Kurma mai rubutu da kafa da ta fi masu hannu kwazo

Wata yarinya ‘yar shekara 17 da haihuwa mai suna Zainab Muntari, wadda kurma ce kuma hannayenta ba sa aiki, da ke zaune a garin Jos babban birnin jihar Filato, ta nuna wa duniya cewa nakasa ba ta hana neman ilimi, domin kuwa duk da halin take ciki yanzu haka tana nan tana karatu da rubutu da kafa a makarantar Sunnah Pribate da ke Unguwar Rimi a garin Jos.
Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan yarinya, Sarkin kuramen Jos kuma shugaban sashin koyar da nakasassu na wannan makaranta, Malam Abubakar Sa’idu, ya bayyana cewa, a lokacin da aka kawo wannan yarinya, ganin cewa kurma ce kuma hannayenta ba sa aiki, ‘’a matsayina na malaminsu sai na tsara yadda zan karantar da ita, inda na koya mata yadda ake rubutu da kafa, har ta iya, ta ma fi ni iya rubutun.’’
Ya ce, ’’ idan tana son wani abu ko kuma tana son yin wani abu, sai ta rubuta mini da kafa. Muna karantar da ita da baki ne, kuma tana gane dukkan abubuwan da muke karantar da ita fiye da wadansu kuramen ma da muke karantar da su a wannan makarantar.’’
Ya ci gaba da cewa, ‘’wannan yarinya, wadda a halin yanzu take aji uku na firamare a wannan makaranta, ta samu wannan nakasar ce a sakamakon kamuwa da cutar sankarau tun tana da shekara 8. A lokacin da ta kamu da wannan cuta ta sankarau an yi ta yin magungunan gargajiya domin ana tsamanin aljanu ne. Amma daga baya da aka je asibitin koyarwa na jami’ar Jos [ JUTH] a nan ne aka gano cewa cutar sankarau ce ta kama ta, ba aljanu ba kamar yadda aka yi tsammani.
Sarkin kuramen ya bayyana godiyarsu ga hukumar gudanarwar wannan makarantar kan kokarin da ta yi na bude wannan sashi na koyar da nakasassu kyauta. Ya ce yanzu haka a wannan makarantar akwai kurame da sauran nakasassu da suke karatun firamre da sakandire.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da sauran kungiyoyi su yi koyi da wannan makaranta wajen tallafa wa nakasassu ta hanyar daukar nauyin karatunsu a makarantu.
Shi ma a zantawarsa da wakilinmu, shugaban makarantar Malam Idris Abdullahi Sangie, ya bayyana cewa sun bude wannan sashi na karantar da nakasassu, da suka hada da guragu da kurame da sauran nakasassu, kyauta ne domin su tallafa musu su saboda su dogara da kansu su bar barace-barace.
Ya kara da cewa, akalla suna da nakasasu, watau guragu da kurame da sauran nakasassu guda 100 da suke koyar da su kyauta. Haka kuma suna karantar da yara marayu sama da 170 kyauta.
Ya ce, ‘’burinmu shi ne idan nakasassun suka kammala karatun nasu su samu abin da za su yi a kasa, su amfanar da kansu da al’umma baki daya.’’
Shugaban makarantar ya kara da cewa, ‘’yadda muke yi wajen daukar nakasassu a wannan makaranta shi ne, duk inda na ga nakasashe na kan kira shi na ce ya zo wannan makaranta domin a yi masa rijista. Wadansu kuma iyayensu ne suke kawo su, wadansu kuma su suke kawo kansu da kansu.’’
Ya kara da cewa, ‘’muna son mu ga mun bada gudunmawarmu wajen dakile dukkan wata hanya ta yin barace-barace, domin idan aka karantar da nakasassu babu maganar bara, su ma za su shiga cikin al’umma su bada gudunmawarsu.’’

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s