Google zai shiga fasahar na’urorin sawa

Kamfanin Google, ya fadada rassansa ta hanyar shiga wani bangare na kasuwar fasahar na’urorin sanya wa, inda zai kera na’urar dake bunkasa kikirar manhajoji.
Na’urar za ta ba masu amfani da ita damar kirkirar wasu na’urori na sanya wa a jiki, kamar agogon komai da ruwanka da kayan motsa jiki ta hanyar amfani da masarrafar Android.
Kawo yanzu gilashin ido ne kawai babban hobbasan da kamfanin ya yi a bangaren na’urorin da ake sanya wa.
Gilashi ne dake hade da kamara, wanda kuma ake iya ba umarni da murya, ba a fara sayar da shi ga jama’a ba, amma wasu sun gwada shi.
“Google na daukar batun na’urorin da ake sanya wa da muhimmanci, kuma ya kamata kowa ma ya dauke su da muhimmanci.” In ji mataimakin shugaban kamfanin a bangaren bincike, John Delaney.
Ya kara da cewa “Google zai shiga kasuwa a goga da shi, bugu da kari zai bada sarari ga wasu, musamman ta hanyar taimakawa masu kirkirar manhajar Android.”
Samsung ya yi agogon komai da ruwanka, Samsung Galaxy Gear dake amfani da manhajar Android, amma daga baya ya fitar da Gear 2 dake amfani da manhajar Tizen.
Yayin da rahotanni ke cewa kamfanin Apple na aiki a kan agogon komai da ruwanka da zai yi amfani da masarrafar da ake amafani da ita a wayoyin komai da ruwanka na iphone da kuma kwamfutar hannu ta ipad.
Mafi yawan wayoyi na komai da ruwanka na amfani da masarrafar Android ne, kuma ana sa ran sayar da wasu na’urori sama da biliyan daya dake amfani da manhajar Android a wannan shekarar, a cewar kamfanin Gatner mai bincike a kan harkar kayayyakin fasaha.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s