TALAUCI DA HALIN NI’YASU A NIGERIA! MAFITA DAGA BAKIN DA BAYA KARYA…!!!

Annabi SAW yace “Alfasha bata taba bayyana a cikin wasu mutane har sukai ado da ita ba face annoba ta watsu acikinsu da ciwuka da basu taba ganin
irinsuba, basu kuma taba tauye mudu da sikeli ba face an kama su da tsananin fari, da kuncin rayuwa da zaluncin shugaba, basu taba hana zakkah ba face
an hanasu ruwan sama badon dabbobi bama da kwata kwata ba ayi musu ruwaba, basu
taba warware alkawarin Allah ba da alkawarin manzonsa face Allah ya dora makiyinsu akansu, makiyan suke dauke da sashen abunda suka mallaka, matikar shuwagabannin su ba suyi hukunci da hukuncin Allah ba sai Allah ya sanya tsananinsu a tsakaninsu”.Ibn Majah 4019 da Ihya Kutub Al’arabiyah.
Annabi SAW Yace “idan kukai kasuwanci irin na ruwa, kuka riki bindinan shanu, kuka amince da hatsi (ma’ana kuka karkata zuwaga holewa rayuwa), kukabar jihadi, to Allah zai buga kaskanci akanku bazai cireshi ba har sai kun koma zuwaga (cikakken)
addininku” Sunan Abi Dawud 3462 Maktabatul Asriyyah, (Hadisi ne Sahihi).
Daga abunda ya gabata zamu gano cewa: Yaduwar alfahsha na kawo ciwuka da Annoba.
Tauye mudu= yana kawo fari, da kuncin rayuwa (kamar tsadar kaya da rashin kudin saye dss),
Zaluncin shugaba. da Hana zakka= yana kawo hana ruwansama.
Karya alkawuran Allah= yana janyo rinjayen makiya.
Rashin hukunci da littafin Allah= yana kawo tsanani tsakanin mutane.
Holewa da barin jihadi= yana kawo kaskanci.

MAFITA:-
Itace komawa zuwa ga cikakken addini, in akai haka za aga canjawar Al’amura.
Allah ya kawo mana karshen wadannan matsaloli da muke fama dasu a Nigeria da Duniya baki daya.
Ameeen

(Musa H Musa)

Advertisements

One Reply to “TALAUCI DA HALIN NI’YASU A NIGERIA! MAFITA DAGA BAKIN DA BAYA KARYA…!!!”

  1. Pingback: Jezyk Wloski

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s