Sau Uku Ake Harin Kashe Shi! …Sheikh Bin Uthman Kano

A ranar Asabar 8 ga watan Rabiu Thani, 1435 (8/2/1014) fitaccen Babban shahararren malamin addinin musuluncin nan dake zaune a birnin Kano, wato Sheikh Muhammad Bin Uthman, Alqafawy (Babban Limamin Masallacin Juma’a dake Kundila) ya kawo wa Sheikh Ahmad Adam Algarkawy ziyara cibiyarsa ta Attatbiq dake Attatbiq Street by Ahmad Buruku road, Kinkinau G.R.A, Kaduna. A ziyarar tasa, banyan malaman sunyi doguwar ganawa a tsakanin su da tattaunawa yadda zasu qara inganta da’awar sunnah da sauran al’amura, daga bisani Sheikh Muhammad bin Uthman ya jagoranci xaukacin xaliban dake kulliyatu tatbiq da sauran bayin Allah da sauran jama’ar dake unguwar sallar la’asar.
Bayan idar da sallar ke da wuya Malam Ahmad Algarkawy ya gabatar da Mu’allimul Ummah, Fadilatus Sheikh Muhammad bin Uthman don yaba xaliban wannan makaranta saqon da yake xauke dashi gare su, inda Sheikh bin Uthman yayi gajeriyar Muhadara ta mintuna kimanin goma da harshen larabci kasancewar akan hanyar tafiya yake, bayan kamala muhadara ne Malam Ahmad ya neme shi da ya canza harshe zuwa Hausa don baqi waxan da larabcin su bai nuna ba.
Shi ne sheikh ya fara da miqa godiyar shi ga Allah ga yadda yaga havakar cibiyar da xinbin xaliban ta maza da mata kai da kuma tarin matan Aure, wanda yace ba zai manta ba shekaru kusan huxu da suka wuce na zo na tarar da malam ya zage ana aiki da shi, nima na shiga ciki na zage na samu hannun jari a ciki, da ni a ka yi xan abin da akai a wannan ranar, amma Malam Ahmad ya tafi da wannan ladan gaba xaya.
Ya qara da cewa “lallai ku sani aikin da’awa iri biyu ne: Akwai a cikin da’awa wanda ake gina mutane akai (wannan yana daga ciki) na samar da matasa maza da mata har da dattawa wanda za su ci gaba da ginawa ko bayan ka wuce! Wanda shine babban burin maqiya su ga ya rushe”.
Sheikh ya ci gaba da cewa: “wallahi da zaka zo kai ta qara da ihu baza su damu ba, amma da za’a ce ya bar baya…
Wannan yasa malamai suke cewa: “Idan kana so ka gane matsayin malami, to ka kalla ka ga wa ya bari, mai ya dasa”.
Sheikh ya qara da cewa: “Lallai kwanakin mu guda Uku ne, jiya ta wuce, kana da yau, dan haka ka ci gajiyar ta! malamai suka ce yau tana aiki a jikin ka, kaima kayi aiki a jikin ta, dan kwanakin ka a jikin ta suke wucewa, sannan sai gobe, wanda baza ta zo ba, kai koda mutuwa ta same mu a wannan hanyar sai me?
Shugaban mu Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) sau uku ake harin kashe shi, na xaya Allah yace: “Iz yamkuru bikallazina kafaru …” na biyu lokacin da suke mitin a gidan (darun nadwa) gidan da qusaiyyu bn kilab ya gina, shekara 95 kafin a haifi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) sun sake yinqurin kashe shi a Madina lokacin da wata Bayahudiya ta gubanta wata karfata da guba.
Umar Farouk (R.A.) sallah yake aka dava masa wuqa mai dafi, Uthman bin Affan yana cikin karatun Alqur’ani aka kashe shi, matar shi ta kawo hannu dan ta kare shi suka datse mata yatsu, sayyidina Aliyyu haka shima kashe shi aka yi. Wannan sunnar Allah ce ga bayin Allah.
A nan qasar aka kashe Sheikh Ja’afar, Sheikh Muhammad Auwal Albany yau satin mu xaya kenan muna cikin raxaxin abin da ya faru, sai dai kwantar da hankalin ka, ai shi dama xan Adam turvaya ne koda basu kashe shi ba, ba zai dawwama ba, mu dai abin da muke so mu bar baya me kyau muga tasirin wannan aikin da muke yi.
A qarshe ya rufi wannan gajeruwar lakca da yabo da jinjina ga Sheikh Ahmad Adam Algarkawy, inda yake cewa Sheikh Ahmad Adam Algarkawy (hafizahullahu)kowa shaida ne a wannan qasar yayi fice akan irin wannan aiki Almu’assis (wanda ya kafu) tun daga tushe, da barin reno (Training) me kyau a bayan qasa. Sannan ya umarci xaliban tatbiq da cewa lalle duk inda suka tsince kansu koda a wajen wannan qasa su isar da wannan karantarwar, don a yanzu mu abin da muke buqata shi ne aiki, amma kuxi ba shi ne abin da ya dame mu ba. A’a, ya za mu yi kaffa-kaffa, ya zamu shiga kabarin mu shi ne abin da yake damun mu.
Mu zama kamar iyalan Ali Yasir mu kasance lokacin da mutuwa tazo muna cewa ya laita qaumi ya’alamun… ina ma da mutane na sun sani na game da gafarar da Ubangiji ya min, kuma ya sanya ni cikin waxan da ake karramawa.
Sannan ya rufe da addu’ar Allah ya qarfafa malaman mu da jagororin mu, ya qara masu jagoranci, ya tsare mana su, yasa mu duk mu gama da duniya lafiya. Ameen.

Advertisements

18 Replies to “Sau Uku Ake Harin Kashe Shi! …Sheikh Bin Uthman Kano”

 1. Allah subhanahu wata’ala yakaremana Malaman mu Na sunnah ya qara masu daukaka da kwarin guiwar cigaba da karatu da karantarwa tareda fatan Allah ya sa alkhairi acikin karantarwar su.

  Like

 2. Duk wanda ya ce “siyasa tafi sallah” to ya fadi kalmar kafirci, kuma duk wanda ya yarda ma haka. shika shikai a musulunci biyar ne. siyasa kam bata a ciki. Tir da Siyasa.

  Like

 3. Allah isaka wa malam man mu da Alkhairi Allah yadada masu basira Allah yakarisu daga sharin masu shari Allah yabamu zama lafiya aqasarmu da sauran qasashin musulme bakidaya Allah ya daukaka musulunci da jama armusulmi bakidaya Allah yadau kaka malam man sunna damabiya sunna masugaba da sunna Allah yaganaddasu sunna malam man mu dasukarigamu gidan gaskiya Allah yagafartamasu mukuma idan tamu mutuwar tazu Allah isa mucika da imani amin Allah yaba shuwagabanni nagari masu sun cigaban adenen musuloci da ja armususulmi bakidaya amin

  Like

 4. Allah yaki yaye malla amin ya kuma kareshi daga abokanen gaba,bayan haka ya allah ka kaskantar da duk wanda yake so yaga bayan musulunci, ya allah ka daukaka musulunci da musulmai a duk kanin fadin duniya

  Like

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s