Da gaske akwai bayi miliyan 20 a duniya?

Wasu kasashen yankin Caribbean suna bukatar diyya daga wajen kasashen Turai saboda cinikin bayi da aka yi a shekarun da suka wuce.
A halin yanzu dai wani fitaccen darektan shirya fina-finai Steve McQueen ya ce a fadin duniya akwai bayi kusan miliyan 21.
Shi dai McQueen ya ce ya samu wadannan alkaluman ne daga wajen kungiyar kwadago ta duniya wato ILO.
A cikin fim din McQueen mai suna ’12 Years a Slave’ ya bayyana yadda aka yi cinikin bayi a duniya inda kasashe takwas na Turai suka yi wa kasashe 15 na yankin Caribbean da Afrika.
‘India ce kan gaba’
Miliyoyin mutane sun fuskanci azabtarwa a hannun Turawa
Kungiyar kwadago ta duniya-ILO ta ce a yanzu haka mutane kusan miliyan 20.9 na fuskantar azabtarwa na nau’in bauta kuma a cewar kungiyar a nahiyar Asiya akwai bayi kusan miliyan 11.7.
Bayanai sun nuna cewar kusan rabin bayi a duniya sun fito ne daga kasar India.
Alkaluma sun nuna cewar a cikin kasashe 162, akwai kangin bauta a kasashen China da Pakistan da kuma Nigeria.
A cikin kasar Amurka, gwamnati ta bayyana cewar ana bautar da mutane kusan 60,000 a cikin gidaje musamman wadanda ba suda takardun izinin shigowa kasar.
A Birtaniya kuma an kiyasta cewar mutane kusan 4,426 na fuskantar wani irin nau’i na bauta.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s