HUKUNCIN MASU AIKATA AIKI IRIN NA MUTANEN ANNABI LUD

1. Mai yinsa tuni Allah ya tsine masa. Hadisin yana cikin Sahihul Jami’ hadisin Abdullahi bn Mas’ud. Annabi (SAW) ya jero wainsu mutane wainda Allah ya tsine musu, wanda a ciki Annabi yace:Wanda ya tara da dabba shima tsinanne ne, kuma wanda yayi aiki irin na mutanen Annabi lud tsinanne ne.

2. Sannan mai aikata wannan aikin bayi da Imani. Allah Madaukakin Sarki yace: “Shin wanda ya kasance mai Imani yana zama kamar wanda ya zama fasiqi? Basu zama dai-dai.”

3. Mai yin wannan aiki hankalinsa yana canzawa, hakanan iliminsa zai canza, wato ya koma siffa irin ta dabba.

4. Sannan mai yinsa bashi ba Aljannah, domin Annabi (SAW) yace:A ranar Alkiyama Allah baya kallon wanda ya tara da matarsa ta dubura. Sune ake majajjawa dasu cikin wutar Jahannama. A wata ruwaya Annabi (SAW) yace: Allah ba zai kalli mutumin da ya tara da namiji ko mace ta duburarta ba.

5. Hukuncin wanda aka kama yana wannan inma mace ko namiji to kisa ne.
Kamar yadda Manzon Allah (SAW) yace:
ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺍﻟﺴﻮﺍﻕ، ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻌﺰﻳﺰ
ﺑﻦ ﻣﺤﻤﺪ، ﻋﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﻤﺮﻭ، ﻋﻦ ﻋﻜﺮﻣﺔ،
ﻋﻦ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺎﺱ، ﻗﺎﻝ ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ” ﻣﻦ ﻭﺟﺪﺗﻤﻮﻩ ﻳﻌﻤﻞ ﻋﻤﻞ ﻗﻮﻡ ﻟﻮﻁ
ﻓﺎﻗﺘﻠﻮﺍ ﺍﻟﻔﺎﻋﻞ ﻭﺍﻟﻤﻔﻌﻮﻝ ﺑﻪ ” .
“Duk wanda aka same shi yana aiki irin na mutanen Annabi Lud, ku kashe wanda yake yi, da wanda ake yi dashi. Wannan hadisin ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) yana cikin Abu Dawud 4464, Sahih Tirmizi 1456, Sunan Ibn Majah 2561 hadisin Abdullahi bn Abbas.
Ibnul Jauziy yace: Babu ko sabani akan cewa wannan shine hukuncin wanda yake wannan aiki. Sannan hadisin bai banbanta mana shin mai yin idan yayi aure ne ko bayyi bane ake kashe shi. Hukuncin duk dayane babu banbanci.

6. Suna jawoma ‘kasa Bala’I. Kamar yadda ya faru da mutanen Annabi Lud. Allah Madaukakin Sarki yayi Mana gargadi a cikin Suratul Anfal cewa: “Ku kiyayi fitina wacce inta sakko bata shafan wainda suka yi zaluncin su kadai, ku kiyaye wannan fitina. Domin Allah mai tsananin uquba ne”.
Don haka ne yasa dole mu tashi tsaye wurin ganin mun kubuta daga wannan musiba, Hadisin Abdullahi Ibn Umar, yana cikin Saheh ibn Majah, Annabi (SAW) yace: Babu yadda za ayi alfahsha ta wanzu a cikin wata Al’umma face wata Annoba ta yadu a cikinsu. Kuma wasu cututtuka zasu bayyana wainda da can babu su a cikin mutanen da suka gabata.
Kenan Sababbin cutuka zasu yi ta bayyana a duniya sanadiyyar masu aikata aiki irin na mutanen Annabi lud. Tabbas Manzon Allah yayi gaskiya idan kayi la’akari da cututtukar da suke fitowa a duniya masu wuyan magani masu kuma saurin wanzuwa. Cututtukan zan rubuto su In shaa Allah.

Don haka maza da mata ‘yan (Luwadi da Madigo) kamar yadda kuke fada, kuji tsoron Allah. Idan har kika mutu kina tarawa da mace ‘yar’uwarki ko ka mutu kana tarawa da namiji ko dabba, to wallahi ba zaka sami sassauci ba, kuma zaka hadu da uquba mai tsanani. Zaka yi kuka kukan da bayi da amfani. Allah ya kiyaye mu da ‘yan’uwan mu daga aikata wannan mummunan aiki. Inda nayi kuskure ina rokon Allah ya gafarta mana.

Advertisements

2 Replies to “HUKUNCIN MASU AIKATA AIKI IRIN NA MUTANEN ANNABI LUD”

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s