INA MASU NEMAN GUZIRI ZUWA LAHIRA??? ‘Yan uwa ga GUZIRI kyauta gareku dan jin dadin tafiya lahirarku.

1= Ku tabbata kuna karanta abinda ya sauwaka daga Qur’ani cikin kowace rana. Sannan kuyawaita SALATI ga Annabin rahma Muhammad SAW.
2= Ku kiyaye SALLOLI 5 da Allah ya farlanta muku, ku kiyaye SALLAR DARE da kuma sallar DUHA ko da raka’o’I 2 ne.
3= Kuba da ZAKKA dan wajibi ne akanku in har Allah ya hore miku, kuyi SADAKA akowace rana ko da da abu kankani ne, idan baku samu damar yi da wani abu ba to kuyi da KALMA ME DADI, ku a zumci RAMADAN, ku yawaita azumin nafila in bai samu ba kuyi kokarin azumtar KWANAKI 3 cikin ko wace wata.
4= Kuna so ku zamo daga cikin wadanda Allah yake so? To kuso Annabinku Muhammad SAW da iyalan gidansa, ku kyautatawa iyayenku, kuma mata kuyi biyayya ga mazajenku.
5= Kuna so ku zamo daga cikin wadanda idan sukace YA RABBI-YA RABBI, Ubangiji zai amsa musu da cewa “Na amsa muku bayina tambayi in ba ku? Ku ciyarda abincinku, ku kimanta mutane aranku sannan ku mu’amalance su mu’amala me kyau.
6= Kuna so kuza mo cikin wadanda ake amsa addu’insu kuma takaddunku su haskaka ranar alkiyama? Ku tsarkake zuciyarku, kuma ku yawaita fadin LA’ILAHA ILLALLAH, ku ne mi gafarar zunubanku dana muminai maza da mata, kada ku sake ku zamo daga cikin masu gafala daga ambaton Allah.
7= Kuna so ku zamo daga cikin masu yabo, masu godiya kuma makusanta? Sani dai, duk lokacinda bawa yace ALHAMDULILLAH, sai Allah ta’ala yace “ينركشو يدبع يندمح”
Bawa na ya yabe ni kuma ya gode mini” dan haka ku yawaita fadin ALHAMDULILLAHI WASALAMUN ALA IBADIHILLAZINASƊAFA.
8= Kuna so ku zamo daga cikin masu godiya, wadanda Allah yake salhanta musu zuriyarsu?
To ku dimanci ayoyin godiya;
= RABBI AUZI’INI AN ASHKURA NI’IMATAKALLATIAN AMTA ALAYYA WA’ALA WALIDAYYA WA’AN AAMALA SALIHAN TARDAH WA’ADKHILNI BIRAHMATIKA FI IBADIKASSALIHIN” (NAML 19)
= RABBI AUZI’INI AN ASHKURA NI’IMATAKALLATYAN AMTA ALAYYA WA’ALA WALIDAYYA WA’AN AAMALA SALIHAN TARDAH, WA’ASLIHLI FI ZURRIYATY INNI TUBTU ILAIKA WA’INNI MINAL MUSLIMIN” (AHQAAF 15)
9= Kuna so in nuna miku abinda zai hada miku al’amuran addininku dana duniyarku? Kuyi aiki da dokokin Allah dai-dai gwargwado. Allah yace: “Ya ku wadanda kukayi imani, kuyi ruku’u kuyi sujjada ku bautawa Ubangijinku kuma ku aikata alkhairi za ku samu babban rabo”
(HAJJ 77)
10= Yan uwa masu daraja, barima kawai in sanar muku abinda zai hada muku dukkan komai. Kuce KUNYI IMANI DA ALLAH, sa’annan KU DAI-DAI TA! Ma’ana KU TSAYA A IYA INDA ALLAH YA TSAIDAKU NA UMARNI DA HANI.
Wadannan na daga cikin GUZlRIN da idan kuka rike su za kuji dadin tafiya lahira (kabarinku bayan barinku duniya kafin isarku lahira) INSHA ALLAHU RABBI.
Alllah yasa ku isa lafia, cikin aminci kuna masu jin dadin haduwa da Ubangijinku.
Amin.

(Iman Bint Imam)

Advertisements

One Reply to “INA MASU NEMAN GUZIRI ZUWA LAHIRA??? ‘Yan uwa ga GUZIRI kyauta gareku dan jin dadin tafiya lahirarku.”

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s