RADDIN ASH-SHEIKH ALBANI ZARIA (RAHIMAHULLAH) ZUWA GA SARKIN ZAZZAU DA WASU MALAMAN MASARAUTA. (SOURCE KARATUN SAHEEHU MUSLIM NO 133)

Wannan Raddin ta na kunshe da muhimman fa’idodi, wadanda dukkanin yan salafiyya baza su gajji da sauraronsu ba, Kuma tamkar bulaliyar kan Hanya ce ga masu son rai.
Ash- sheikh Albani yana cikin karatun Saheeh Muslim ne sai akazo babin da mutanen banza suke zargin mutanen kirki da lallata al’umma inda ya tsaya yayi raddi kamar haka;
” Abun mamaki, wai ni Albani sarkin zazzau zai kalla yace wai ina halakar da jama’a. O’! Kaji shi da bai taba tara jama’a ya koya musu koda Bismillahir Rahmanir Rahim ba wai shine zai ce mu dake karantar da Qur’ani da hadisi batar da mutane muke yi.
Wahal afsadaddina illalmuluku wa ulama’u suuil waruhubaanuha. Yau shekara dubu daya da dari biyu Abdullahi bn mubarak yace su waye suka lallata addini? Abdullahi bn Mubarak yace ba kowa bane suka lallata addini sai sarakunan gargajiya da miyagun malamai.
Tabbas! Sai ga miyagun malaman darikar tijjaniyya da wasu yan kungiyar izala shedanu sun hada kai. Wai Babban malamin izala irin Baban Tuni saboda rashin kunya shine zai ce wai aiki da sunnah zata kawo raba kan musulmi. Ikon Allah! yanzu dan izala mai hankali zai ce aiki da sunna zata kawo raba kan musulmi?
Ma’ana wai ana kallan mu cewa bamu san tarihi bane da har za’a hada kai da shedanin dan izala da dan darika a fadar sarkin zazzau wai ace sunnah zata raba kan musulmi. Wai shin ma kuna bin junanku sallah ne? Ba kwa bin junan ku sallah. Wannan na kallon wannan kafiri haka kuke zama, domin kun riga kun kafirta junanku. Amma yanzu izala da ‘darika ne wai zasu hade mana kai.
Jama’a wayannan sune dan Mubarak yake kira miyagun malamai da masu bautar Allah da jahilci. Me suke karantar da al’umma? Babu.
Shine wai har wasu yan izala dake nan zaria sukaje suka buga ma Bala Lau waya cewa ga Albani ni nan yana fada da malaman izala. Shine nake gayama wani daga cikin yan sakon nake cewa kunga irinta. Yanzu su wayannan malaman sun yi fada damu ne a madadin izala? Jama’a ko kun fahimta. Yau shekara talatin kenan ana zaluntar mu da sunan muna fada da izala. Sai wani shedanin dan izala yayi fada da sunna, mu kuma idan muka kausasa magana akanshi sai ya zuke yace muna fada da izala.
Babu wanda ya isa ya wulakanta sunnar manzon Allah (SAW) sannan yasa ran cewa zamu kyale shi. Kuma mu usulubin fadan mu a duniyar malamai fadane irin na malaman hadisi, har abada za’a yi shi har sai ran da ka dawo ka tuba ka janye sukar sunnah daka yi.
Sannan jama’a ku dubi wani mara kunya, shedanin dan dariqa wai ni Albani zai kalla yace wai hadisin dana kawo da’ifi ne. Kaji wanda shi tunda aka haifeshi shi da’ifine a cikin hadisi. Dan zalumci kuma aka ki bani daman in mayar mishi da martani saboda dama zalumci suka shirya. Zamanin mulkin sarautar gargajiya ta wuce domin ana tafiyane abisa jagorancin mulkin bature ne. Saboda haka sarkin gargajiya bashi da izinin dazai tursasa mutum yayi ko yaki yi.
Matasa ku cigaba da karatu, suna fuskantar barazana ne wanda tafi kowanne girma fiye da tashin hankalin dake faruwa a kasar saboda matasa suna ilimi. Abun da suke so shine, sun fiso ku dauki bindiga domin wannan zai basu daman su dauki makami su zalunceku. Saboda haka matasa zaku yi maganinsu ne da karatu. Kuma duk wayannan makaryatan malaman masu gemun shedanu da kuka gansu a fadar sarkin gargajiya zasu gama barabaren su, kuma asirinsu sai ya tonu. Kudai dage da karatu domin kune manyan gobe.

Advertisements

32 Replies to “RADDIN ASH-SHEIKH ALBANI ZARIA (RAHIMAHULLAH) ZUWA GA SARKIN ZAZZAU DA WASU MALAMAN MASARAUTA. (SOURCE KARATUN SAHEEHU MUSLIM NO 133)”

 1. Allahu Akbar Allah sarki Allah y jikan Babban Malamin Salapiyya Shaikul islam Almuhaddis Al Allama Abu Abdurrahman Sheik muhaammad Adam Aalbaany xaria Rahimahullah

  Like

 2. Allah y taimaki sunna da masu da,awar yada sunnah sannan Allah kaji kan malam albani zaria da malam jafar Allah y karbi shahadar su sannan ina son nayi kira ga maluman sunnah dasu rinka jan hankulan mu matasa akan karatun addini domin samari sune al,umma idan suka baci kowa ya baci Allah y kare mu

  Like

 3. assalamu alaikum jama,a nidai INA son Ku fahimci wani Abu a cikin maganar nan ta. wurin da yake cewa muyi karatu wanan magana ce wadda duk wani malami ahlissunnah zaka ji yana fadi don haka qalubalin Ku ahlissunah

  Like

 4. Muna da munafukan shuwagabanni a wannan kasa tamu mai suna Nigeri’a, wayanda farahinsu yake agoshin su, halin da ake ciki yanzu shi ne sunaji suna gani kisannan da akewa musulmai awannan kasan babu wanda yatashi yayi magana alhalin suna datacewa aciki amma kowa yayi yayi shiru sai ‘yan kadan. To wallahi in basu tubaba suna cikin wulakanci tun aduniya kafin ALLAH yakama su suci uban duka. Ya Allah in masu shiryuwa ne Allah kashiryar da su in bamasu shiryuwa ba ne Allah katarwatsasu ka hanasu sakat kacire musu kwanciyar hankali. AMEN.

  Like

 5. Malam Abdullahi Gaskiya inajin baka dade kana yawo a cikin Blog dina ba. Da ka duba kasan Post din zakaga Wani link mai suna “Tags” a jikinsa zakaga sunan duk source din rubutun da nayi Sannan Idan ka duba wani page “INFO” zakaga bayanan da nayi.

  Like

 6. Next time ya kamata kayi kokari ka rink a rubuta inda ka ‘dauko rubutu. Nina rubuta wannan post ‘din amma banga inda ka rubuta sunana a matsayin source ba.

  Like

 7. This is the right site for anyone who wants to find out about this topic. You know a whole lot its almost hard to argue with you (not that I really would want to…HaHa). You definitely put a brand new spin on a subject which has been discussed for a long time. Great stuff, just wonderful!

  Like

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s