kuma na ga makuden kudin da suke samu, sai kawai na yanke shawarar shiga cikinta don ni ma na rika gwagwarmaya da su, na samu abin da zan rufa wa kaina asiri. Saboda haka sai na shiga don na gwada sa’ata. Da ma ni tun ina makaranta nake sha’awar kalubantar maza.
Aminiya: Da ma kin iya tuka babur kafin ki shiga sana’ar?
Kenny: Ban iya tuka babur ba kuma ban taba gwadawa ba, sai a lokacin da na shiga sana’ar sannan na koya. Na je inda ake koya na biya kudi na koya cikin wata guda. Sannan wani mutum ya saya mini sabon babur ya ba ni, nake ajiye masa balas. Yau shekara ta kusan biyu ina yi, kuma kwalliya tana biyan kudin sabulu. Da ma ni abin da na fi iyawa shi ne kasuwanci, saboda mahaifiyata tana sayar da kifi a kasuwar Ilefoja.
Aminiya: Shin sana’ar haya da babur ta fi sayar da kifi ne?
Kenny: Gaskiya a ganina ta fi, saboda ina samun alheri daidai gwargwado, kuma ka ga a da ina zaune a karkashin mahaifiyata ce, amma yanzu ina zaman kaina ne. Saboda haka zaman kaina da nake yi ya fi dadi saboda babu wanda zai tsangwame ni ya rika tambaya ta dalilin da ya sa ban fito kasuwa da wuri ba.
Aminiya: Kin ce kin yi makarantar boko, shin kina da burin komawa makaranta nan gaba?
Kenny: Gaskiya ne na yi karatun boko daidai gwargwado. Na yi makarantar firamaren Ebeneza da ke unguwar Egbeda da kuma babbar sakandire da ke yankin karamar hukumar Alimosho. A yanzu ko nan gaba ba ni da burin ci gaba da karatun boko. Zan ci gaba da yin sana’at ta yin hayar babur. Idan na samu sana’ar da ta fi ta sai na daina. Amma yanzu ina so kuma ina jin dadin sana’ar.
Aminiya: Wane kalubale kike fuskanta daga abokan sana’arki maza
Kenny: Gaskiya akwai kalubale da yawa. Ka san su maza gani suke yi mace raguwa ce, ci-ma-zaune, ba za ta iya komai ba. Amma ni ina nuna musu cewa ba haka ba ne, duk abin da da namiji ya yi mace idan ta daure za ta iya. Shi ya sa nake bin su a hankali, ina zaman lafiya da su, ina raha da kowa, suna kaunata, ina kaunarsu. Saboda ina burge su.
Aminiya: Sauran maza masu hawa babur dinki fa?
Kenny: Su ma suna nuna mini kauna, don har wadansu mazan sun fi son su hau babur dina saboda burge su da nake yi da irin tukin da nake yi cikin nutsuwa da lura. Shi ya sa nake da abokan hulda maza da yawa. A cikin fasinjojina maza sun fi yawa. Haka su ma jami’an tsaro na ’yan sanda da sauransu, duk lokacin da suka gan ni suna karfafa mini gwiwa. Shi ya sa nake samun kudi sosai fiye da abokan sana’ata. Wadansu sukan tausaya mini su kara mini kudi, wadansu ma sukan kara mini kudi saboda burge su da na yi na kasancewa mace mai tuka babur.
Aminiya: Shin za ki ci gaba da yin sana’ar ko da bayan aurenki?
Kenny: Ai ba zan bar yin wannan sana’a ba har sai idan mijin da zan aura ya amince zai bude mini kasuwancin da ya fi sana’ata samun kudi. Akwai wani saurayi da ya ce yana so na zai aure ni idan na bar yin sana’ar tuka babur, sai na ce masa zai bude mini kasuwancin da ya fi shi? sai ya ce ba zai iya ba, ni kuwa sai na ce idan ba zai sama mini wata sana’a da ta fi ta ba, ba zan aure shi ba, haka shi ne dalilin rabuwarmu. Samari da yawa sun sha fitowa suna nuna mini cewa suna sona amma ba sa son sana’ata, ni kuwa sai na ce musu duk wanda ba ya son sana’a ta ni ma ba na sonsa. Wadansu mazan kuwa tsorona suke yi, gani suke na fi karfinsu, ba za su iya rike ni ba. Ni kuwa ba zan auri mijin da ba ya son sana’at ba, sai wanda yake son sana’ar da nake yi, wanda zai ba ni ’yancin neman na kaina. Ka san su maza wani lokaci sun cika son kansu.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s